← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 40

Sashe 35

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da ta nuna min ya sanya da na haifi diyata na mai da sunanta akanta, wato NANA ASMA'U" Wani farin ciki ya mamaye Ahmad har ma ya rasa abunda zai furta, sai yake kawai yake, kaunar Nana ta fara shiga ransa.ganin abun yake kamar a cikin mafarkin da ya saba idan ya kwanta bacci. Wai yau shine ya san asalinsa da dalilin haukar mahaifiyarsa? Ashe mahaifiyarsa bata aikata wani abu na sabon UBANGIJI ba! Malam Sulaiman yayi doguwar kabbara da godiya ga ALLAH cikin tsananin farin ciki da murna. Umma kam bakinta ya ki rufuwa ashe zata ga wannan rana a rayuwarta? Kowa jinsa yake wani iri daban, kallo daya zaka yiwa kowa kaga mamaki da farin ciki karara akan fuskarsa. A take a nan aka yiwa Hajiya Amina waya ta iso gidan. Ita ma tayi mamaki da farin cikin jin Ahmad dan gidan manya ne, aka dinga murna da mai da yanda aka yi. Hatta Malam jibril ma sai da ya shigo da ya ji hayaniya tayi yawa, don duk mazan gidan sai da aka Kira su a waya suka zo. Mamaki da tu'ajabi ya kama shi saboda ganin Alhaji Nura Kwangila a cikin gidan zaune a tsakiyarsu Malam Sulaiman suna tattaunawa don duk wanda ya kwana ya tashi a garin nan ya san Alhaji Nura Kwangila. "Yau kuma masu dukiya babu iyaka ne suka zo gidansu?" Ya ayyana hakan a cikin ransa sai kuma ya ji wai kanin baban Ahmad ne, iko sai ALLAH. Dakyar Alhaji Nura Kwangila ya iya barin gidan, amma da rokon gobe za a bashi dama ya tafi da Ahmad can garinsu na 'yan leman sannan zai yi masa visa shi da iyalinsa su tafi Saudiyya gurin mahaifinsa da kakarsa. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Wannan dare mai muhimmanci ne ga Ahmad da duk wani mai kaunarsa. Bayan sun koma gida ya kankame ma'u yana kukan dadi da farin ciki. "Ma'u ashe ina da rabon ganin dangina da mahaifina har da kakata? Ashe ina da rabon yin farin ciki har da alfaharin yanda kowanne da keyi da iyayensa da danginsa? Ma'u me ya fi wannan dadi a gare ni? Me zan yi na godiya ga ALLAH? Tabbas ni din dan gatan UBANGIJI ne, bai taba tozarta rayuwata ba, bai taba wulakanta ni ba. Me zan cewa ALLAH? Yana magana yana kuka, amman daga gani kukan farin ciki ne. Ita ma ma'u kukan take yi na taya mijinta murna da kuma rarrashinsa. Tace masa "sallah zamu kwana muna yi da yin godiya ga ALLAH da ya kaddara mana ganin wannan lokaci, wannan shine kadai hanyar da zamu nunawa ALLAH farin cikinmu" Ya kada kai yana fadin "haka ne tashi mu fara" A cikin gidan su Lami kuwa, wuki-wuki Lami tayi jin asalin Ahmad tana zare ido, lallai ta ga dumbin darasi a rayuwarta. Malam jibril yace mata "shi ya Sanya kullum nake gaya miki babu kyau wulakanta dan Adam. Yau dai ga iyayen Ahmad da kike yiwa gori kullum shi shege ne to danginsa dangi ne masu asali da arziki. Ke yanzu ina dangin jikarki diyar raliya suke? Kin ga hakan ya tabbatar miki ke ce mai shege ba shi ba" Sai kawai Lami ta fashe da kuka tana fadin "lallai nayi kuskuren da ba zai gyaru ba, me ya Sanya na biyewa zuciyata har na aikata wannan abun? Kaicona!" Malam jibrul yace "Lami ai baki daina kuka ba tunda har yanzu har yanzu baki san halin da diyarki raliya take ciki ba" Diyar raliya ta iso ta zauna akan cinyar Lami tana fadin "ke Lami me aka yi miki kike kuka?" Lami ta kalli yarinyar da tausayin halin da ta janyowa rayuwarta, da yanzu ita ce zata kasance cikin wannan daular. A gidan Alhaji Nura Kwangila kam dan karamin fim aka yi, domin yanda ya shiga da farin ciki yana kwalawa matarshi da diyarshi kira ya ba su mamaki don ba halinsa ba ne. Suka fito da tsananin mamaki suna tambayarsa abunda ya faru. Hajiya Batula tace "duk yanda aka yi an tsai da auren Nana da Ahmad" Dadi ya cika Nana. Alhaji Nura Kwangila ya kada kai, "wannan abun yafi auren Nana da Ahmad, farin ciki akan farin ciki, ku zauna na gaya muku abunda ya faru" Ba musu suka zauna, Alhaji Nura Kwangila ya kalle su yana murmushi yace "ashe Ahmad dana ne, domin dan dan uwana ne. Shi ya Sanya ni da diyata ALLAH ya jarrabe mu da tsananin sonsa da kaunarsa" Hajiya Batula ta cika mamaki, domin ta san duk abunda ya faru ga yayan mijinta, duk da lokacin ko tunanin aurenta ma ba a yi ba, amma ta yaya hakan zata kasance? Nan Alhaji Nura Kwangila ya kwashe labarin duk abunda ya faru ya sanar da su. Nana ta daka tsalle ta rungume mahaifiyarta wacce ke yin dariya tana fadin "sakarya kin manta ba ki da lafiya ne?" Sannan ta kalli mijinta da farin ciki. "Ban taba jin irin wannan labarin ba ko cikin littattafan hikaya ko kuma cikin fina-finan da ake yi ba. Lallai girma da tsira ya tabbata ga ALLAH. Wato a sanda ake tunanin Asma'u ta mutu ashe ita tana can cikin mawuyacin hali, sai dai ALLAH ya cika lamarinsa na haihuwar Ahmad sannan ta koma ga MAHALICCINTA. lallai wadannan mutane da suka rike shi sun cancanci Yabo" Yace "lallai kam shi ya sanya ya kasa hada diyarsu da kowacce mace a duniya, domin sun bashi aure ne sanda kowa a duniya suka ki bashi diyoyinsu. Tsarki da iko sun tabbata ga ALLAH Mahalicccin kowa da komai, mai yin yanda ya so kuma a lokacin da ya so!" Nana tafi kowa farin ciki, wato bayan Ahmad zai zama mijinta kuma zai kasance dan uwanta na jini, ko ma ya kasance. Su ma dai a haka kowa ya kwana da abunda yake sakawa a cikin ransa, amman duk umman Ahmad tafi kowa farin ciki, don danta ya fita daga sunan shege daga masu yi masa kallon hakan. Washe gari da sassafe Alhaji Nura Kwangila da iyalinsa suka nufi gidan Malam Sulaiman. Lokacin Ahmad bai karaso ba shi da iyalinsa sai da aka Kira su a waya sannan suka taho. Alhaji Nura Kwangila ya kalle taho da manyan motoci don tafiyar har da su Umma da Hajiya Amina Su Ahmad suka iso aka fara gaggaisawa. Ma'u da Nana aka hada ido kowacce gabanta ya fadi da ganin 'yar uwarta. Shi kam Ahmad dakewa yayi ya kasa kallon inda Nana take duk da yana jinta a jikinsa a matsayin 'yar uwarsa a yanzu, amma yana jin kunyar ma'u don ba zata zaci haka ba. Nana ce da kanta ta isa inda suke ta kalleshi tana murmushi da fadin "yayana wannan ce Auntyna Ma'u?" Ya kalli ma'u yana murmushi wacce ta dan saki ranta yace "eh ita ce, kin gan ta nan Maman yarana" Nana tayi yake tana fadin "Antina ina kwana?" Ma'u ta dan saki jiki suka gaisa amma zuciyarta na bugawa. Ashe Nanan ma bata wuce tsararta ba, tayi zaton wata k atuwar mace ce irin KISAN BOKO din nan. Nana kam ta dan tsorata don ta kula Ahmad yana bala'in son matarshi ma'u da ji da ita, kuma babu wani abu da zata nunawa Ma'un, don babu wanda zai taba yin zaton Ma'un tayi auren fari balle ace har ta haifi 'ya'ya. Da aka tashi shiga mota sai tace ita motar Ahmad zata shiga, yaran suka koma motar Alhaji Nura Kwangila wanda shine ya bukaci hakan da kansa, don kallonsu faranta masa rai yake yi, don yana ganin sun fara yawa kenan cikin iyalinsu, don duk yanzu sai tsofi da dangi na can nesa. Ma'u bata so hakan ba,amman babu yanda ta iya, sai dai kishinta ya gaza boyuwa aka Nana, duk da Ahmad yana nunawa ita ce fa matarshi ta gaskiya abar sonsa. Shine mai tuka motar ma'u na kusa da shi, Nana tana baya sai suka yi kamar basu san da ita ba, suka dinga hirarsu sai jefi-jefi Ahmad ke dan tsomata yace ko kanwata? Sai tayi murmushin yake kawai har sai da tayi da ta sanin shiga motar, a yanzu kam ta gano waye Ahmad da kuma yanda ya dauki ma'u a cikin ransa bata da hadi da kowacce mace, don haka addu'a kawai ta dinka yi aka ALLAH ya kai su lafiya zuciyarta bata buga ba. Wannan abunda yayi shine ya sanyaya wa ma'u rai, ta tabbatar mijinta bai son Nana kwata-kwata kuma dukkan abunda yake gaya mata gaskiya ne. Lokacin da dangi suka ki waye Ahmad sun yi ta murna da mamaki, musamman gidan kakanninsu har yanzu matan nan nasa suna nan cikin gidan gadonsu, Alhaji Nura Kwangila shi ke musu komai tunda ALLAH bai basu haihuwa ba, aka yi ta yawo da Ahmad ana nuna shi da Sanya masa albarka, sai da suka kwana biyu a garin sannan suka koma gida. Cikin wannan kwanakin kuma Nana ta gano lallai Ahmad da Ma'u sun yi nisa, amman bata karaya ba tana nan akan bakanta don ta san idan ta zamo matarsa dole ya sota kuma yayi adalci a tsakaninsu. Duk wani mutum dake kamfani sai da yayi mamaki jin wai Ahmad dan gidan Alhaji Abdullahi yayan Alhaji Nura Kwangila ne, randa suka shiga ofis Alhaji Nura Kwangila ya mai da masa da mukamin D.G hannunsa, Nana kuma ta koma kan kujerarsa, don yace shi yafi dacewa da kujerar, sa nan ya fara nemar musu visa da passport musamman Ahmad da iyalinsa, ya kuma bayar da izinin gina wani katon gidansa da ya fara yace a cigaba da aiki, babban gida ne sosai. Sannan aka sauya Ahmad mota mallakinsa ta kansa tare da ba shi kyautar kudi masu yawa ya fara gyara gidanshi da iyalinsa kamar yadda Alhaji Nura Kwangila yace. "A dukiya irinta mahaifinka ya kamata ace ka sauya" Shi Ahmad rasa me zai yi ma da kudin yayi, sai kai ya dinga yiwa iyayensa da 'yan uwansa da Ma'u abun alkhairi da su, har Ma'un ta dinga fada akan irin kashe kudin da yake yi mai yawa haka. Ahmad yace bai yi yawa ba don bai ci ko rabin kudin da
Chapter 35 · 0% Book details