← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 40

Sashe 30

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin airport. Hankalinsa ya kara tashi kwarai da gaske amman ya dake. Dukkan gwaje-gwajen da ya kamata an yiwa Nana, sai dai sakamakon ya dan girgiza likitan, don haka ya ja bakinsa yayi shiru don bai kamata ya sanar da mace wannan labarin ba. Ana kiran sallar Isha'i Alhaji Nura Kwangila ya iso garin. Kai tsaye asibin Dr. Musa ya wuce, har dakin da Nana take ciki, lokacin an yi mata wata allurar barci, idonta ya rufe. Hajiya Batula kuma tana sallah. Alhaji Nura Kwangila ya isa gaban gadon da Nana kr kwance akai ya tsaya yana kallonta, sai kuma ya fara lalubo wayar Dr. Musa, da ya tabbatar masa yana cikin asibitin sai ya fita ya nufi ofis dinsa. Yana shiga Dr. Musa ya mike cikin girmamawa yana gaisheshi, amman bai kula da wannan ba cewa kawai yake yi "Dr. Musa meke damun diyata, me ya faru da ita?" Dr. Musa ya jinjina kai yace "kwantar da hankalinka Alhaji, zauna nayi maka bayani" Alhaji Nura Kwangila kamar ba zai zauna ba, amman dai ya hakura ya zauna yana kallon likita. Dr. Musa ya zauna ya dauko masa envelop a rufe kamar guda uku ya fara dubawa yana kallon Alhaji Nura Kwangila wanda ya kagu yaji abinda zai ce. Dr. Musa ya fara baya ni. "Da farko na fara yiwa Nana gwajin jini ne na tadda jininta ya hau" "Nana, me zai sanya jininta hawa kuma!? Alhaji Nura Kwangila ya tambaya a gigice. Dr. Musa yace "wannan ba shine abindake bani mamaki. Sannan bugun zuciyarta ya sauya yana gudu fiye da yanda ka'idarsa take, wannan dalilin ya sanya nace nu taho asibiti don ayi mata sauran gwaje-gwaje, ga mamaki sai naga zuciyarta ta dan samu matsala don ta buga fiye da yanda ya kamata ta buga, musamman lokacin da ta fadi, ALLAH ya taimaka anyi gaggawar kawota asibita da wani mummunan abun ya faru da ita" Hankalin Alhaji Nura Kwangila ya kuma tashi yace "abin mamaki meye zai sanya zuciyar diyata bugawa har ta kusa rasa rayuwarta?" "Kwantar da hankalinka Alhaji, wannan ba wata matsala bace, insha ALLAH komai zai zama daidai, zata dawo daidai musamman idan anyi gaggawar gano abinda ke damunta an kuma magance mata shi da wuri" Alhaji Nura Kwangila ya gyada kai yana cewa "na gode likita, bari naje gurin mahaifiyarta" Ya tsare Hajiya Batula da tambayoyi abinda ta gaya masa a can shi ta kara gaya masa a nan din ma, dole dai su bari diyar tasu ta samu lafiya tukunna. Washe gari tunda safe Ahmad yaji labarin abinda ya faru, hankakinsa yayi matukar tashi, don haka DA wuri ya wuce asibitin, ya tadda mutane anyi dandazo kama daga 'yan fadanci zuwa dangin Hajiya Batula dana Alhajin, amman ba a barin kowa ya ya shiga sai dai ko su gaisa da mahaifanta ka juya ka tafi. Shi ma Ahmad da su din ya gaisa, sai dai bai samu ganin Hajiya Batula ba tana ciki, da yake dakin irin na masu kudi ne har da wani katon falo. Nana tana bacci kamar cikin mafarki ta dinga jin muryar Ahmad lokacin da yake sallama da Alhaji Nura Kwangila. Da sauri ta bude idonta ta kalli mahaifiyarta Hajiya Batula dake zaune a kusa da ita tayi tagumi, cikin sanyin murya tace "mommy ba Ahmad ne ya zo ba? Hajiya Batula ta ce"ban sani ba KO kina son ganinsa ne? Ta daga kai alamar eh. Da sauri Hajiya Batula ta mike ta nufi falon. Alhaji Nura Kwangila ya kalle ta sauri ganin ta fito a rude yace "yaya dai Hajiya, lafiya? Cikin karewa mutanen gurin kallo tace "Nana ce tace taji muryar Ahmad wai" "Ba wai bane shine, yanzun nan ya fita, bari na kira shi idan tana son ganinsa ne" Ya dauko wayarshi ya fara neman layin Ahmad. Bugu daya ya daga Ahmad din har ya tayar da motarsa amman yace masa ya dawo maza-maza Nana na son ganinshi. Gaban Ahmad ya fadi, yaji kamar kada ya koma din, amma ba zai iya kin zuwa ba, don haka dole ya fita daga motar ya nufi dakin gabansa yana faduwa yana ta addu'a a cikin ransa. Kai tsaye Alhaji Nura Kwangila ya shige da shi cikin dakin da Nana take kwance, mutanen dake zaune a gurin suka rinka mamakin irin matsayin da Ahmad yake da shi a gurin Alhaji Nura Kwangila din da ya samu shiga gurin Nana. Nana ta kurawa kofar dakin ido, daidai lokacin da Ahmad ya shigo suka yi ido hudu, tayi doguwar ajiyar zuciya, murmushi ya bayyana akan fuskarta. Ahmad ya matsa kusa da gadon nata ya tsaya da damuwa akan fuskarshi yace "sannu Hajiya Nana, ya jikin naki? Tayi murmushi "Da sauki, na gode da ka zo duba ni, ka kula da komai kafin na koma" A zahiri kowa zai zaci tana magana ne ko taso ganinshi ne don kamfani da gaske, sai dai a kadan zuciyarta tayi haka ne kawai don ta gan shi. Alhaji Nura Kwangila da Hajiya Batula suka kalli juna da mamakin abinda tace. Ahmad yayi tsaye kamar ba zai tafi ba, sai da ya dan jima sannan yayi musu sallama ya wuce, idonsa ya ciko da kwalla saboda ganin irin halin da Nana ta shiga, idonta ya yi jawur hawaye ne kawai ke zuba daga cikinsa. Koda ya isa ofis kasa yin komai yayi, sai tunanin halin da Nana ke ciki, da ace zai iya taimakonta da yayi, amman ba zai iya bari rayuwar Nana ta lalace ba, dole zai san abin yi. Kwanaki hudu tana cikin asibitin amma babu sauki sai abin dake karuwa. Musamman ga hawan jinin gashi an yi an yi ta fadi abun dake damunta ta ki sai dai kuka. Shi kansa Ahmad tun zuwansa na farko ya kasa komawa, don bai son ganin Nana cikin halin da ya san ba zai iya taimakonta ba. So Sartse... DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. BAYAN KWANA UKU A bangaren Nana kuwa hankalin iyayenta kullum a tashe yake, yau kam Alhaji Nura Kwangila ya tabbatarwa kansa sai ya san abinda ke haddasawa diyarsa wannan halin da take ciki, don suna jin kukan da take kusan kwana tana yi indai ba a yi mata allurar bacci ba. Tana zaune a tsakar gado tana shan ice cream ya taso daga inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna a gefen hadadden gadon dake kama da na gidan wani hamshakin sarki don ya sha gyara. Cikin sanyin murya Alhaji Nura Kwangila ya kira sunanta, ta dago kai ta kalle shi gabanta yana faduwa ta amsa. Ya sake kwantar da murya yace "Nana ki taimake ni ki sanar da ni gaskiyar abun dake damun ranki? Nana ki tuna bani da kowacce diya bayan ke, ke kadai ALLAH ya bani, dan uwana guda daya ne yana kwance cikin jinya, ke kadai nake kallo a dangina kuma 'yata, idan kika bari na rasa ki na zan yafe miki ba, don babu makawa ni ma karshen rayuwata ya zo" Yayi shiru yana dan kallonta sannan ya cigaba "Nana ki taimaka ki sanar da ni abin dake damun ki, ina da kudin da zan iya siyo miki dukkan abun da kike bukata a wannan duniyar, idan kuma yafi karfin soya zan iya taya ki da addu'a ALLAH ya ba ki shi, ko kuma ya sanya sanyi da salama a cikin zuciyarki, ki fada min abun dake damun ki Nana." Nana ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na zubowa daga idanunta tace "Daddy idan na gaya muku abun dake damun zuciyata zaku ji haushina da abin, wata kila ma hakan ya sanya ku daina tausaya min" "In ji wa ya gaya miki? Dukkan abun da zai sanya shi cuta irin wannan ya wuce mu sauke shi karami. Ki gaya min Nana ko kin manta nine daddy dinki da kike gayawa dukkan damuwarki?" Ta dago kanta ta kalle shi kamar ba zata fada ba, sai tace "Daddy tun ranar da nayi wa Ahmad wulakanci a gidan mai Na fara kamuwa da sonsa, nayi zaton wasa ne ko zan rabu da son a hankali, amma sai abun ya cigaba DA hauhawa a cikin raina, har ta kai na zamto bani da buri bayan ganinsa kullum, don haka kullum sai naje gidan mansu, daga baya nayi hanyar da ya samu aiki kusa da ni, wannan ya sanya na samu sanyi a cikin raina, ban taba zaton idan na bayyanawa Ahmad bukatata zai juya min baya ba, na gwada masa dukkan abunda zai sanya ya gane ina kaunarsa amma ya kau da kansa, daga karshe da naga son sa yana neman ya hallaka ni ya sanya na sanar da shi, amma sai ya gaya min bai sona bai kuma taba sona ba..." Ta fashe da kuka maganar ta kasa ci gaba da kuka. Hajiya Batula da Alhaji Nura Kwangila suka bita da kallo da tausayawa, basu taba zaton abun dake damun diyarsu kenan ba. Wato hakan na nuna musu ta warke daga cutar dake damunta tun tana da kuruciyarta wacce suke kashe makudan kudade gurin ganin sun samar mata lafiya. Alhaji Nura Kwangila ya riko hannunta ya dora kanta bisa kafadarsa yace "Kwantar da hankalinki diyata, na san illar da soyayya take yiwa zuciyar dan adam, don ta taba illata rayuwata, amma in dai akan Ahmad ne kukanki ya kare, damuwarki ta kare, zan samar miki shi da ikon ALLAH" Ya mike da sauri "Yanzu zan je gare shi, insha ALLAH kukanki da damuwarki sun kare" Idon Nana yana zubar da hawaye tana kallon baban nata da ya nufi kofa kai tsaye zai fita. Cikin sanyin murya tace "Daddy don ALLAH idan yaji yarda kada kace zaka kore shi, ganinshi kadai abun jin dadine a gurina, kada kayi masa dole akan sai ya soni" Alhaji Nura Kwangila yayi shiru bai juyo ba, amman tabbas maganar diyar tashi ta shige shi, tausayinta ya kara kama shi, ashe akwai wani abu a wannan duniyar da diyarsa zata iya rasawa yana raye? Lallai iko yana gurin UBANGIJI. Ya kada kai ya fice. Hajiya Batula ta matsa kusa da Nana don rarrashinta. Ahmad yana zaune a ofis wayarshi ta fara kara. Ya dago da
Chapter 30 · 0% Book details