Sashe 38
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ciki, sannan danginsu daga can 'yan leman sun zo, yaga duk wannan taron don shi ake yi, don haka ya gaza boye farin cikinsa sam. Wannan shine abunda ya kara tayar da hankalin Ma'u don ranar Ahmad bai kula ta kanta ba, tunda ya fice tun safe sai kw nciyar bacci ta dawo da shi gidan. Can gidan baban nasa ya zauna ana ta hira da wasa da dariya da 'yan uwansa. Sanda ya dawo ya tarar da gidan cike da mutane, don haka kai tsaye dakinsa ya wuce ya watsa ruwa ya fito da nufin kiran Ma'u sai kuma ya kama hira da Nana da ta kira shi. A nan ya shantake har bacci ya dauke shi bai nemi ma'u ba. Yana tashi da safe ma da shirin fita ya fito, kasancewar abokinshi Jabir ya shirya masa 'yar walima su da abokansu da suka yi karatu tare, sanda ya shiga dakin Ma'u don yin magana da ita aka ce tana wanka shi kuma ba zai iya tsayawa jiranta ba, saboda can an dame shi da Kira a waya, don haka ya juya ya fice. Wannan abun ya karawa Ma'u tsoro a ranta har take ganin tata ta kare gurin Ahmad, ba shi da sauran lokacinta, kuma bata kara ganinshi ko jin wayarshi ba har dare sai 'yan kawo amarya suka fara jerin gwano da motoci, tun tana iya ganin adadin motocin da suke ta zuwa har ta kai ga gaza yin hakan, harabar gidan kato ne zai iya cin motoci kanana hamsin, kuma bangaren Ma'u da Nana daban, akwai 'yar tazara mai nisa. Asalin gidan Alhaji Nura Kwangila ne da ya bata shekaru yana ginawa ya bai wa Ahmad da zummar shi zai kara gina wani gidan nasa. Gudar kawo amarya da ake yi kamar cikin ran Ma'u ake yin ta, ga shi lokacin babu kowa a gidan, duk jiya aka zo mata, daga ita sai masu aiki sai ta fashe da kuka ta hada kai da bango tana kuka. Gaba ki daya gidan yayi zafi da kunci, babu abunda take so illa ta fita ta barshi ko zata huta. Tana nan har 'yan kawo amarya suka watse. Can wajen karfe goma da mintuna Ahmad ya iso gidan. Kai tsaye dakin Ma'u ya nufa, ya sha mamaki ganin bai ga komai a kan fuskarta ba na bacin rai, don ita kadai ta san abunda ta kudurce a cikin ranta. Ya dan zolaye ta tana murmushi ya bukaci suje sashin amarya tace ba dai yau ba yau ba sai gobe. Ya ajiye mata kasonta da ya shigo da shi yayi mata sai da safe ya nufi sashin Nana cikin dokin da ya kasa boyuwa akan fuskarshi don yau kusan tare ya yini da Nana, kwalliya ta dinga yi ta tsuma shi kwarai da gaske, wannan abun yayi wa Ma'u ciwo kwarai da gaske,yana fita ta kara fashewa da kuka. Wai yau Ahmad dinta ne ke nuna zumudi akan wata mace ba ita ba? Shi kam Ahmad yana shiga dakin amaryarsa ya dan zokayeta ta ki sakin jiki sai ya sureta cak suka yi bandaki yin alwala idonta a rufe da kunya. A gaskiya a matse yake da Nana don tun ranar da ya ganta kusan tsirara sha'awarta ta gama nuna a cikin ranshi, don haka suna idar da sallah ya far nuna mata bukatarshi da yake ita ma ta jima tana jiran wannan lokaci bata yi wani noke-noke ba ta bayar da kanta. Abunda ya bashi mamaki bai wuce ganin bai sha wata wahala kamar yadda yasha akan Ma'u ba, nan da nan yaji ya gamsu. Bayan ba haka ya so ba, yayi kyakkyawan shirin da zai yi yanda ya so sai dai bai samu ba, yanayin mace 'yar Shekara sha shidda sha bakwai da mai Shekara ashirin da uku hudu da bambanci, don ita 'yar sha komai bata kankani yake bai saki ba, sabanin na wacce ta dan yi shekaru ashirin. Sannan kuma a daren ya fuskanci Nana tana da tsawon bukata, sai yayi mamakin dalilin da ya Sanya bata yi aure da wuri ba. Koda yake da alamun bata taba yin mu'amala da wani namiji ba don ta dan wahala, amman sai yaji daren farko shi da Ma'u yafi wannan nesa ba kusa ba, amman ya bar abun a cikin ranshi. Ita kuma Nana wannan shine dare mafi alkhairi a rayuwarta. Sai a yau ta gano ashe tana kwarar kanta da rayuwarta, jikinta yana bukatar wani abu da take tauye masa. Lallai Ahmad ya kai ta gurin da bata taba zuwa ba, ba ta ma taba mafarkin zuwa ba. Da safe duk da Ma'u tana ranshi gajiya da kasala bai bar su sun fito da wuri ba sai wajen karfe goma sha daya na safe. Lokacin sun shirya yace da Nana tazo su shiga wajen Ma'u su gaisa suka jera suka nufi sashinta. Masu aiki suna ta hidimarsu suka shiga suka dinga gaishe su, sai wata Yaya Abu ta fito daga kicin da sauri ta mikawa Ahmad wata takarda tace in ji Hajiya tace a baka. Da mamaki yace "wacce Hajiya kenan?" Cikin ladabi ta amsa "Hajiya Ma'u mana" "Tana ina yanzu?" Tace "Ta fita tun asuba..." Ya katse ta da fargaba "Ma'un ina ta tafi? "WALLAHI ban sani ba ni ma Alhaji" Damuwa da tashin hankali suka bayyana aka fuskarsa, sai yace "Babu damuwa jeki kawai" Ya kalli Nana dake kallonsa da fargaba sannan ya mai da hankalinsa ga wasikar ya bude. Ga abunda ta kunsa. Mijina Ahmad. Nayi iyakacin kokarina na danne zuciyata na zauna da kai, amman na kasa don na gano yanzu kayi min nisa, ka girmi rayuwata, wancan Ahmad din mijina da muke daidai shine talakan nan mai kula da ni da cina da shana, mai kula da yanda na kwana da yanda na tashi, ba kai ba babban mutum. A yanzu rayuwarka tafi dacewa da diyar masu kudi da arziki irinka ba wadda kake taimako ba, mai ilimin degree da master's da wayewa. Rayuwarka ta girmi ta Ma'u yanzu, don haka naga yafi dacewar na matsa ba baku guri, na san ba zaka iya sakina ba saboda kunya da tunanin kada duniya ta zage ka, don haka na hutar da kai na tafi inda ba zaka kara ganina ba, ba zaka ji kunyar iyayena ka sakeni ba, amma ina son wata rana ka furta sakina ko cikin ranka ne, don kada nayi ta yawo da aurenka. Ga kuma amanar 'ya'yana wata kila zan gan su wata rana. A lokacin da zaka ci karo da wannan wasikar tawa tuni nayi nisa daga inda kake! Ina yi maka fatan alkhairi kai da matarka. ASMA'U Matarka a baya. Wani irin abu ya bi ta jininshi ya wuce zir! Kamar wutar nepa ta jashi, ya waro ido da fadin "what? Me kika aikata haka Ma'u, ya kike tsammanin zan rayu babu ke? Nana ta kalle shi ganin kamar yana shirin zarewa ne tace "yaya Ahmad lafiya, me ya faru? Cikin kidima yace "Ma'u ta gudu, tabbas cikin satin nan na wofintar da rayuwarta, ban damu da damuwarta ba, hakan ya sanya tayi zaton na daina sonta ne. Yaya zan yi na shiga ukuna, WALLAHI idan babu Ma'u ba zan rayu ba, bari naje na gayawa Abba da Umma" Sai ya juya ya nufi fita daga falon, Nana tayi hanzarin riko shi da sauri tace "haba yaya Ahmad wannan matsala ce tsakaninka da matarka, ka san ko ina Ma'u zata je ba zata yi nisa da kai ba, bacin raine ya sanyata tafiya, idan ka gayawa iyayenta kamar ka tona muku asiri ne, zaka iya janyowa suyi fushi da ita" Maganganun Nana suka shige shi yace "haka ne yanzu me ya kamata nayi? Don ALLAH gaya min Nana kaina ya kulle, ina tsananin son matata" Ta ciza baki tace "ka je kowanne gida da ka san zata je ba da sunan cigiya ba da sunan kaje gaishe su ne, ta haka zaka gano inda ta shiga" Yace "yauwa haka za a yi bari na dawo" ya fice da sauri a rude. Ta bishi da kallo idonta ya cika da kwalla. Lallai Ma'u tayi nisa a zuciyar mijinta, idan kuma tace sai tayi gasa da ita zata iya zamtowa cikin takaici, abu daya be zai janyo sonta ya zama daya da na Ma'u ko ma ya fishi shine asiri, wanda bata taba sha'awar yin sa ba, don wadanda taji labarin sun yi ma bai amfana musu da komai ba. Ta goge hawayen dake zubo mata ta nufi sashinta. Ga Ahmad kuwa dukkan inda ya san zai samu Ma'u sai da yaje har yamma tayi masa ya gaji likis ba tare da ya gano inda take ba, ya far sarewa da tunanin ko ya sanar da iyayenta, don duk wayoyin Ma'u a kulle suke. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Tunda Ma'u ta isa garin Zaria gidan kawarta Maryam wacce tayi aure kusan shekaru uku da suka wuce ta auri wani soja, Ma'u taje mata tana muka dakyar Maryam ta rarrasheta ta sanar da ita abunda ya faru ta hada da rokonta akan ta rufa mata asiri ta barta kada ta gayawa kowa tana gurinta har zuwa sanda zata san inda zata tafi don ba zata taba komawa gidansu ba ko gurin danginta ba har abada. Maryam ta matukar mamakin jin labarin da Ma'u ta bata, amma san bata ga laifin Ahmad a cikin wannan labarin ba, ko din ita ma tana da kishiyar ne? Ita ce ma amarya. Da Ma'u ta san irin halin da kishiyarta ta shiga sanda zai aureta da tace Ahmad dan aljanna ne, don haka ta far baiwa Ma'u hakuri da labarai kala-kala na mazajen da zasu yi aure, duk jikin Ma'u yayi sanyi amman tace mata ita dai ta kyaleta. Daga karshe ta dora da ce mata 'yanzu haka mijin nata Yana gidan uwargidanta zai mata kwana biyu ba zata kara ganinsa ba sai bayan kwana biyu koda cuta zata kasheta ita da danta kuwa, ga rashin wadatasu da take yi, aikinta shine gatanta (da yake tayi karatu mai zurfi har degree) amman tana lallaba aurenta domin ta jima bata samu yinsa ba' Duk