← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 40

Sashe 34

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

uba daya! Abunda ka jima kana nema, ka dauwama cikin damuwa da bakin ciki saboda shi" Mamaki da fargaba ya kama Ahmad domin har cikin ransa bai yarda da wannan maganar ba, yana ga wata makarkashiya ce kawai Alhaji Nura Kwangila ya shirya don ya auri diyarsa, banda haka ta yaya ya gano shi dan dan uwansa ne yau bai gano tuntuni ba? Kamar Alhaji Nura Kwangila ya san abunda Ahmad yake sakawa, don yana kallon irin yanayin da ya nuna. Ya fara magana "Ahmad bayan dukkan kokarin da muka yi ni da diyata na ganin ka aure ta abun ya faskara sai na taho gurin mahaifinka don neman alfarma, shine yake sanar da ni waye kai, bayan yayi min alkawarin hada aurenka da Nana." Ma'u ta kalli Ahmad da mahaifinta a gigice da damuwa hankalinta ya tashi gaba daya. Alhaji Nura Kwangila ya cigaba da maganarsa "sunan da ya fada na mahaifuyarka da cewar tana hauka ya sanya nace idan akwai hotonta ya ba ni. WALLAHI Ahmad kai dan dan uwana ne Alhaji Abdullahi" Ahmad ya kalle shi da wani irin yanayi, yanzu zancen ya fara shigarsa ya tattara hankalinshi gaba daya kan Alhaji Nura Kwangila wanda ya cigaba da bayaninsa. "Bamu da yawa cikin danginmu irin karamin iyali ne da mu, don kowanne bai wuce mutum zuwa uku ake haihuwa ba sai dai shi mahaifunmu shi daya babansa ya haifa duk da baban nashi yayi ta aure-aure don samun haihuwa bai samu ba sai shi daya kawai. Duk da ALLAH ya sanya ba mu da yawa amma muna da arziki irin na gadon da muka gada kasancewar iyayenmu asalin 'yan kasuwa ne na garin 'yanleman. Mahaifunmu Alhaji Abba bai samu haihuwa ba har sai da ya Shekara kusan goma sha biyar da aurensa duk da matansa hudu ne. Cikin ikon ALLAH a shekaru na kusan ashirin da aurensa ALLAH ya bai wa matarsa ta uku ciki, wacce ita ce ta haife mu. Mahaifinmu yayi murna Kwarai da gaske da samun wannan ciki, ALLAH ya sauke ta lafiya dan ya sami soyayya da gata gurin kowa, hatta matan suna kaunar yayana Abdullahi. Daga kanshi ba a kara haihuwa ba shi kuwa daman mahaifinmu bai sanya aka ba, don haka ya dora yayana akan harkokin kasuwancinsa tun yana da shekaru bakwai don haka don haka yafi mayar da hankali ga harkar kasuwanci tunda ya tashi, abun mamaki da dadi ga mahaifinmu shine samun cikina lokacin yayana Abdullahi yana da shekaru goma sha bakwai (17) a duniya, an fidda rai da haihuwa ALLAH Ya kawo ni, wannan ya sanya na Zama dan gata ta ko ina, amma ni na samu ilimi mai zurfi domin lokacin mahaifinmu ya fara gano amfanin ilimi. Mahaifinmu ya rasu lokacin Yayana Abdullahi yana da mata biyu ya Zama cikakken dan kasuwa. Yayana Alhaji Abdullahi ya sami nasibi a harkar kasuwancinsa da ya gada gurin mahaifinmu da yake ya dan sami ilimi kalilan na zamani, kuma yana da nasibi akan kasuwancin. Yayana shine ya dauki dukkan nauyin rayuwata, naji dadi fiye da lokacin da mahaifinmu yana raye, sai na kasance matsayin dansa kuma kaninsa. Uwargidansa ta kasa Zama saboda rashin haihuwarshi da kuma fitinar matarshi ta biyu Hajiya Lami wacce ta kasance mace mai fadan tsiya da iko.hatta ni kaina ina samun matsala da ita, fitar uwargidan ya sanya Hajiya Lami ta kara mike kafa tana yin duk abunda taga dama tsawon shekaru. Da yake Alhaji Abdullahi bai da fada balle fushi, shi ya sanya ta sami abunda take so, sannan mahaifiyarmu ma mace ce mai kau da kai, a haka har shekaru suka ja. Lokacin da na kammala sikandire yayana ya fara neman auren ASMA'U wacce ta kasance 'yar dan uwan mahaifinmu wato kakanta da namu abokan wasa ne. Dangi sun yi murna da hakan, don kwata-kwata ba za a iya cewa ga auren da aka yi na zumunci a cikin wannan iyali namu ba. Sai dai Hajiya Lami ta tayar da hankalinta ta kuma yi dukkan abunda zata iya ganin hana auren amma sai da ALLAH ya kaddara aka yi auren. Bayan an yi auren a nan ma tsugune bata kare ba duk da ba gidansu daya ba, a wannan lokacin Yayana ya biya min kudi na tafi kasar waje karatu, amman ina jin labarin gida. Hajiya Lami ta dan sassauta bala'inta ganin shekaru sun ja har kusan biyar ASMA'U bata samu haihuwa ba, sai take ganin kowa zai zauna haka ne. Shekarar da na dawo daga karatu na hada degree na da masters a shekarar komai ya faru, kasancewar yayana ya Gina katon kamfani a Kano wanda shine ya Zama na sarrafa mai da kayan abinci kuma ALLAH ya sanya nasibi a kai. Hakan ya sanya ya dauko Asma'u ya ajiyeta a nan ita kuma Hajiya Lami tana can garin mu na 'yan leman a cikin jigawa. ALLAH ya sanya nasibi da albarka akan wannan dukiya ta yayana a garin Kano, sannan kuma ALLAH ya kara saukar masa da rahamar samun cikinka Ahmad. Babu Wanda ya san mahaifiyarka na da ciki har yayi wata uku a jikinta sai da ciwo ya dameta na kai ta asiniti daga nan aka tabbatar da ciki ne da ita na tsawon wata uku. Yayana yayi farin ciki da jin wannan labari har ya kasa boye murnarshi ya sanar danginmu na can 'yan leman. Cikin kankanin lokaci labari ya fasu har ya isa kunnen Hajiya Lami. Tayi matukar bakin ciki da jin wannan labarin, ta kuma kuduri aniyar ganin bayan cikin nan. Kwatsam wata rana ina dakina kasancewar ina Kano gidan Asma'u lokacin Yayana yana can 'yan leman daga ni sai ita a gida. Cikin dare daga dakina na dinga jiyo ihu da hargowarata, abun ya bani mamaki don na san ita ba ma'abociyar rigima bace, don haka na fita da gudu sai na taddata cikin falonta tana ihu tana wurgi da duk wani abu dake cikin dakin. Na nufe ta da sauri da mamaki ina tambayarta abunda ya faru, amman sai na kula sam bata cikin hayyacinta na fara kokarin riketa amma abun ya faskara, don watsi tayi da ni gefe, na kuma mikewa da sauri na fara kokarin rike ta, a wannan karon ma ta kara watsar da ni. Da abun ya faskara sai na fice gurin Masu gadin gidan suma suka kawo mini dauki muka tura ta cikin dakin baccinta muka kulle ta a ciki. Nayi ta buga wayar gidan Yaya Abdullahi land line amma ba a dauka ba. Haka muka kwana cikin damuwa da tashin hankali, sai da gari ya waye sannan Hajiya Lami ta daga kiran ta sanar da ni yayan baya nan, da yake wancan lokacin babu wayar hannu haka na hau mota na nufi garin 'yan leman na sanarwa da iyayenmu da yayana. Muka dingumo gaba daya cikin tashin hankali da tsananin damuwa muka dawo Kano. Kai tsaye aka wuce da ita gidan nasu tabin hankali amman tsawon wata guda babu wani ci gaba da aka samu game da warkewarta, kullum sai dai a kulleta a cikin daki sai dakyar ake samu ta dan daina buge-bugen da take sai rawa da waka. Ga kuma ciki a jikinta. Daga karshe dai likitocin asibitin suka bamu shawara akan gaskiya mu gwada na aljanu don abun nata yayi kama da sammu, amman sunce zasu yi mata allurar bacci yanda zamu ji dadin tafiya da ita gida. Hakan ko aka yi bayan an mata allurar bacci muka sanya ta a bayan mota muka dauki hanyar yan leman, muna tafe nine ke tuka motar yayana yana baya kusa da Asma'u ya dora kan Asma'u akan cinyarsa. Muna tafe muna hira har bacci ya dauke yayana ya jingina da kujera ya fara bacci sosai. Kwatsam muna tsaka da tafiya sai naji an shaku wuyana an rike kam. Na fara kokarin kwatar kaina na saki kan mota ina salati ina kiran yaya don na gano Asma'u ce ta shako min wuya. Yaya ya tashi a gigice yaga abunda ke faruwa ya fara kokarin bambareta daga wuyana abun ya faskara, motar ta kara gudu tana yawo akan titi muna ta ihu da salati har hatsarin ya afku. Ba mu farka ba sai a gadon asibiti, ni kam bayan buguwa babu abun da ya same ni, yayana ya samu karaya da buguwa a baya, sai dai bayan ya farka matarshi da cikin jikinta ya fara tambaya, sai dai mummunan labari ya riske mu cewar mu kadai aka gani zube a gefen titi motarmu ta kama da wuta. Wannan ya sanya jikin yayana ya kara rikicewa don an ce matarshi ta mutu da kuma cikinsa wanda ya sanya rai da shi. Tun daga wannan lokacin har yau ba a kuma samun lafiyar yayana ba, shi da kansa yace a maidashi Saudiyya don ya fi jin dadin likitocin can da kuma Zama a can. Hakan ya sanya aka sai masa gida mahaifiyarmu ma ta koma can da Zama. Bayan ALLAH ya toni asirin Hajiya Lami ta hanyar zuwan wani dan uwanta gidan suna hira naji ashe itace ta shiryawa Asma'u wannan ciwo da bokanta. Nayi kuka saboda jin irin mugun tuggun da Hajiya Lami ta shiryawa Asma'u, na sanar da yaya abunda ya faru aka hada meeting na gaggawa na iyalinmu da Hajiya Lami na fara fadin dukkan abunda naji tana fada, nan da nan hankalinta ya tashi ta fashe da kuka tana fadin "tsautsayi ne ya kai ta ga aikata hakan" Yayana yana kuka yace ya saki Hajiya Lami saki uku! Ta sanya hannu aka tana ihu da rokon ayi hakuri ba zata kara ba, wannan ma wai tsautsayi ne da sharrin shaidan. Babu wanda ya kula ta don ta illata rayuwar yayana, ba zai kara samun macen da zata aure shi ba tunda ya Zama Mara lafiya. Wannan shine dalilin rabuwar yayana da Hajiya Lami wacce yanzu take cikin mugun hali na ciwon hauka ga rashin gata. Alhaji Nura Kwangila ya goge hawayen dake zubo masa yana dariya lokaci guda. "Naji dadi na godewa ALLAH da ya kaddara Asma'u bata rasu ba sai da ta haihu. Ina zaton ganinka Ahmad zai iya sanyawa yayana ya samu sauki daga ciwo da azabar da yake ciki tsawon shekaru, don ya kasa mantawa da matarshi Asma'u, mace tagari mai KARAMCI. Saboda kyautayi da gatan
Chapter 34 · 0% Book details