Sashe 14
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BAYAN WATA TARA Kwanci tashi babu wuya a gurin ALLAH domin zuwa yanzu cikin ma'u har ya shiga watanni na tara. Dukkan wata kulawa da gata tana samunsu a wannan ciki kamar ranshi haka ahmad ke tattalin cikinta, da ta yi motsi zai yunkuro yace "mene ne ma'u? Kai hatta wajen aiki ma ban DA dole ba zau dinga zuwa ba. Jama'a kuwa kowa ya san ma'u na da ciki tun yana watanni hudu musamman Hajiya da umma sune abokan hirar cikin da neman shawararsu kullum, sam baya jin kunyarsu in dai akan cikin nan ne. Ma'u takan yi mamakin yanda ahmad ke tsananin son haihuwa kamar yayi hauka akan kula da cikin. Aiki ma don dadi ance ana bukatar shi a wajen me dole shi yasa yake kyaleta ya tafi. Yau tana kishingide akan kujera tana kallo, ta yi wata irin kiba cikinta ya fito sosai. Ahmad ya shigo falon da sallama hannunsa dauke da manyan ledoji guda biyu. Ta yunkura dakyar tana kokarin mikewa gami da amsa sallamar. Ya karaso kusa da ita da sauri yana fadin "kin ga ban ce ki taso ki tareni ba, cigaba da hutawarki na gode" Ta yi murmushi "wato kayi mini haramiyar wannan ladan ko yaya? Kai ni ka hanani samun ladan dake cikin aure na baki daya" Ya ajiye kayan hannunsa yana murmushi "ban da ladan da kike samu ma daukar wannan cikin mai nauyi ma'u? Ya fara kokarin fito da kayan dake cikin ledojin da ya zo da su. Ta katse shi. "Yaya ka fara cin abincin kafin kayi komai bari na dauko maka" Ta sake yunkurawa zata mike tsaye, yayi saurin dakatar da ita. "Dakata ma'u, na ga alamar dai so kike sai kin tashi nan dole to ni a koshe nake" "A koshe yaya? A ina kaci abinci kuma? Ta tambaya yanayin fuskarta ya fara sauyawa zuwa damuwa. Ya lakuce mata hanci "kada kiyi kuka matata kanwata, daga gidan Hajiya nake ba wata ce ta ba ni abinci ba. Ita ce ma ta ba ni wannan kayan wanda ta tara ne weai tace a kawo miki" Ta fan saki fuska tana dariya. "To ai ka ci gurin wata matar mana idan zaka iya. Na ga kayan hajiyar" Ya daga ledar farko. "Wannan tawa ce ni na siyo su, wannan kuma na hajiyar ne, wanne zaki fara gani? Tayi shiru tana kallon ledojin duka, sai tayi murmushi ta nuna ledar da yace nashi ne kayan. Yayi dariya ya ajiye mata a gabanta. Ta ja ledar ta fara dubawa tana fadin "na san mijina dan gayu ne yafi Hajiya iya zabe" Ta fara daga kayan (over roll) ne biri da wando da takalma na jarirai da safa. Kayan sun matukar kyau, ta dinga kalla da fara'arta cikin farin ciki tana dubawa har ta kammala ta dube shi tace "yaya kayan nan sun yi kyau, ka iya zabe WALLAHI. amman kamar sun yi yawa ko? Ya harare ta a wasance "in ji wa? Yarinya da ace kudin ne da ni WALLAHI akwati ma zan ciko na kayan dana ko diyata..." "To wai yaya ma aka yi ka sami biyu ga naka ga kuma na Hajiya, ai daya ya hakura tunda daya ya siya" "Da kowa bai siyo ba fa? Ya ba ta amsa da tambaya. Bai bari tayi magana ba ya dora da jawabinsa. "Wasu kudin da muke dan karamin adashi aka hada min yau a gurin aiki, shine naje kasuwa nayo siyayyar nan, sai na yanke shawarar naje na nunawa Hajiya abinda babu sai ta gaya min na karo. To ina zuwa tana ganina ta kama fada akan me yasa da zan siyo ban yi shawara da ita ba, domin ita ma ta rigada ta siyo nata kayan. Daga karshe dai ta hado ni da natan ma tace sai na karata tunda wai bani da kunya balle kara" Ma'u tayi dariya. "Gaskiya ta fada WALLAHI ka zama wani babban maras kunya akan cikin nan, ko gaban umma da Abba baka jin kunyar yin maganar cikin nan" Yayi yake yana fadin "ma'u kenan laifina kika gani? Idan ban yi dokin cikin ba me ya kamata nayi dokinsa? Kada ki manta fa shine dan uwana jinina kuma tsatsona. Na kasance bani da kowa da ya zamto mun hada wata alaka ta jini a wannan duniyar, abibda zaki haifa ne kawai zai zamto min haka" Idonsa ya dan taru da kwalla. Jikin ma'u yayi sanyi, bata son ya dinga yin irin wadannan maganganun kwata-kwata, tun ba ta jin damuwa akan halin da yake ciki har ta fara. Ya goge wani dan hawaye da ya zubo masa ya wayance don kada ma'un taga sanda ya goge ya cigaba da maganarsa. "Ina son ki haifa min yara guda ashirin ma'u yanda zan raya sabuwar zuri'a daga bangarena nima tunda bani da kowa a wannan duniyar sai mahaifiyata mahaukaciya da ta rasu, da ace ta rayu ma da ta iya zame min abar kallo ko kuma ta kaini gurin babana da yayi mata cikin shege har aka haifeni..." Ta sanya hannu ta toshe masa baki da sauri tana kada kkowaDon ALLAH ka daina wannnan maganar" sai kawai ya fashe da kuka ya dora kansa akan kafadarta yana kuka, sai ita ma ta rasa abinda ya kamata tayi masa sai kawai itama ta fashe da kukan. Yayi shiru da sauri ya dago ido yana kallonta ya janye jikinsa. "Yi shiru ma'u, kuka bai kamace ki ba, ke fa 'yar gata ce, kina da uwa da uba DA yayye da kuma miji kuma yayanki, ni kuma bani da kowa da ya kasance jinina sai wannan abin dake cikinki. Ya shafa cikin nata yana dan murmushi. Ta kai hannu ta toshe masa bakinsa tana fadin "ya isa haka yaya idan ba so kake ka daga min hankali ba" Yayi shiru yana ajiyar zuciya, Kala manta sun ratsa zuviyarsa cikin kunnensa tace "gobe zan je aso yaya za a yi ne? "Zan kai ki idan an gama miki sai ki wuce gidan umma, idan na tashi daga aiki sai na biya ta can na taho da ke." Dadi ya cikata tana son zuwa awo, duk ranar da taje awon sai ta biya ta gidansu ta yini a can. Sai wajen karfe biyu ta kammala komai DA komai na awon, ta tako dakyar ta nufo bakin kofa, sai take jin duk jikinta yayi nauyi yanzu. Dakyar ta isa bakin titi ta sami shatar mota har gidansu. Ta biya mai mota ta shiga soro, sai ta ja ta tsaya turus! Da fargaba don ganin raliya tsaye a bakin kofar gidansu tana yin waya. Hankalin raliyar yayi kanta itama suka yiwa juna kallon-kallo, kowacce mamaki ya bayyana akan fuskarta ganin 'yar uwarta dauke da ciki. Amman raliya bayan mamaki har tsananin takaici da kishi, domin bayan ta dawo taji labarin ma'un aka aurawa ahmad, sai kuma ta ganta kwatsam da ciki babu zato babu tsammani. Ita kuma ma'u tana mamakin ganin raliya da ciki tsoho bayan ta san ba aure ne da ita ba. _"ko cikin shege tayo ne?"_ Raliya ce ta ja wani dogon tsaki ta juya cikin gidansu da sauri. Ashe fa Hajiya Raliya uwargidan Ahmadu an dawo gida daga gudun DA tayi bayan shekaru biyu. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Lami tana zaune akan benci tayi tagumi, raliya ta shiga tana kwalla mata kira da karfi. "Lami! Lami!! Lami!!!" Lami dake zaune ta dago ido ta kalle ta da sauri cikin fargaba, bakin cikin duniya duk ya isheta tace "yaya aka yi ne kike ta kwala min kira haka? Ta isa gabanta tinkis-tinkis da ciki ta zauna tana haki tace. "Yarinyar nan ma'u ce ta shigo yanzu na ganta da ciki, kuma cikin ma tsoho. Wai kina nufin har ciki ta samu da mijina? Lami ta tabe baki. "Ba gashi nan idonki ya nuna miki ba raliya? WALLAHI ko ganinki bani kaunar yi raliya, na gama kuri da cika baki akanki, amman ki dawo min da wannan abin kunyar, da wanne ido zan kalli duniya da makiyana masu neman gazawata su yi mini dariya?" Raliya ta turo baki ta kuma kumbura "haba lami sau dubu nawa zan gaya miki banyi iskanci da kowa ba, wannan cikin na ahmad ne, kwanciya yayi nayi zaton ma ya fadi tuni sai cikin watan nan ya tashi, idan ke ba ki yarda cikinsa bane waye zai yarda da ni har a kwantar min 'yancina? Lami ta kalleta ta dan fara yarda da abinda diyar tata ta fada. Lami ta kuta ta cigaba da magana. "Laifinki daya ne da baki sanar da ni kina da cikin ba, ni baki ma nuna min wata alaka ta taba shiga tsakaninku da shi ba, da na sani ai da ba zan barki ki tafi da ciki ba, ya kuma kwanta miki tsawon shekarun nan kina fama da shi. Amman dai bari babanki ya shigo dole za a yita ta kare. Idan kuma ya watsa mana kasa a ido shi ya sani, domin har shi ginin zai cinye ba mu kadai ba" *** Ma'u ta shiga cikin gidansu da sanyin jiki bayan doguwar tsayuwar da tayi cikin mamaki da fargaba. Ummanta tana zaune akan tabarma tana cin abinci ta shiga gidan da sallama. Umma ta dago kai da sauri ta kalleta ta kura mata ido, ganin yanda take tafiya kamar tana tafiya ne akan kwai. "Ke kina lafiyarki kuwa ma'u? Ma'u ta isa kusa da umma ta zauna tana nishi tace "lafiya kalau umma, wani abu na gani ya a soron gidan nan wanda ya daga min hankali" Umma tayi tsaki ta cigaba da cin abincinta tana fadin "ni WALLAHI har kin tayar min da hankali ma, nayi zaton jikin naki ne ma" Ta tura mata kwanon da take cin abincin. Dambun shinkafa ne da kun un gyada a gefe tana fadin "ki ci abinci don naga idonki yayi ciki, na san yunwa ce ke dawainiya da ke, wai ni gurin awon ba kwa cin komai ne?" Ta gyara zama ta mike kafafuwanta "umma muna ci mana akwai kwai da alala amman ni ban iya cin alala sai dai kwan" "Shi yasa kike dawowa a jigace" Umma ta bata