Sashe 40
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 2 min read
karmasasshiyar mata kamar fatalwa, matar ta fadi Lami na kokarin tashinta tana kuka, ta lallaba ta tasheta ta rungume a jikinta tana takawa dakyar! Har ta isa kusa da su ana tsaye cirko-cirko. Malam Sulaiman ne yace "Lami lafiya wacece kuma wannan? Cikin kuka Lami tace "yaya raliya ce, kusan wata hudu kenan da aka kawo ta da cuta mai karya garkuwar jiki (H.I.V.) dukkan abunda nake dashi ya kare gurin neman magani, kullum mahaifinta idan zai zo gurinka sai nace ya gaya maka sai yace a'a shi ba zai fada maka ba, shine ni kuma da naga kamar zata mutu na kwasota ko tafiya bata iya yi don ku taimaka mata" Yaya Auwal yace "raliya ce wannan Lami? Subhanallahi" Kowa ya tsorata da ganin yanda raliya ta koma, yaya Auwal yace a kaita asibitinshi zai yi mata komai kyauta, shi kuka Ahmad ya basu kudi mai yawa yace kuma duk karshen wata ta dinga zuwa gurin Ma'u tana amsar kudi. Raliya da Lami suka fashe da kuka. Umma tace "A to, duniya kenan ta fi duk yanda ka dauke ta, sakayya ce take zuwar muku" Suka kalli juna da mamaki. Tammat Bihamdullah. Nan muka kawo karshen wannan littafi mai suna DA ME AKE ADO? Abun da muka fada daidai ALLAH ya ba mu ladansa na kuskuren kuma muna rokon ALLAH ya yafe mana da zunubanmu baki daya. FAUZANKU CE take muku fatan alkhairi. SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData M5 mini TECNO LD7 WPS Office Normal Default Paragraph Font Table Normal No List Times New Roman Times New Roman Symbol Symbol Arial Arial Calibri Calibri SimSun Cambria Math Cambria Math !%),.:;>?]} $([{ 67fa022331ed479ab15cd79df714149a