Sashe 37
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ita don haka suka kirawo ta har gida, ta taho cikin motarta domin Ahmad ya koya mata, Umma da Malam Sulaiman suka sanya ta gaba cikin hadadden falonsu suka fara yi mata nasiha, ta kasa gane akan mene ne, sai da aka ce mata ita matar mutum kabarinsa ce, kuma shi aure nufi ne na ALLAH sannan ta gano inda maganar ta dosa. Umma tace "an sanya ranar auren Ahmad da Nana yau saura wata guda" Ma'u ta zabura a firgice tace "shi ne ba a gaya min ba don munafurci? Macuci mayaudarin banza" ta fashe ta fashe da wani uban kuka. Umma tace "ke kama bakinki mijin naki kike gayawa haka? Dukkan halaccin da yayi miki bai yi ba kenan? Yaron da ya ki komai na duniya ya gwammace ya rasa komai saboda ke amman kike fadin haka a kansa?" Malam Sulaiman yace "ai ni ya dace ta cewa munafiki kuma mayaudari, domin har yau Ahmad bai san me ake ciki akan maganar aurenshi da Nana ba, sannan bai taba cewa kala a kai ba, hasalima kamar nine nayi masa dole zai aureta tun farko, don haka ni ya dace ki gayawa haka ba Ahmad ba" Ma'u ta kara fashewa da kuka, yaya zata yi da ranta ta shiga uku, amman da iyayenta suka sanyata a gaba da nasiha da ban baki da kawo aya da hadisi sai gata ta warware ta hakura. Sanda Ahmad yayi mata waya bata dauka ba, ya dan damu da yake yaran basa gidan suna gidan babansa da kakarshi shi ya sanya su ma basu dauka sun gaya masa komai ba kamar yanda suka saba idan bata kusa da wayar, don haka ya nufi gidan kai tsaye, amman mai gadi ya sanar da shi ta fita. Sai ya wuce gidansu kai tsaye anan gidan ya tarar da ita a gaban iyayensu tayi kuka idonta yayi jajir yayi luhu-luhu. Hankalinshi ya tashi ya fara tambayarta abunda ya faru. Malam Sulaiman ne yace masa sun gaya mata maganar aurensa ne. Shima hankalinshi ya kara tashi yace "baba kun bar ni na gaya mata kun ga yanzu kun sata a damuwa, ku kalli idonta don ALLAH" Umma tace "ka ci gidanku rufe mana baki, kai da ka san yakin da muka yi da ita da baka ce haka ba, ka tadda ta tayi laushi ne yanzu akan KISHI duk yarinya tabi ta haukace" Ahmad yace "da gaskiyarki fa, ke fa Umma baki san KISHI ba tunda baba bai taba yi miki ba" Suka fashe da dariya gaba dayansu, Umma ta dauki filon kujera ta wurga masa tana fadin "kaci gidanku Ahmadu" Malam Sulaiman yace "gaskiya ya fada fa ko a gwada a gani ne?" Suka kara kwashewa da dariya ban da Ma'u dake yake kawai, ita kadai ta san me take ji a cikin ranta. Ahmad ya amshi mukullin motarta ya damkawa Malam yace zai turo direba ya amsa zasu wuce a tashi. Tun a hanya yake lallabata da rarrashinta, duk da ta nuna babu komai, kuma komai ya wuce amman ya kula a kasan ranta akwai wani abu linke da take boye masa, bai damu da ya sani ba don ya san kishin ne. Ya dinga lallabata da riritata, motsi kadan yace ma'u me kike bukata, me zan kawo miki? Sai tace babu komai kawai. Don ko me zai yi mata ba zai wanke kansa ba a wajenta. Shi da kanshi ya gano rashin kyautawar da yake yiwa Nana. Bai taba zuwa gidansu da sunan zuwa zance ba duk da kuwa halaccin da mahaifinta yayi masa ya kamata yayi musu dan wani abu da zasu ji dadi. Don haka yau daga ofis yace da Ma'u ya wuce gidan babansa amman sai ya wuce can. Ya tarar da Hajiya Batula da Alhaji Nura Kwangila suna ta hira, yawanci akan bikin ne wanda ya rage saura sati uku. Sun fi farin ciki da ganinsa ya zauna suka gaisa suka dan taba hira cikin 'yar kunya yace "kawu wai ina budurwar kauyen nan tayi ne ban gan ta ba?" Alhaji Nura Kwangila ya kalli Hajiya Batula da farin ciki fal fuskarsa yace "tana can sashinta ko tana kallo ko bacci" Ahmad ta mike tsaye yace "bari na je na tsokanota" Ya nufi sashin nata kai tsaye. Dadi ya cika su Alhaji Nura Kwangila, wannan shine karo na farko da Ahmad ya taba nuna wani abu na kulawa akan 'yarsu Nana. Alhaji Nura Kwangila ya dubi Hajiya Batula yace "kin gani ko? Na gaya miki wata rana za a wayi gari Ahmad yana son Nana. Ai jini guda ba karya ba ne" Hajiya Batula tayi dariya da jin dadi tace "lallai na yarda da fadinka Alhaji" DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Nana tana bandakinta tana wanka Ahmad ya shigo yana kwala mata kira. "Ke budurwar kauye kina ina ne?" Sam bata jiyo shi ba har ya shigo uwardakinta. Daidai lokacin ta fito daga bandakin suka yi ido hudu da juna, gaba daya jikin Nana a waje yake, don dan tawul din da ta yafa bai kai ko rabin cinyarta ba, ga kanta da wuyanta a bude, duk wanda ya san siffar kyau da tsarin mutane ba zai tsaya mamakin hakittar Nana ba wanda Ahmad bai taba kula da ita ba sai yau. Ko don hankalinshi bai taba kai wa kanta bane oho! Dukkaninsu suka yi saranda kowanne na kame. Ita kunya ce, shi kuma sani abu ya ji ya daki zuciyarshi wanda babu makawa ya san sha'awa da sonta ne yake ratsa shi. Lallai ya yarda UBANGIJI Gwanin hikima ne da ya halittawa maza auren mace sama da daya, da ya so ya cuci kansa. Ganin yadda ya kura mata ido ya sanya tayi gyaran murya sai a lokacin ya farga, kunya ta kama shi, ya juya da sauri yace "ina jiranki a falo idan kin gama shiryawa" Wani irin dadi ya shigeta. Lallai ta yarda mahakurci mawadaci ne wata rana. Bata taba ganin irin wannan kallon daga Ahmad ba sai yau. Ta yarda yanzu Ahmad din ya fara sonta kamar yadda ita ma take tsananin sonsa da kaunarsa. Tayi tsalle ta fada kan gado tana ihun murna, tare da yiwa ALLAH godiya da ya nuna mata wannan lokaci. Ta ma rasa wacce irin kwalliyar zata yi ta jima tana zabe har ta karke akan wata doguwar riga mai kama jikinta ta atamfa mai hadi da yadi da ake kawasu daga Dubai masu dan duwatsu. Rigar na dacewa da ita kwarai da gaske, kuma tayi masifar yi mata kyau. Ta fesa turaruka masu kamshi ta fito falo da ta tadda Ahmad yana ciki yana jiranta tana rangwada. Kamshin turaren da ya ji mai mai sanyi da dadi shi yasa shi yin saurin dago kai yana murmushi. Koda ya kalleta sai ya sake yin murmushi yace "eye, lallai budurwar kauye ashe kin iya kwalliya?" Ta turo baki gaba tana fadin "gaskiya yaya Ahmad bana so ka daina ce min budurwar kauye" cikin shagwaba take maganar. Yayi dariya da jin Dadi yace "shikenan na daina, zo nan ki zauna ki bani labarin kuruciyarki naji" Ta fashe da dariya ta zauna suka fara hira. Bai farga ba sai da kiran Ma'u ya shigo wayarsa, ya dubi agogon bango dake kafe a falon yaga karfe goma na dare har ta gota, ya mike da sauri yana fadin "YA SALAM! Ma'u ta gaji da jirana har ta kira ni. Bari na wuce" Nana ta hade rai da takaici a yau tana murna ta dan fara samo shi amma Ma'u ta bata mata bajat, bai kula da halin da Nana ta shiga ba sai ya nufi kofar fita daga falon. A lokacin su Alhaji Nura Kwangila sun bar falon da ya same su sun shige daki, hakan yasa Ahmad ya sake tabbatarwa lallai hirar tasu da Nana tayi nisa. Koda ya isa gida Ma'un bata gano komai ba, domin haka ya rinka bata labarin yaransu da babanshi da kakarshi da irin diramar da suke yi tana dariya. Tun daga wannan ranar kullum da dare sai yaje gurin babansa ya wuce gurin Nana. A hankali sabo da SHAKUWA ya fara shiga tsakaninsu, amman koda wasa bai taba yarda Ma'u ta gano ba. Ita kanta Nana ta gano Ahmad yana bala'in kaffa-kaffa da duk wani abu da ya shafi Ma'unsa, shi ya sanya ma bata hada kanta da ita kwata-kwata. 'Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya' in ji masu iya magana. Domin lokacin auren Nana da Ahmad yayi, Alhaji Nura Kwangila ne yayi komai, sai dai yayi adalci don duk wani abu da aka sanyawa Nana a cikin kayan lefe an sanyawa a matsayin kayan fadar kishiya. Biki ne irin na masu kudi da gata, abun dake bawa Ma'u bakin ciki shine ta rasa wanda zai taya ta bakin ciki, don gidajen 'yan uwanta dake cikin kwatas din nan kowa hidimar bikin ce a gabansa, haka gidansu, haka gidan Alhaji Nura Kwangila, haka gidan Hajiya Ruma, idan akwai mai tausaya mata bai wuce Hajiya ba sai kuma Ahmad da bai nuna damuwarshi ko zumudin auren a gabanta ba sam har takan ji kamar dole aka yi masa a ranta. Hankalin Ma'u bai tashi ba sai da aka zo daurin aure taga irin dumbin jama'ar da aka tara sannan da irin kudin da iyaye ke kashewa saboda bikin. Sai da aka zo jere hankalinta ya gama tashi don bata taba ganin kaya irin na Nana ba ko a cikin fim, don Hajiya Batula da kanta ta dinga nuna irin kayan da za a yiwa diyarta a kasar Dubai, duk da tana ganin matukar kyau da tsarin gidan sai da ta raina kanta da taga irin kayan da ake shigowa da su gidan da irin hidimar da ake yi kamar ba a son kudin. Shi kansa Ahmad irin shigar da yake yi sai take ganin kamar yanzu yafi karfi ta, don wasu dakakkun shaddoji da yaduka Alhaji Nura Kwangila ya dinko masa a Dubai, kuma a cikin gidan yake shiryawa sai dai ya shigo mata. Ran da aka daura aure farin cikinsa ya kasa boyuwa don ganin mahaifinsa ya taka kafarsa babu sanda yana hawayen farin