Sashe 8
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hannunsa daga cikin nata yana dan ja da baya yace 'sai na dawo ma'una' ya juya da sauri ya fice. Ma'u ta kurawa kofar ido kamar ta bishi. Sai a yanzu take jin kaunar mijin nata, can a waje ta jiyo muryarsa suna gaisawa da Musa har sun dan tsaya suna hira ma. Tayi tsaye tana sauraron muryarsa. Sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama. Haka ta koma gidan salo-salo babu kwari balle karsashi a jikinta. Sanda ta isa dakin sai ta tadda babanta tuni ya tafi dakinshi, ummanta tana can da alama hirarsu suke yi ma. Ta nufi gadon da take mayatar kauna da mafarki ta kwanta, ta nannade jikinta ta lumshe ido, a hankali irin hirarrakin da suke yi ita da yayanta kafin su kwanta bacci suka dinga fado mata, sai ga idonta ya kekashe ta kasa yin barci har dare ya fara rabawa. Ummanta ta dawo ta kwanta a gabanta, sai dai lumshe ido kawai tayi har bacci ya dauke umman ma. Tana ta ayyanawa a ranta ko wane hali yayan nata ke ciki yanzu, ko ya kwanta a kan gadon ko a kan leda ya kwanta? Dakyar dai bacci ya lallabo ya saceta tana cikin tunane-tunanen yayan nata. Da safe gidan nasu cike yake da yayyanta dakan shigo su gai da iyayansu kafin su wuce gurin aiki. Yawanci sai sun ci dumame na gado a gidan sannan suke tafiya. Hakan ya sanya ta dan ji dadi, nan aka yi ta hira da cafta sannan suka watse. Shi ma malam ya nufi kasuwa, ummanta ta mike yace "maza ta tashi ta fara gyaran gida" haka nan ta wuni suku-suku babu walwala a tattare da ita, ga shi yini tayi yin aiki, sai can yamma ta samu kanta a hannun umma, ta dauko littafi ta fara karantawa. Wannan ya dan rage mata damuwa. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Ga su ahmad sai dare suka sami isa garin legas. Kai tsaye gidan da za su sauka suka isa, da yake a motar kamfaninsu suka tafi. Gida ne irin jinin legas amman babu laifi yana dw kyau. Kowa da dakinsa daban aka ba shi. Dakyar suka iya cin dan abinci suka kwanta baccin gajiya. Washe gari da safe kuma aka kwashe su a motar aka kaisu sabon gidan man mai suna 'YAN LRMAN PETROLEUM & 10 dayake duk sunan gidajen man nasa daya ne. Sun tarar da ma'aikatan gurin wanda a ranar zasu fara aiki, babban gidan kai ya gina wanda yafi na can, kasancewar shi kadai ne da shi a legas kuma na farko a jahohin kudu, dayake yana da kishin jama'arsa HAUSAWA kusan kaso sittin na ginin duk Hausawa ne sai sauran yarbawa. Basu sha wahalar fara aikin ba, kasancewar an rage kudin litar da kaso biyu (2%) cikin dari (100%) saboda gidan man sabo ne. Hakan ya sanya aka yi ta samun masu siya. A wannan rana dakyar Ahmad ya samu dan lokacin yin tunanin ummanshi da ma'unsa, kodayake ma lokacin da yana aikin ma yakan tuno su jefi-jefi, kuma a duk yayin da ya tuno da su sai yayi murmushi. *** Kwanaki suka yi ta zuwa suna wucewa zuciyoyi na kara shiga cikin damuwa. A wannan lokaci ma'un ta fara fahimtar meye aure, meye miji, domin tayi nisa cikin karance-karancen, sannan umma ta ajiye kunya tana tayi mata bayanin meye aure, me ya kunsa, mene ne alfanunsa. Wannan yake sanyawa tana kara son mijinta, idan tayi kwance a gado sai tayi ta tunaninsa, burinta bai wuce ya dawo ba, musamman lokacin da Hajiya amina ta tadda ta tana karatun littafi ta siyo mata jaka guda tace a yi ta yi. A nan ma ta samu abubuwan karuwa kwarai da gaske. Takaicinta daya tunda ahmad ya tafi bata taba jin koda muryarsa ba, kullum sai dai yaya auwal ko yaya sani ya zo yana basu labarin yace sun yi waya da shi sun gaisa. Tana son tace a bata shi idan ya kira amman ba zata iya ba sam, su kuma sun kasa yin karar su bata din. A haka har wata har watanni biyar suka cika, zuwa lokacin ma'un ta koyi abubuwa masu dama, ta kara girma ta cika ta zama budurwa domin ta cika Shekaru sha shida kenan, ga shi kullum umma sai ta bata kunun daka irin na mutanen Niger da tukudi tun bata son sha har ya Zame mata jiki, dukkan halittarta ta kammala fitowa ta zama cikakkiyar mace. Idan ta tuno abin da tayi wa mijinta a baya sai tayi ta dariya tana ganin wautarta. Gaskiya Ahmad yayi kokari tsawon shekara da wata bakwai ya zauna da ita a gidansa bai yi mata komai ba. Ta tabbar yayan nata yana matukar kaunarta a yanzu. Sai dai abun dake dmunta bai wuce rashin dawowarsa ba a yanzu, kullum sai umma tayi mita, domin ita kanta ta gaji, amma yaya auwal yace har yanzu ba a basu damar dawowa ba ne. Sai dai duk karshen wata yana yi musu aike da ta akawun (account) yaya auwal, kadan yake daukar kudin ya aiko sauran. Wannan abun shine yake farantawa malam Sulaiman rai kwarai da gaske, domin a yanzu KO bai fita kasuwa ba bai rasa abinda zai sanya a bakinsa darajar 'yayansa. Kowanne a cikin yaran nasa yana yin iyakacin karfinsa sabanin dan uwansa da yake cikin damuwa da wahala, domin dan nasa guda daya ne tal, Musa ba kuma wani karatu mai zurfi yayi ba, don haka albashin nasa bai wadatar dasu, musamman yadda lami ta dora dukkan burikanta akan kudin nasa ita da diyanta. Kafin wata ya kare lami har bashi take ci, ya kasa tsinana komai domin albashin malami na firamare ba wani yawan kirki ne da shi ba. *** INA LABARIN MUTANEN LAGOS? Ahmad yana cikin tsananin damuwa da takura saboda rashin iyalinsa da iyayensa. A yadda Alhaji Nura yayi musu alkawari watanni uku zasu yi, amma ga shi har sun shiga wata na shida, kuma watan yana neman karewa ba a ce musu komai ba. Hankalinsa duk ya tashi har ya rasa abinda zai ce a gayawa ummansa da ma'unsa, amman dai ya san suna cikin damuwa kwarai da gaske. Lokacin da suka cika watanni bakwai ya gama fusta, bai jin komai bayan ya isa ga ahalinsa, don haka lokacin da Alhaji Nura ya iso garin don ya duba yadda abubuwa suke tafiya, ahmad yaji kamar dukkan matsalarsa ta kare, don haka lokacin ya zauna mitin da su ya kuduri aniyar fadin abindake ransa. Bayan yayi yabo da jin dadi akan yadda aka samu cigaba da abin da ake bukata ga gidan man, yayi musu albishir da samun albashi mai tsoka, murna da jin dadi ya cika su, amma banda ahmad, domin yawancin wadanda suka taho kamar ba su damu da iyalinsu ba, da yawansu sun saki jikinsu suna ta mu'amalarsu har da masu ajiye daduro ma. Bayan Alhaji Nura ya gama bayaninsa ahmad ya daga hannu yana fadin"idan yallabai ya ba ni dama ina da maganar da nake son yi" Gaba daya kallo ya koma gurinsa, abokinsa Isuhu Harka ya dan zungure shi alamar kada yayi magana, domin ya san abinda zai ce, saboda kullum sai yayi musu korafi amman ahmad bai kula da shi ba. Alhaji ya kada kai "kana da damar yin magana ahmad" sai ya mike tsaye ya fara koro bayani. "Yallabai kamar yadda aka fada a baya kafin mu zo garin nan, kace watanni uku kacal zamu yi amman ga shi yanzu har mun shiga wata na bakwai, kuma watan yan gab da karewa amma babu labarin tafiya gidan, shine nake son a yi mana bayanin yadda abun yake..." "Rufe mana baki mara kunya, kai kadai kake da iyali ko bakin magana? Baka ganin wasu neman aikin suke yi ido rufe" manajan gidan man ya fadi haka bayan ya katse shi cikin tsananin bacin rai da masifa. Ahmad yace "haka ne amman ka san babu wanda ya isa ya ba wani aiki idan ba ALLAH ya kaddara ya amince ba. Ina ji a jikina aikin da nake yi yana cikin kaddarata, su kuma wadanda basu samu haka aka rubuta a littafin kaddararsu, don haka zaka iya yanke kowanne hukunci akaina" babu tsoro balle fargaba ahmad ya sake fadar maganganunsa. Manajan ya kara fusata da jin maganganun da Ahmad ya fada masa ba tare DA shakkarsa ko fargaba ba. Gurin kowa yayi tsuru-tsuru cike da tsoro musamman Isuhu abokin ahmad. Manaja ya nuna ahmad da dan yatsa cikin fushi da fusata "kai kada ka sake kayi min rashin kunya, daman na ga take-takenka dan matsiyacin ba za..." "Kai manaja dakata!" Alhaji Nura Kwangila ya doka masa tsawa. Jikin manaja ya dauki rawa, ya guntse bakinsa da sauri, domin yau dai asirinsa ya tony. Duk yanda ya so ya kare abun ya faskara. Alhaji Nura yana huci ya kalli ma'aikatan yace "a cikinku waye ya samu manaja da maganar yana son a barshi anan idan har za a dinga bashi alawus din da zai rinka aikawa iyalinsa? Kowa yayi shiru ana kallon-kallo. Manaja ya fara hada gumi, ji yake kamar kasa ya tsage ya shige cikinta saboda tsananin kunya. Alhaji Nura kwangila ya bisu da kallo daya bayan daya yace "BABU?" suka yi shiru wanda ya tabbatar masa da babu din kenan. Ya kada kai cikin takaici. "Na yi matukar bakin ciki da manaja ya aikata wannan zaluncin da sunana. Tun lokacin da kuka cika wata uku na same shi da maganar komawa ga iyalinku. Idan kuma akwai wanda yake da bukatar zama a nan legas ya ci gaba da zamansa, amma sai mutumin nan yace min ai duk kun ce a nan zaku zauna indai za a dinga ba ku alawus kuna turawa iyalinku. Nace ya ware wasu kudi ya dinga baku dukkan sati, ashe karya ce ya shirga min ba haka bane gaskiyar al'amari. Na ji dadin wannan magana da kayi ahmad ina son mutum irinka da baya tsoron fadar gaskiya duk dacinta a ko ina yake. Kai kuma manaja ka tafi gida na dakatar da kai tsawon wata uku babu albashi, mataimakinka zai maye gurbinka. Kuma dukkan mai bukatar tafiya gidan sai ya