← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 40

Sashe 21

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ahmad ya hango wata hadaddiyar mota ta shigo cikin gidan man. Ya jima bai ga mota jai kyan wannan motar ba. Amma ga mamakinsa sai ya ga mota ta wuce layin tana tunkaro shi kai tsaye, har ta iso kusa da shi ta ja gefe ta tsaya. Gaba daya hankalin mutanen dake kan layin yayi kan mitar musamman da horn ya fara fitowa daga cikin motar da karfi, a bayan motar an rubuta 'NANA ONE' Wani mai taxi dake jingine jikin motarsa wanda layi ya kusa zuwa kansa yace "aikin banza wai su masu kudi ba zasu bi layi ba sai dai su shigo a basu kawai" wani mai hayis dake kusa da shi yace "kai baka ga wani rainin hankali ba ma, wai ba zasu fito daga cikin motar su roki arziki ba sai dai aje a zuba musu saboda takamar suna da kudi, ko gilas din motar ma Anni saukewa. Kai 'ya'yan masu kudin garin nan suna abinda suka ga dama WALLAHI" Ahmad yana jin duk abinda suke tattaunawa a kai, a ransa cewa yake "saidai su dige a nan, amma WALLAHI idan basu bi layi ba ba zan zuba musu man ba" horn din motar ya ci gaba DA cika kunnen mutanen dake wajen, su kuma mutane suna ta surutai kala-kala. Shi kuwa Ahmad ko kallon tsiya motar bata ishe shi ba balle kallon arziki. Can sai aka bude motar a fusace aka fito. Takalma ne hadaddu cikin wata hadaddiyar kafa suka fara bayyana sannan ta karasa fitowa. Hadaddiyar budurwa ce akin farko akin farko ta fito tana sanye da doguwar riga ta yadin material mai tsada irin wacce ake yowa daga kasashen larabawa. Ta yane kanta DA dan siririn mayafi idonta sanye da gilas baki. Ta nufi ahmad tana haki kamar tayi tseren gudu. Gaba daya hankalin jama'ar dake gurin yayi kanta, wasu na fadin "ikon ALLAH ashe ma mace ce" wasu ko na fadin "ai lallai kam kya yi izgilanci don kina da kudi kuma ga kyau" shi kuwa Ahmad bai na kalli inda take ba ma balle ya san wace ce ita ko ya kamanninta suke. Ta iso ta tsaya a kansa cikin zafin rai tace "kai malam kai kurma ne baja jin horn ne? Ahmad ya dago kai ya kalle ta yana rike da bututun zuba mai yace "koda ba kurma bane ni horn dinki bai DA alaka da ni tunda ba don ni kike yinsa ba, me zai sa nace Sai na kalli inda yake fitowa? Ta Kara kumbura tace "wai kana nufin baka fahimci kiranka nake yi ka zuba min mai ba kenan? To ka sanyani har na fito sai kaje ka zuba min ko" ta rikr kugu tana wani girgiza tana kallonsa, amma ahmad bai yi magana ba, bai ma kara kallonta ba ya nufi motar dake kan layi zai zuba mata. Da yawa mutanen dake gurin abinda yayi ya burge su don wasu har sai DA suka furta. Ta bishi da sauri tana fadin "kai malam wanna irin dan rainin hankali ne kai, yaya ina yi maka magana kana wani share ni?" Ya tsaya ya kalleta cikin idonta yace "da alama kina da ciwon ido ko kuma ciwon rashin fahimta, baki kula da duk wanda ya shigo layi yake bi bane, idan har da gaske kina son man nan sai ki koma ki biyo kayi kamar yadda kowa yayi" Ya fara zuba man cikin motar dake kan layi mai motar yana fadin "ka mini daidai samari, kowa ma ai mutum ne, tun safe muke kan layi haka kawai don kina takamar kudi sai ki shigo kice sai an zuba miki, kibi layi kawai Hajiya" Maganar mutumin ta kara fusata budurwar tace "wai kai ka san wacece ni kake min irin wulakancin kuwa? Ahamd yayi dan murmushi. "Na sani mana ke yarinya ce diyar mai kudi amma kuma mara tarbiyya" ta kara fusata ainun har ma ta rasa ne zata kuma cewa. Tunda take ba a taba yi mata cin mutunci irin wannan ba. Mai zuba man dake kusa DA ahmad ya karaso yana rarrashin ahmad. "Kaga don ALLAH share ka zuba mata kawai, kaga ai macece" Ahmad ya kalle shi yace "WALLAHI ba zan zuba mata ba, da tana son taimako da sai ta zo da mutunci da girmamawa ba ta irin haka ba" "Kai din banza! Waye kai da har zan girmamaka, rashin sani wacece ni ya sanya kake yin komai, zan nuna maka kai karamin Dan iska ne yanzun nan" Ahmad yayi murmushin takaici yace "ni babu abun da ya hada alakata da iska balle har na zamo karamin danta" mutanen gurin suka sanya dariya. Jazuli abokin zuba man nashi yace"taho ki matso da motar taki gurina na zuba miki, ahmad ba kanwar lasa bane baya daukar wargi" "ALLAH ya sanya wuta ne shi amman shi zai zuba min man don dolenshi, kuma WALLAHI zan nuna masa iyakarsa yau" ta fara kokarin danna wata hadaddiyar waya dake hannunta. Jazuli ya kada kai domin ya fuskanci ita ma ban kanwar lasa bace yace "shikenan Hajiya ma ga wanda zai karya rantsuwarsa tsakanin ke da shi" ya juya ya cigaba DA aikinsa. Shi kuma Ahmad bai Kara bi ta kanta ba ya cigaba DA zubawa wadanda suke kan layi mansu suna tafiya. Daga bangaren budurwar cikin isa ta fara magana a waya. "Hello Sadam kana ina ne? Ko ma ina kake kayi gaggawa kazo gani nan a gidan manku" ta kashe wayar tana kallon ahmad tayi kwafa ta koma jikin motarta. Sarai ahmad yaji sunan wanda ta fada Saddam shine manajan gidan man DA yake aiki yanzu, amman ko dar bai ji a jikinsa ba. Jazuli ya kuma matsowa gurin daidai kunnen ahmad yace "kai abokina duk yadda aka yi yarinyar nan tana da matsayi babba, ko baka ji sunan manaja ta kira bane? Ahmad yace "sai me din ta kira sunan manaja, koda ace sunan Alhaji Nura Kwangila ta kira ni babu abubda ya shafe ni don akan aikina nake ni" Jazuli ya koma da baya ya kada kai, ya san halin Ahmad da taurin kai ba zai tankwaru ta dadi ba. Budurwar tana jiyo su sai huci take yi. Tabbas yau sai ta nunawa wannan mutumin iyakarsa zata ga da abinda yake takama. Minti biyar a tsakani sai ga motar manaja sadam tana shigowa gidan nan a guje. Kai tsaye gaban budurwa ya isa ya tsaya ya fito daga cikin motar ya isa gabanta da sauri kamar zai durkusa mata don ladabi yace "Hajiya barka da zuwa wani abu ne ya faru? Tayi murmushin mugunta tana kallon Ahmad tace "wannan ma'aikacin naku ne ke neman raina min wayo, na iso ina ta horn ya zo ya zuba min mai ya ki, har na fito NA isa inda yake nayi masa magana amma yayi min wulakanci da rashin mutunci har ana bashi hakuri akan ya zuba min yace ba zai zuba ba, shin waye shi da me yake takama? Manaja Saddam ya fusata ya waiga gurin Ahmad da sauri yace "kai ahmad baka san wacece wannan ba kayi mata rashin kunya ba, diyar mai gidan nan ce gaba daya Alhaji Nura Kwangila fa" Ko dar ahmad bai tsorata ba ya dai sakale abinda yake zuba man yace "to manaja don tana diyar Alhaji Nura Kwangila sai tazo har inda nake sana'a tace zata yi min iko da gadara? Naga ba kyauta ake biyana albashi a gidan man nan ba, sai nayi aiki da karfina da tunanina akan me zan yarda a taka ni? Da tazo da sai tayi bayanin wace ita ba wai ta dinga kallon mutane kamar dabbobi ba" "Kai malam ya ishe ka haka, wai kai dan uban waye da kake gaya min duk abinda kake so eye? Budurwar ta fada da bacin rai ganin bai ko risina ba. Kalmar uban da ta ambata ita ce ta kashe masa jiki, amman ta kara fusata shi bai DA uba ma ko matsiyaci ne balle har ace za a zageshi. Ganin yayi shiru bai ce komai ba ya sanya tayi zaton ya fara risina ne ta cigaba DA rashin mutuncinta. Manaja Saddam ya ce "don ALLAH Hajiya kiyi hakuri bari a zuba miki man" ya kalli Ahmad dake huci yace "ka dauko bututun ka zuba mata" Ahmad ya girgiza kai "kayi hakuri yallabai ai na rantse ba zan zuba mata ba, ba kuma zan yi azumin kaffara har uku saboda ita ba" Manaja Saddam ya san halin taurin ran Ahmad don haka ya kama fadan karya. "Banda shashashanci meye abin rantsuemwa akan wannan yar matsalar, ni bana son irin wannan abun da kake yi sam, baka san waye mutum ba bai kamata ka dinda saurin rantsuwa ba" Ya kalli budurwar dake ci gaba DA huci yace "Hajiya nana don ALLAH kiyi hakuri muje can gurin jazuli ya zuba miki man, bai san ke wacece ba shi yasa ya aikata hakan, amma daga yau ba zai kara ba, dole zanyi masa hukunci daidai da laifin sa" Nana ta yamutsa fuska tace "manaja WALLAHI shi ne zai zuba mini man nan, idan shi mara mutunci ne no na fishi. Dole shi zai zuna min" Ahmad ya kalle ta DA mamaki yana kada kai. Shi kansa manaja gumi ne ya karyo masa cikin ranshi yake fadin "na shiga uku! Wadanne irin yara ne wadannan marasa mutunci? Amma yaya na iya, dole a kyautatawa diyar Alhaji" don haka yace da ahmad "Kaga ahmad tunda Hajiya nana tayi rantsuwa kuma ta dage kaine zaka zuba mata kayi hakuri ka zuba mata din, idan yaso sai ka kiyaye yin saurin rantsuwa a gaba" Ahmad ya kalli nana wacce ke kallon sa tana murmushin mugunta sannan ya kalli manaja Saddam yace "gaskiya yallabai ba zan iya ba. Ai ni na fara yin rantsuwa don haka ni ya kamata ayiwa uzuri ba ita ba" "Kai ahmad bana son iskanci, yaya ina yi maka magana kana yi min gardama, zaka iya rasa aikinka akan yarinyar nan fa. Musamman idan kaki zuba mata man nan, kaje ka zuba mata kana bata mana lokaci" Gurin yayi shiru kallon ahmad kawai ake yi, gaban jazuli sai bugawa kawai yake yi, yana addu'ar ALLAH ya sanya Ahmad ya hakura ya zuba mata man nan, amma sai ga Ahmad ya girgiza kai
Chapter 21 · 0% Book details