← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 40

Sashe 13

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 2 min read

murmushi. Ahamd ya kura mata ido yana kallonta, ya ma rasa wanne irin farin ciki ya kamata yayi, ya dan kalli mutanen dake kai wa DA komowa, ban da gudun baki DA ya suri matarsa yayi rawa da ita sannan ya kai ta har bakin titi inda za su hau mota, amman dai ya daure ya riko hannunta kawai yana ta wage baki tamkar mai tallan makilin yace "ma'u mai ya sanya kika boye min wannan farin labarin? Bata iya kallon fuskarsa ba don kunya. "Ni ma fa ban sani ba yaya" Zai kara magana ta katse shi "Yaya mu tafi gida mutane suna kallonmu sannan kuma yunwa nake ji" Wannan abibda ta fada ne ya sanya ya dan nutsu ya kama hannunta suka nufi titi. Shatar adaidaita sahu ya daukar musu har kofar gida. Daman ya tsaya ya sai mata abincin _Take Away_ don haka suna shiga gidan shi ya fara shirya mata a gaba yace ya cinye tas sannan tayi sallah. Alluran da aka yi mata na tsai da amai sun yi aiki sosai a jikinta, bata jin aman ko tashin zuciya a yanzu, don haka ta dan ci abincin da yawa. Ranar dai ko gurin aiki Ahamd bai iya zuwa ba, sai waya yayi ya sanar musu matarsa bata da lafiya a gayawa manaja. Ya ci gaba da kula da ma'unsa kamar zai kashe ta.
Chapter 13 · 0% Book details