Sashe 36
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
baffansa ya tura masa cikin account dinsa ba. Rayuwa ta sauya. Daman dare daya ALLAH kan yi bature. Sun sami tafiya Saudiyya gaba dayansu Nana da Ma'u da Ahmad da yaran da Alhaji Nura Kwangila. Idan akwai wani abu dake burge Ma'u ga Nana bai wuce yanda take son 'ya'yanta ba da ji da su ba, tunda suka hadu da yaran ta share iyayen, bayan gaisawa bata kara bi ta kansu ba, don ta kula suna gab da haddasa mata dawowar ciwonta, suka dinga hirarsu da yara. Alhaji Nura Kwangila na kallonsu da dariya, ba ya ganin laifin Ahmad, ganin son da yake nunawa Ma'u don iyayenta da ita kanta yarinyar sun yi masa halaccin da bai kamata ya juya musu baya lokaci guda ba. Sannan kuma akwai SOYAYYA DA SHAKUWA mai karfi a tsakaninsu. Sun isa gidan Alhaji Abdullahi wanda yake babban gaske tun daga waje, suka tadda Hajiya Ruma a falonta tana kallo, tsohuwa mai ran karfe. Jin dadi da kwanciyar hankali sun bayyana a jikinta duk da fatarta da jikinta ya nuna tsufanta, tayi matukar mamaki da ganinsu zuwan babu zato. Bayan an gaisa ta janyo yaran gurinta cike da sha'awa. Alhaji Nura Kwangila yace "Hajiya da da hali hutu ne ya kamace mu, amman abun dake tafe da mu ba zai bar mu mu huta ba idan ba mu fada ba. Ina Yaya Abdullahi yake?" Tace "Tun safe masu hidima suka tafi harami da shi..." Tana cikin maganar sai ga shi nan an shigo da shi cikin wani keken guragu irin na masu hali mai amfani da wutar lantarki, da kansa kuma yake tafiya. Farin ciki ya cika fuskarsa da ganin Alhaji Nura Kwangila da Nana, shi kuwa Ahmad zabura yayi ya mike da sauri yana kallon mahaifinsa. Tabbas babu makawa wannan mahaifinsa ne! Sai yanzu ya gano da waye yayi kama, don yana kallon hoton mahaifiyarsa ya kasa gano kamarsu, ashe da shi yayi kama. Shi kansa Alhaji Abdullahi yaran ya fara suje gurinshi, suka tafi da gudunsu suna dariya da mamakin kekensa. Sai da aka nutsu sannan aka fara gaisawa, sannan Alhaji Nura Kwangila ya kalli yayansa yace "yaya da wa wannan matashin yayi kama?" Alhaji Abdullahi ya kalli Ahmad da sauri wanda bai maida hankalinsa akansa ba tunda ya shigo. Ya kura masa ido sai idonsa ya ciko da kwalla yace "da ace Nana Asma'u ta haihu da zan ce danta ne wannan, domin babu abun da ya taba kamanninsa da nawa lokacin da ina cikin kuruciyata. Duk inda wannan yaro ya fito jininmu ne, jinin Buba Wali wanda muka hada kaka na hudu da shi, don iyalan gidansa ne ke kama da ni" Hajiya Ruma tace "wannan haka yake" Ahmad yayi ajiyar zuciya da jin Dadi. Lallai ya kara sakankancewa wannan ne mahaifinsa. Alhaji Nura Kwangila ya mike yana murmushi ya ciro hoton Asma'u wanda take mace ya nufi Alhaji Abdullahi da shi ya nuna masa yace "yaya ka shaida wannan wace ce?" Alhaji Abdullahi ya karbi hoton ya kura masa ido, sai ya hau salati yana fadin "Subhanallahi! Wannan ai Nana Asma'u ce, Ma'una ce!" Hajiya Ruma ta mike da gaggawa ta amshi hoton, sai ta koma ta zauna tana salati tare da fadin "Nura ina ka samo hoton gawar Asma'u, yarinyar da aka ce mana ta rasu a cikin mota ta kone kurmus ko tokarta ba a samu ba?" Alhaji Nura Kwangila yayi murmushi yana kallonsu ganin duk sun gigice sannan ya fara ba su labarin abunda ya faru da Asma'u da danta da ta haifa har zuwa yau. Yana kaiwa karshe Alhaji eya kalli Ahmad yace "WALLAHI wannan shine dana, kai jinina ne, zo nan na rungume ka naji dadi don ALLAH! Ahmad ya mike da sauri ya isa ga mahaifinsa ya dora kansa bisa cinyarsa ya fashe da kuka yana goge kan kamar wani karamin yaro. Alhaji Abdullahi ya Shafa kansa yana hawaye shi ma. Ahmad ke fadin "Ashe ina da iyaye masu daraja haka na dinga shan gori da hantara saboda rashinsu, ashe ni dan gata ne gaba da baya? Amma na godewa ALLAH da iyayena da na rayu a gurinsu basu tagayyara rayuwata ba. Na godewa ALLAH da ya hada ni da ku sanda nake tsananin bukatarku" Maganganunsa sai da suka dinga sanya kowa hawaye. Alhaji Abdullahi yace "ka daina kuka Ahmadu, WALLAHI ban taba jin dadi da jinin jikina yana tafiya kamar daidai kamar na yau ba. Dana ina jin kamar zan iya mikewa tsaye yanzu, kama ni na gani zan tashi, domin naji kamar na warke babu sauran ciwo a jikina" Ahmad ya mike da sauri ya kama mahaifin nasa, sai ya mike tsaye dakyar! Amma ya kasa tsayuwa sai ya kwanta jikin dan nasa yana fadin "ashe zuciyata ce ta mike ba gangar jikina ba, nayi zaton na tashi daga yau" Alhaji Nura Kwangila ya isa kusa da shi ya kamoshi zai zaunar da shi sai Ahmad yace "bar shi kawu zan iya" wannan kalma da ya gayawa Alhaji Nura Kwangila ya Sanya shi jin wani irin dadi da nishadi. Yace "lallai yaya yanda zuciya ta warke insha ALLAHU kafafuwan ma zasu warke da yardar ALLAH" Hajiya Ruma da Ma'u sun kasa koda motsi sai hawaye. Ita kuwa Nana kallon Ahmad kawai take yi da jin dadi, dukkan sakwan sonshi na kara shiga ranta. An jima ana hira sallah ce kawai ke tashinsu, sai da dare yayi sannan kowa ya nemi makwnacinsa. Alhaji Abdullahi yana jin kamar ya lashe Ahmad da iyalinsa. Hajiya Ruma kuwa ta rike Ma'u katamau a jikinta suna jin kamar su cinyeta saboda kasancewarta mata mai son dansu, don Ahmad ya ba su labarin irin son da Umman Ma'u da iyalin gidanta ke masa. Sai dare kowa ya nemi makwancinsa. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Cikin gidan nan kowa ya koma sashinsa da yake babban gida ne, Ahmad ba zai iya rabuwa da ma'unsa sa ba, don haka sashi daya suka dauka, amman yaran suna gurin Hajiya Ruma, sai dai yini suke yi gurin Alhaji Abdullahi. Su kansu likitoci sun yarda Alhaji Abdullahi ya samu lafiya, dama sun san ba ainahin ciwon shi ya hana shi tafiya ba sai dai bakin ciki da ciwon zuciya ne wacce ta warke yanzu garas! Babu sauran rauni a tattare da ita. Kafin sati gida sai gashi ya fara kokarin mikewa tsaye. Ahmad ya mai da rayuwarshi gaba daya ga mahaifinsa yana taimakonsa, shine yake yi masa komai, wanda kullum ke kara faranta masa ranshi yana Sanya shi cikin nishadi da samun sauki. Ga ma'u kuwa tun bata sakin jiki ga Nana har ta hakura ta sakar mata saboda yanda take kaunar 'ya'yanta da janta a jikinta, da ta ga kuma kowa ya gane tana kishin mijinta ne bayan ko babu komai kanwar Ahmad ce wacce ta dalilinta mijinta ya gano danginsa. Kuma ta ga babu wani aibu na soyayyar da Ahmad yake yiwa Nana, ko ita ke yi masa, hakan ya Sanya ta ga babu amfanin cigaba da shariyar. Nanan ce ta dinga janta zuwa harami suna addu'a da salloli. Cikin zuciyar Nana addu'a take akan ALLAH ya sassauto zuciyar Ma'u ta bata Aron mijinta koda sau daya ne a Shekara. Ita kuma Ma'u godiya take yiwa ALLAH bisa rahamar da yayi musu. Wai yau ita ce a gaban dakin ALLAH mai girma, me yafi wannan dadi? Satinsu uku suka fara shirin komawa Nigeria amma Alhaji Abdullahi da Hajiya Ruma suka dage su ma sun gama zaman Saudiyya tunda mai jinyar ya samu sauki yanzu har yana tafiya da sanduna biyu irin na masu kudin larabawa, don haka tare suka tattara suka dawo Nigeria. Da yake Alhaji Abdullahi yana da gidanshi bai sauka a can ba, sai ya sauka a gidan dan uwanshi aka bada umarnin a gyara masa nasa. Cikin kwanaki uku aka sauya komai na gidan, ya koma sabo dal! Hatta fenti. Suka koma shi da mahaifuyarsu da masu aikinsu wadanda dama tare suka tafi da su can kasa mai tsarki (Saudiyya). Lokacin da aka hadu da su Malam Sulaiman da Alhaji Abdullahi, kuka kawai Alhaji Abdullahi ya fashe da shi, don ya rasa bakin da zai yi godiya ga su Malam Sulaiman, karshe yace dole zasu bar wannan gidan nasu cikin sati guda su koma wani sabo cikin rukunin gidajen da ya gina shi da iyalinsu gaba daya. Gini aka yi irin na quarters guda, manyan gidaje da manyan dakuna da za a sanya 'yan haya da amman yanzu ya zama na Malam Sulaiman da iyalinsa. Da yake Ahmad dan halak ne sai da ya sanya har da sunan Musa cikin jerin wadanda zasu mallaki gidan da Hajiyarsa. Yayyensa kuwa kowa sai da ya samu daya, ALLAH ya raba su da yawon haya, don daman kusan duk yawon haya suke yi. Yaya Auwal ne ma ya fara gini a wani filinsa rabi wanda har yau ba a yi ko rabi ba, kuma abun jin dadin kowa kyauta aka ba shi ba aro ba, da sunanka da takardun gidan mallakinka. Alhaji Abdullahi yace wannan kadai zai yi ya san yayi dan wani abu daga cikin taimakon da suka yiwa danshi. Sannan wadanda ke bukatar ajiye aikinsu suyi tare da shi, yayi musu alkawarin ninka musu albashinsu sau uku. Shi kuwa Yaya Auwal asibiti za a gina masa maimakon chemist din da yake yi a gida. Bangaren su Umma aka sanya 'yan haya da suka fara addabar Lami da gori da tsokana. Cikin wannan lokaci aka kammala ginin gidan Ahmad, Alhaji Nura Kwangila ya sanya masa komai na jin dadin rayuwar duniya, don gidan kanshi gari guda ne, don har su gama rayuwarsu wani gurin ma ba lallai su zauna a cikinsa ba. Ranar da suka shiga wannan gida daga Ma'u har Ahmad sai da suka yi kukan dadi, rayuwa ta sauya, farin ciki ya dawo sabo a gare su da duk wani mai kaunarsu. Alhaji Nura Kwangila da Malam Sulaiman sun cigaba da shirye-shiryen bikin Ahmad da Nana kamar yadda suka tsara. Ahmad ya kasa sanarwa da Ma'u don yana gudun irin halin da zata shiga, sai da ya rage saura wata daya sannan Umma tace ya kamata su sanar