Sashe 22
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yana fadin "gaskiya manaja ba zan iya zuba mata man nan ba" "Sai dai ka bar aikinka kuwa, waye kai da har diyar Alhaji Nura Kwangila zata Sanyaka abu kace kai ba zaka yi ba? Baka isa ba karya kake yi WALLAHI ka zabi daya ko ka zuba mata mai ko kuma ka bar aikinka" Nana taba kallonsu tana murmushin mugunta domin ta san bashi da zabi bayan ya zuba mata man. Ahmad ya girgiza kai "gara na bar aikin don ALLAH ke ciyarwa ba kai ba" manaja Saddam ya bude baki yana kallon ahmad da matukar mamaki. Ita kanta nana mamaki ya bata, bata taba ganin mutum mai taurin rai kamar shi ba. Ya juya ya nufi can gurin da ya ajiye babur dinsa da jakar kayansa. Manaja ya fara kwala masa kira yana fadin "Kai Ahmad". Amman ahmad bai waigo ba sai da ya isa ga babur dinsa ya dauko jakarsa ya cire rigar uniform ya gidan man ya sanya tashi ya cikin jaka, ya goya jakarshi a baya sannan ya kama babur dinsa ya haye kai. Mutanen dake wajen sao binsa da kallo kawai suke yi musamman nana. Ya isa inda suke tsaye ya sanya hannu cikin aljihu ya fiddo cinikin da yayi ya mikawa manaja. Manaja ya dube shi cikin takaici yace "wai kai wanne irin soko ne Ahmad? Kai yanzu da ka zuba mata man ka gwammace ka rasa aikinka? Ahmad yace "ba zuba mata man ne kawai illa a gare ni ba, zubar da mutuncina ne ba zan taba yarda bayi ba. Manaja zan iya yarda na rasa komai amma ba zan yarda na rasa mutuncina da darajar da ALLAH ya bani ta mutum dan adam ba. Na gode. Ga cinikin da nayi na wannan ranar. Yau kwanan wata ashirin idan ya cika zan zo a cire kudin kwanaki goma a bani hakkina" "Kai namijin duniya! Irinku ne suka yi mana karanci a wannan zamanin. Gaskiya ka burge ni. ALLAH ya sauya maka wani aikin mafi alkhairi a rayuwarsa" wani dattijo dake gefe guda ya fada cikin karfafa masa guiwa. Manaja Saddam ya amshi kudin jikinsa yayi sanyi, don bai yi zaton Ahmad zai iya hakura da aikinsa ba, barazana ce kawai yayi masa. Nana kam mamaki da takaici ne ya cika ta wato ita ce tayi rantsuwar banza kenan? Ahmad ya kunna babur dinsa yana goye da jakarsa a bayansa ya nufi hanyar ficewa daga gidan man. Jazuli da sauran mutane suka bishi da kallo cike da mamakin abinda ya aikata har ya fice daga gidan man. Manaja ya kalli Nana da sanyin jiki yace "Hajiya bari na zuba miki ni" "Bar shi kawai na fasa" Ta juya a fusace ta nufi motarta ta shige, jama'ar wajen suna ta cece-kuce, wadanda ke kan layi suka kalli manaja da takaici. "Malam sai ka ci gaba DA zuba mana man ko? Ya bi su DA kallo da bakin ciki yace "sai dai ku yi hakuri ku sake bin wani layin" ya bar gurin da sauri. "Amman dai wannan zalunci ne yaya zamu yi ta bin layi tun safe akan wata banza ace sai dai mu sake bin wani..." Wani tsageran mai adaidaita sahu ke fadin hakan. Sauran ma suka kama surutai da zage-zage. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Nana ta isa kofar gidansu a fusace tana danna horn da karfi, don ta fasa zuwa ofis din da tayi niyya yau. Maigadi ya tashi da sauri a gigice ya bude kofar don ya san horn din nana ne, idan har bai bude da sauri ba ranshi zai baci. Ta shiga gidan a fusace kamar zata bi ta kan mai gadin, yayi tsalle ya koma gefe daya don saura kiris ta buge shi. Ta nufi harabar gidan a fusace tayi parking din motarta ta fito ta tura kofar motar da karfi ta nufi cikin gidan da sauri a fusace. Mahaifiyarta Hajiya Batula tana falo tana kallo, masu aiki sai kaiwa da komowa suke yi suna aikinsu nana ta shigo falon a fusace. Hajiya batula ta bita da kallo da mamaki tana fadin "nana lafiyarki kuwa sai wani kumbiri kike yi? Nana ta fada kan kujera ta zauna ta dafa kai tace "mommy WALLAHI wani mutum mai girman kan tsiya na hadu da shi a gidan man daddy na nan cikin G.R.A." nana ta kwashe labarin dukkan abinda ya faru da ita ta sanar mata. Hajiya batula ta girgiza kai tana murmushi tace "ya burge ni kwarai da gaske, da za a dinga samun talakawa na muku bore irin haka da kun rage taka su" nana ta kara bata rai cikin shagwaba tace "au mommy kema abinda yayi min yayi miki daidai kenan kamar yanda zuciyarshi ta nuna masa ko?" "Eh mana to ya rantse kema kin rantse, idan shi har ya yarda ya zuba miki man, to ya zama sokon namiji abinda yayi miki shine zai tabbatar da cewa shi cikakken namiji ne ba solobiyo ba. Amma sai dai ina shawartarki da ki bar maganar nan iya nan, don WALLAHI idan daddynki yaji kin san ranki ne zai baci, bai son a wulakanta dan adam kin sani sarai" "Amma mommy ni ba a ga abin da yayi min ba?" "Kome yayi miki ai kece kika jawowa kanki. Da kika shiga gidan man kamata yayi ki fita ki isa kusa da shi ku gaisa, idan kika ga bait gane ki ba sai ki bashi sani ko kuma ki nemi manaja ya sanar da shi, amman sai ki haushi da fada da nuna masa isa da gadara kamar wata uwarsa" Nana ta mike da sauri tana turo baki cikin alamun shagwaba tace "daman na san mommy ba zaki taba goya min baya ba, da daddy ne yaji WALLAHI sai ya rama min" "Me zai rama miki bayan koran da kika ja masa daga gurin cin abincinsa? Yanzu ba zaki tunanin da me zai ci gaba DA rike iyalinsa da danginsa ba, me zai ci gaba da ba su, a ina zai samu aiki? Saboda kin zuba miki mai duk kin ruguza masa rayuwa. Ki bari baban naki yaji zaki ga yanda zaiyi dake. Duk son da yake yi miki ai bai ce ki wulakanta jama'a ba" Jikinta ya dan yi sanyi, amman har lokacin bata saduda ba ta juya DA sauri ta nufi bangarenta tana cika tana batsewa. Hajiya batula ta gyada kai tana fadin "ALLAH ya shirye ki nana" A can gidan ahmad kuwa ma'u tana tsakar gida zaune tana gyarawa Sayyada kanta da ribon, ta kammala shirya Hajiya. Shi kuma yana daki yana bacci don lokacin shekararsa daya ne. Kawai sai ta jiyo karar babur gidansu. Ko kusa ba tayi zaton mijinta bane ba, domin ta san lokacin dawowarsa bai yi ba, sai da taji ana kokarin shigowa da babur din cikin gidan sannan ta mike da sauri, tuni yaran suka yi kofar gida da gudu suna fadin "ga Abba ga abba." Ya karasa shigowa da babur din nasa yana dan murmushi. Ma'u na tsaye tana kallonsa da mamaki, ta kasa cewa komai. Ya kafe babur din ya dauki yaran kowanne a hannu daya yana musu wasa sannan ya dire su suna tayi masa gwaranci. Ya durkusa daidai tsawonsu yana taya su shirmen tsawon mintuna sannan yace "to maza aje a nunawa babar a'ilo kwalliyar domin kun yi kyau" Ai kuwa kamar jira suke yi, don dama suna son shiga gidan innar, amman mamansu ta hana su. Ya mike tsaye ya isa gaban ma'u ya lakuce mata hanci yana fadin "yaya dai 'yan mata, ko kin zama gunki ne?" Tayi ajiyar zuciya tace "yaya dai ka dawo da tsakiyar ranar nan, ban taba ganin haka ba, me yake faruwa? Ya karkada kai "babu komai kawai bana jin dadi ne" Ya nufi daki da sauri ya shiga ya bishi da kallo da mamaki, sai ta bishi dakin ta tadda shi ya kwanta a kan gado yayi rigingine amman idonshi a lumshe. Ta isa kusa da shi ta tsaya kamar zata yi magana amman sai ta fasa domin yace mata baya jin dadi. Washe gari da safe shine ya fara shirya Sayyada domin tafiya makaranta, ma'u tana kokarin kai masa ruwan wanka amma yace mata sai ya dawo daga kai Sayyada makarantar zai yi wanka. Mamaki ya kama ta shi da yake sauri idan gari ya waye ya tafi gurin aiki. Ita ce ke kai Sayyada makaranta kullum amman dai ta kyaleshi suka fice akan babur dinsa. Daga can makarantarsu Sayyada gidansu ya wuce. Ya jina suna hira da ummansa da tayi masa maganar tafiya aiki sai yace ai ya dauki hutu ne. A can gida ma'u ta gama cika domin ta gano akwai wani Abu da yake boye mata, don kwana yayi yana sallah da addu'a, ta tabbatar akwai wani abu da yake damunsa da ya ki sanar da ita. Sai da rana sannan ya iso gidan, koda ya iso bai barta ta tuhume shi ba, ya dinga kwasarta da hira daga karshe ta daure ta tamabaye shi batun zuwa gurin aiki yace yau ba zai je ba sun san bashi DA lafiya. Wasa-wasasa sai gashi ya kwashe kwana uku a gida. Yau ta kasance lahadi yana kwance a gado yana bacci, ma'u ta kammala gyaran gidan ta tadda shi a daki, idonshi biyu amma ya kurawa silin dakin yana kallo. Tunanin abinda ya kamata yayi yake yi, ba shi da wasu ajiyayyun kudi da zai iya cigaba da wata sana'ar wacce zai cigaba da daukar dawainiyar rayuwarsa. Shin mai ya kamata yayi? Wannan tunanin shi ke kai kawo a cikin ransa, sai ga ma'u ta shigo dakin. Yayi sauri ya rintse idon alamar bacci ya dauke shi, tayi dan tsam tana kallonsa, sannan ta karasa gefen gadon ta zauna ta kirawo sunanshi cikin sanyin murya. "Yaya! Yaya!!" Yayi shiru bai amsa mata ba a zuwan bacci yake yi. Ta kara matsawa kusa da shi tana fadin "na san ba bacci kake yi ba, don da ba shigo dakin idonka a bude yake, gara ma ka bude muyi maganar DA ta dace, don na gaji da kumbiya-kunbiyar da kake mini" ta kai hannunta kan kirjinsa tana masa wani