Sashe 11
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kamo kanta ya fara karanta addu'a "ALLAHUMMA INNI AS'ALUKA KAIRAHA WA KAIRA MAJA BALTAHA AKAIHIM WA'AZUBIKA SHARRIHA WA SHARRA MA JABALTAHA ALAIHI" Yayi dan shiru bayan ya gama karanto addu'ar yana kallonta cikin kwantar da murya yace "Ma'u na san kin iya dukkan farillan addini da ya kamata ki sani, ko akwai wani abu da baki sani ba? Ma'u ta girgiza kai kawai, ya sake yin murmushi yace "ai ban gane me kike nufi ba, ki bude baki ki sanar da ni eh ko a'a zaki ce min shi ne zan fahimta kuma har na gamsu" "Eh na sani" ta fada da sauri. Yace "yauwa na san haka, tashi ki je ki sanya rigar da kika sanya dazu ki kwanta" Bai jira jin abinda zata ce ba ya mike ya fice ya nufi kicin dinsu, ya duba yayi sa'a akwai kalanzir don haka ya dora ruwan zafi kadan ya dafa shayi a dan karamin kofi ya sanya koren ganyen shayi (Green Lipton) ya shanye karamin kofi sannan ya nufi dakin. Yayi sa'a akwai wutar nepa fanka tana kada dakin nasu. Yanda ta kwanta dazu yanzu ma haka ta kwanta, ya sanya hannu ya kashe kwan fitilar dake dakin, ya karasa gadon ya kwanta daga gefe daga inda yake yana jin sautin ajiyar zuciyar Ma'u. Ya dan matsa gab da ita har yana dan gogar jikinta, amma bai shafe ta ba sai yace "Ma'u ba ni labarin me da me ya faru bayan tafiyata? Tayi shiru ta kasa magana amma sai dai faduwar gaban nata ya dan ragu. Ya ci gaba DA magana a hankali daidai saitin kunnenta. "Tunda kin ji ba ni labari bari na ba ki nawa labarin. Lokacin da aka ce an daura aurena da ke sai nake ga abun kamar wasa, kamar shiririta har na tare da ke bana jin komai a kanki sai kulawa ta kanwata, sannu a hankali damuwa da tunaninki ya fara shiga raina, lokacin da zan tafi legas nayi tsammanin na damu da rabuwa da ke ne, domin sabo da shakuwa da ta kuma shiga tsakaninmu, sai dai bayan naje can na gano kaunarki da soyayyarki ne na gaskiya ya shiga zuciyata..." Ya dan yi shiru yana murmushi shi daya cikin duhu, wani irin shauki da bakon abu na sake shigarsa. Ya dan kara matsawa jikinta ya kamo hannunta ya rike cikin nasa ya fara wasa da shi. "Tsarki da buwaya sun tabbata ga UBANGIJI da yake halittar zuciyoyi ya sanya Soyayya a cikinsu. Ma'u yanzu babu abun da nake so a duniya bayan ALLAH DA MANZONSA da kuma ummata kamarki" Tsigar jikinta ta tashi yarr! Ta dinga jin wani Abu yana shigarta wanda ba zata iya fasalta shi ba, ta dinga jin kamar ta juya ya rungume mijinta, amman sai ta ji tafukan hannunsa sun saki hannunta sun fara kai komo cikin jikinta, ya cigaba da magana cikin kunnenta. "Ban taba zaton zan yi wa ma'una irin wannan soyayyar ba, ki gaya min Ma'u me kike ji a kaina yanzu? Domin tunda na dawo na gano wani abu a cikin kwayar idanunki, juma gangar jikinki kamar tana nuna min wani abu na yadda..." Ya sake yin kasa da murya yana cigaba da magana. "Ma'u kin yi wayo yanzu, kin san meye aure kin amince min na zama mijinki na gaske a gare ki ba suna ba? Ki bar ni na fara raya sunnah da ke a farkon duniyata. Ki bar ni naji abibda kowa ke ji a cikin aurensa ma'u." Ya kankameta a jikinsa kamar zai mai da ta cikin nasa. Ita kam ta gaza cewa komai domin yayi mata dukkan abun da zai kashe mata jiki, tana jin jikinta da zuciyarta ya gamsu da amsar mijinta, ta karanta littattafan Soyayya masu dama, amman bata taba karanta irin soyayyar da mijinta ke gwada mata ba. Cikin duniyar shauki ta jiyo shi yana cigaba da sambatu da rokonta. "Ba ki ce komai ba ma'u, ki ba ni dama don ALLAH ki amince na zama miji a gare ki da gaske" Cikin rawar baki tace "na amince maka yayana" domin ta fuskanci yana gab da shide mata. _ALLAH MAI IKO_ kawai Ahmad yake iya ayyanawa a cikin ransa, har ya kai ma'un ga matsayin da kowacce mace ke shiga wato CIKAKKIYAR MACE. Ba ma'un kadai ba, shi kansa ya sha wahala, domin tare suka bare junansu a kwali, amman ma'un ta ba shi mamaki domin tayi matukar dauriya, don haka har bacci ya dauke ta tana kan kirjinsa yana shafar gashin kanta da jin dadi cikin ransa gami da yiwa ALLAH godiya da ya nufe shi da yin aure har ya dandani zakin dake cikin auren. Gajiya da kasala suka taru suka yi musu rubdugu, don haka sun kusa makara, shine ya fara tashi ya dora ruwa ya shiga wanka, kafin ya fito daga wankan an idar da sallah a masallaci. Bai ji dadin hakan ba, amman ya san ALL AH zai yafe masa tunda ba da niyya ya aikata hakan ba. Sai da ya fara yin sallah sannan ya girka ruwa mai dumi ya nufi daki. Har lokacin ma'u tana bacci, domin ta sha matukar wahalar da bata taba sha ba a rayuwarta. Cak ya dauke ta kamar 'yar bebi, sai sannan ta farka tana jinta a jikinsa ta kara mai da idonta ta rufe domin kunya ta gama rufe ta. Yayi murmushi kawai bai ce komai ba. Cikin faffadar robar da ya kusa cikawa da ruwan zafi ya tsunduma ta a ciki bayan cire dan yalolon zanin dake jikinta, tayi doguwar ajiyar zuciyar sanda ruwan ya fara ratsa jikinta, amman har lokacin idonta yana rufe ta kasa budewa. Yayi murmushi ya juya ya fice ya bar ta a bandakin ita kadai. Ta yi wanka ta gasa jikinta, sai ta ji kwarin jiki. Kafin karfe takwas na safe tayi ahmad ya gama yi musu komai na kayan karin kumallo. Sai da yayi DA gaske ta ci domin kunyarshi ta hana ta sakat, shi kam dariya kawai yake yi mata da tsokanarta. Ranar haka nan suka kare shi cikin nishadi da jin dadi gami da kaunar juna. A ranar tare suka fita sayayyar kayan abinci, da yake akwai dan kudi a hannunsa har dan karamin cooker gas ya siya mata, ya kuma yi mata siyayyar kayan kwalliya da na shafa daidai karfinsa. *** Rayuwar Ahmad da ma'u ta zamo abar sha'awa domin kullum soyayyar junansu kara karuwa take cikin ransa, sun saba da juna sun shaku da juna. Ahmad ya iya Soyayya ya kuma koyar da ma'u Soyayya da sonsa, domin idan ya fita aiki ta kagu ya dawo, don ma dai karatun littafi yana dan dauke mata hankali kadan. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. BAYAN SHEKARA BIYU Ma'u ta zama cikakkiyar mace da ta iya rike mijinta. Zuwa wannan lokaci duk wata kira ta halittarta ta kammala fitowa. ALLAH yayi halitta mai tsananin daukar hankali, musamman tsarin jikinta da ake cewa mai kirar kalangu. Bata cika haske ba, amman mai sheki ce da sulbi. Doguwa ce sambal bata DA jiki ko kadan. Amman kirarta da cikar kirjinta ta sanya take dab ciko ido. Mijinta bai gajiyawa da kallonta, musamman idan tayi kwalliya har yakan rasa a ina matarshi take koyo abubuwan da takan yi. Ita dai ba wasu kawaye take da su ba, domin yan matan dake dan shigo mata ma a baya yanzu duk sun daina, domin ta fara kishin mijin ta, wasunsu kuma suna makarantar kwana. Ahamd ya kasa gano sirrin matarsa, daga karshe ya bawa zuciyarsa amsar kawai Allah ne ya halicceta a haka. Amman duk lokacin da zata fita unguwa sai an kai ruwa rana, ya dinga kallon irin shigar da zata yi, yayi mata tsari, ta cire wannan kayan Santa wancan shi ne zai kai ta kuma ya dawo da ita, tun tana dariya tsananin kishinsa har abun ya fara damun ta. Yau tana zaune tana gogewa mijinta kayan da ta wanke masa jiya, ta jiyo sallamar Maryam kawarta daga kofar falon. Tayi saroro da mamaki don tana tantamar abinda kunnenta ya jiyo mata na muryar kawar tata. Maryam ta dago labule tana fadin "ko matar gidan bata nan ne? Ma'u ta mike da sauri tana ihun farin ciki ta rungume Maryam suna tsalle cikin farin ciki. Maryam ta janye jikinta tana fadin "rufa min asiri na koma gidanmu lafiya, kada ki ji ciwo mijinki ya tayar min da kayar baya" Ma'u tayi murmushi tana fadin "naji dadin ganinki Maryam, nayi zaton ai kin manta da ni ne tunda su Aisha sun watsar da ni" "Wace ni kin san makarantar ce ke hana ni zuwa, amman yanzu tunda mun yi candy ai har sai kin gaji mda ni kafin na samu admission" Admission kuma Maryam? Ma'u ta tambayeta da sanyin jiki da damuwa. Marayam ta bata amsa da "eh kin san baban yana sin na cigaba da karatu kamar sauran yayyena, idan result dina yayi kyau medicine nake son karanta ko pharmacy" Da damuwa ma'u tace "kin ji dadinki dama no ce, ni yanzu sai zaman gidan ban san a halin da nake ba, ko da a ce candyn ma nayi to da da dan sauki" "A zatona kece baby ki son karatun amma Yayanki ahmad bai yi kama da wanda zai hana ki karatu ba, domin ai shi ma yayi karatun ma gani ko? Ma'u tayi murmushi kawai tare da mikewa tsaye tana fadin "ba ki san halin yaya Ahmad ba, dan banzan kishin sa ba zai kyale ni nayi karatu ba. Bari dai na kawo miki abin sha muna ta zuba hira ban sauke ki da ko ruwan sha ba" ta nufi kofa kai tsaye. A nan gidan ma'u Maryam ta yini har sai da ta gaya ma'u girkin dare ita ma ma'un na sha'awarta na kammala karatun ta, ita kuma tana sha'awar ma'un na yanda tayi sa'ar aure duk da mijinta ba mai hali bane amma suna cikin rufin asiri. Sai gab da sallar magriba Maryam ta bar gidan, amman ta tafi ta bar zuciyar ma'u DA miki, wanda tayi nufin amayar da shi yau ko ta huta. Kamar yadda ahmad ya saba dawowa da