Sashe 1
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry WordDocument 0Table Data DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Ma'u tana tafe cikin duhuwa tana ta sauri, burinta tayi nisa da gidan, cikin ranta tana saka ba zata je gidan kowa cikin yayyenta ba, ko gidan umma ba zata ba, domin za su iya dawo da ita gidan yaya Ahmad, shi kuma ya cigaba da dukan ta yana kulle ta cikin gidan ita daya kamar mayya. Bata ankara ba tayi karo da wani mutum, kayanta suka zube, tayi taga-taga kamar zata fadi, ALLAH dai ya sanya bata fadi din ba, mutumin ya zabga salati yana kokarin bata hakuri, sai gabanta ya hau bugawa domin muryar yayan nata ne, hakan ya sanya ta gimtse bakinta bata ce komai ba, ta suri kullin kayanta ta wuce shi DA sauri. Cikin ikon ALLAH aka kawo wuta daidai lokacin, Ahmad dake ta bata hakuri ya dan bita da kallo da mamakin jin wace ce ya buge din bata ce komai ba, har ya ayyana a cikin ranshi ko kurma ce sai kuma ya hango kamar ma'unsa ce, mamakinsa ya kara karuwa ganin tana ta sauri tayi gaba, ya fara kwalla nata kira. "Ma'u! Ma'u!! Ma'u!!!" Jikin ma'u ya dauki rawa saboda tsoro ya gama shigarta ta tsaya cak, ta kasa matsawa daga inda take, ta kuma kasa cigaba da tafiya har ya isa inda take tsaye, ya leka fuskarta don kara tabbatarwa ita ce, hankalinsa ya tashi da ya tabbatar ita ce din. Har lokacin ta kasa magana sai idonta dake zub da hawayen tsoro, kamar ya kara yin magana sai kuma ya fasa ya kama hannunta kawai ya fara tafiya. Asma'un ta fara binsa tana hawaye. Shi kenan ta shiga uku, ta san yau mai raba ta DA yaya Ahmad sai dai ALLAH. ga shi gidan babu kowa babu mai kwatar ta. Haka tayi ta binsa zaro-zaro tana rungume da kayan nata har suka shiga cikin gidan. Suna shiga ya mai da sakata ya datse, hakan ya kuma kada mata ciki ta fashe da kuka sosai, ya kalle ta har lokacin hannunta yana cikin nasa bai ce mata komai ba sai da suka dangana da cikin dakinsu. Ya zaunar da ita gefen kujera yana fadin "ina zuwa bari na zo" ya fice ya nufi daya dakin. Da sauri ya mike ta fara zagaya dakin tana kuka, hannunta bisa kanta ta fara magiya. "Don ALLAH yaya kayi hakuri WALLAHI ina daina ba zan kuma ba" Daidai lokacin DA ya shigo DA zabgegiyar belt sai ta kuma zabura ta fara ihu da karfi, ya sanya hannu bisa lebensa yana fadin "shisshi! Ki daina kuka ma'u ba dukan ki zan yi ba, ma dauko ta ne domin ku dake ni ki rama dukan da na yi miki, yanzu ma gano illar abinda na aikata, amshi ki rama ma'u" Ya mika mata belt din, mamaki ya cikata, ta fara ja da baya domin bata yarda har zuciyarshi abinda yake nufi ba kenen, ta fi yarda yana yin hakan ne don ya samu damar kama ta kawai. Ganin tana ja da baya ya sanya ya cafko hannunta gam cikin nasa, sai ta ta fara kara jikinta yana rawa, ya damka mata belt din yana fadin "da gaske nake ma'u ba dukanki zan yi ba, ki rama dukan da nayi miki in dai har zaki daina yunkurin guduwa ki bar ni ma'u" Kalamansa suka sanya ta yin saroro tana kallon shi rike da belt din a hannunta, duk da karancin shekarunta maganar yayan nata ya girgizata. Ya sakar mata hannu da belt din, ya juya ya zauna akan kujera yana mai cigaba da kallonta. "Ki daina kuka ma'u, ki rama don ALLAH gani na zauna yanda zaki iya dukana, bana fatan ki kara yunkurin guduwa, idan kika gudu na shiga uku, ban san inda zan sanya rayuwata ba, ko baki san raliya ma guduwa tayi ta bar ni da aurena ba? Ta dan zaro ido tana mamakin abinda yace, ta daure tace "da gaske raliya ta gudu, ita ma dukanta kayi ta gudu yaya? Yanda tayi maganar sai Abun ya ba shi dariya, amman ya dake yace "ban dake ta ba, kin san halin raliya ban isa ma na taba ta ba balle duka, ban so kema ki gudu, idan kika gudu kowa ba zai yafe min ba har ummata mai sona. Ki rama don na tabbatar kin huce kin ji ma'u" Tayi murmushi zuwa yanzu hankalinta ya dan kwanta, ta isa gabansa ta durkusa ta mika masa belt din tana fadin "yaya ba zan iya dukanka ba, na san ni ce nayi laifin ma, kayi hakuri ba zan kara ba" Ranshi yayi haske yace "shi kenan na hakura, amma ki min alkawarin ba zaki kara yunkurin guduwa ki bar ni ba" "ALLAH yaya ba zan kara ba, na daina ba zan yi maka irin abinda raliya tayi maka ba," "Alkawari na biyu ne mai girma ma'u, ki yi kokarin rikeshi" ta daga kai alamar to tana murmushi, ya mike tsaye. "Shikenan kin huce yanzu me kike so na dafa miki kici ki kwanta" Ta turo baki da shagwaba. "Yaya kaine kace na dinga yin Abu irin na matar aure, amma kaki bari na koyi girki, daman umma ma bata koya mini nakasai tace jagwalgwalo nake yi wai, kuma matan aure ai sune suke yin girkinsu da kansu na gani" yayi murmushi 'ma'u ko buhun shiririta' ya kamo hannunta. "Zan fara koya miki abinci daga yau, amman ba za ki fara yin girki ba har sai kin iya sosai, kin yarda da hakan? "Eh na yarda, sai randa kace nayi zan yi, ba zan kara saba maka ba' ta fada cikin hanzari. "Shikenan muje me zamu dafa? Tana biye da shi sai da suka nufi kicin din tace "danmalele da wainar fulawa mai manja" "Wannan duk ba abinci ba ne, kayan kwadayi ne kuma ni ban iya su ba. Yanzu dare yayi indomie zamu dafa da albasa mu ci" ya bata amsa. "Ai ita ma tana da dadi yaya, amman ni na iya, ita fa ba sai an sanya ta a wuta ba, idan aka jika ta DA ruwa ta dade sai ka ga ta yi laushi sai aci" Ya kalle ta DA sauri DA mamaki sai da ya fara dauko indomie din daga cikin kwali a kicin din sannan yace "waye yace miki haka ake dafa indomie? Ta sami kujera ta zauna tana dariya ganin yanda ya saki baki yana kallonta. Tace "a makarantar boarding haka muke yi tunda ba a barinmu kunna risho, kuma a kicin ma ba a barinmu sai siniyoyi kawai suke bari" "To ba haka ake yi ba, zan koya miki yanzu ki ga yanda ake yi" Ya fara kokarin bude indomie din yana zubawa a cikin tukunya, ya dauko albasa ya yanka ya zuba a kai. Tana kallonshi ya kammala hadawa ya zuba akan ruwan zafin dake kan risho ya juya ya rufe bayan 'yan mintuna ya bude. Ta rike baki "wai har ta daho kenan yaya? Lallai ta fi sauri a haka, da a makaranta ne sai ta wuni a jike " Haka dai ta dinga surutu ratata yana jin ta kawai yana murmushi har ya juye a faranti suka nufi daki, sanda suka zauna aka fara ci din ma surutun ta cigaba da yi har lokacin sai dai yayi murmushi sai dai wata tambayar data yi masa ce ta sanya shi saurin dago kai da sauri ya kalleta. "Yaya wai ya aka yi ka fasa auren aunty ummi ka auri raliya ne, bayan na san aunty ummi tana matukar sonka, me ya sa ka guje ta ja auri raliya? Ta kuma tsare shi DA ido tana jiran ya bata amsa, jikinsa yayi sanyi hankalinsa yayi matukar tashi, ta tsokano masa mikin dake ranshi wanda yayi zaton ya warke ashe har yanzu da saura. "Yaya baka ce komai ba don ALLAH ka gaya min" yayi ajiyar zuciya yana son ya shirya abinda gaya mata, sannan ya fara magana. "Iyayen ummi ne suka ce ba zata aure ni ba domin ba ni da kowa..." "Waye yace musu baka da kowa? Ba gani da umma da malam da yaya auwal da su yaya sani ba, me yasa baka gaya musu haka ba? Ta katse shi DA sauri. Yayi murmushi yace "haka ne Ina jin ummi ta gaji da sona ne shi ya sanya ta yarda da abinda iyayenta suka ce akaina" ya fada idonshi ya fara sauya kala juwa jawur. Tausayinsa ya rufe ma'u ganin yadda kamanninsa lokaci guda suka sauya ta bata fuska tace "daman an ce ai mata mayaudara ne, wata kila wani mai kudi ta gani shi ya sanya tace bata sonka, amma yaya DA aunty ummi tace bata sonka ai da ka nemi wata ba raliya ba, kasan raliya fa 'yar iska ce amman ka aure ta" Ya shiga uku yau da tambayar ma'u, amma yaya ya iya dole ya bata amsa kada tayi fishi ta gudu ta bar shi, ba tare da yin tunani ba yace "ba ina sonta bane, ba kuma ni nace a aura min ita ba, su baba ne suka yi min auren dole da ita, bana son ta" "Auren dole yaya? Da girmanka suka yi maka auren dole ka yarda? Kaga ita da bata sonka AI ta gudu, da ka sani kai ma ka gudu" "Gwara dai da ban gudu ba domin gudun nawa zai iya bata ran mutane da yawa. Kuma idan ba gudu ban san gidan wa zani ba, wata kila ma ran umma da baba ya fadi su tsine min. Shi da nagari duk abinda iyayensa suka yi masa amsa yake yi sai ya ga alkhairin a gaba" Ta kada kai alamar gamsuwa da abinda yace tana fadin "haka ne, shi ya sa ma da aka yi mun auren dole da kai nace zan zauna don kada su umma su tsine min" ya waro ido da fargaba yace "ma'u auren dole aka yi miki ba kya sona ashe? Ta rufe bakinta da sauri ta dan ja da baya. "A'a na manta kayi hakuri yaya, ba zan kuma fadin haka ba" Jikinshi yayi lakwas, gaba daya sai abincin ya fita daga ranshi,