Sashe 32
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yanzu don ya samu damar auren Nana, don haka sai tayi murmushi cikin ranta tana fadin zaka iya rubuta littafin hikaya lallai. Amman a fili cewa tayi. "Amman bai kamata ka bar Nana ta rasa rayuwarta ba bayan dumbin alkhairin da ta aikata maka ba" Tana gama fadin hakan ya mike ya bita da kallo baki bude ya gaza gano inda zancenta ya dosa, shin da gaske take yi ko kuma gatse take yi masa? Ya kamata ya ji cikakken bayani daga gare ta. Taku uku ma'u tayi a na hudun juwa ta kwasheta ta yanke jiki ta fadi tim! Ahmad ya tashi da gudu a gigice ya nufe ta yana kurma salati, ya tallafota yana jijjigata g ami da kiran sunanta amman ma'u ta suma. Ya mike da sauri ya samo ruwa ya kamota ya tallafota ya zuba mata a fuskarta ta bude idonta da sauri tana ganinta rike shi a jikinshi ta fashe da kuka ta fara kokarin kwacewa daga jikinsa amman ta kasa domin jikinta ya mutu lubus. Cikin kuka take fadin "me ya sanya baka bar ni na mutu ba Ahmad? Mamaki ya Kama shi har ya kasa boyewa ya waro ido yau shi ma'u take kira da Ahmad kai tsaye abunda bata taba fadi ba tsawon rayuwarta. A fili yace "Ahmad fa kika ce ma'u? Ta yunkura ta mike dakyar tana kuka "na fada me kuma ya rage tsakanina da kai tunda ka zama mayaudari azzalumi. Ni zaka yaudara, ni zaka cuta bayan ka tauye min rayuwa kaje kuma yanzu kace zaka auro diyar masu kudi da ilimi ban son kara ganin fuskar macuci irinka." Jiwa ta kara dibanta tayi tagal-tagal zata fadi ya mika hannunsa zai tare ta yana fadin "kiyi hakuri ki zauna ma'u, ki bari nutsuwarki ta dawo tukunna" Ta kubce daga rikon da ya so yi mata ta fada kujera ta zauna ta dafe kanta dake juyawa kamar zai fado. Ahmad ya matso kusa da ita zai kamo hannunta ta hankade hannuwan nasa tana fadin "don ALLAH ka bar ni, ka kyale ni na mutu mana, sai kaji dadin aurarta kayi abunda ka ga dama, na san ni ba diyar kowa bace illa wadda aka lika maka dole wata rana zan ga fiye da haka ma" Dakyar take magana tana fidda wani irin numfashi. Gaba daya hankakinsa ya tashi cikin lallashi yake fadin "don ALLAH kiyi shiru, ki daina magana ma'u, ki kwantar da hankalinka, WALLAHI ba zan yi abunda ba kya so ba. Bari muje asibiti bugun kirjinki ya sauya" Gaba daya ya rude ya rasa me zai yi, ya mike da sauri ya fara neman makullin motarsa ya nufi dakin baccinsu. Ma'u ta mike dakyar tana jin jiwa ta nufi wani dakin da suke ajiye shirgi ta shiga ta rufo kanta da sakata ta matsa can wani sako ta nade kai da gwiwa tana kuka, kirjinta yana zogi tana jin kamar zuciyarta zata faso ta fito waje, da ace idan ta mutu ba za a tambaye ta dalilin da ya sanya ta kashe kanta ba, da ta rataye wuyanta ta huta da wannan bakin cikin. Ahmad ya samo mukulli cikin daki ya fito, sam ya manta da yaransu dake cikin dakin suna bacci. Sai dai me bai ga kowa a falin ba, hankalinsa ya tashi kwarai da gaske ya fara nemanta a gigice. "Ma'u! Ma'u! Ina kina shiga? Daga can cikin dakin shirgin ya jiyo numfashinta na fita dakyar. Ya nufi kofar dakin ya leka ta windo duhun dake dakin ba zai bashi damar ganinta ba, sai dai yana jiyo numfashinta na fita kadan-kadan. A rude ya kira sunanta "Ma'u! Don ALLAH ki bude kofar nan kada ki cutar da kanki fa, na gaya miki na fasa ki bude don ALLAH" Bata kula shi ba sai dafe kirjinta da tayi wanda ke wani irin bugu kamar zuciyarta zata faso ta fito. Ahmad ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa, sai ya fara kokarin dude kofar da karfi amman yaji ta kam, ya fara kokarin fasa ta ya kasa, amman hankalinsa ba zai kwanta ba sai can ya koma ya dauko wani katon karfe kamar diga ya fara dukan gefen kofar dakin. Duk kwarin kofar nan sai da ya ballata don hankalinsa a tashe yake, musamman da ya daina jiyo numfashin ma'u, a zatonsa ko kashe kanta tayi. Ya banko dakin a rude ya fara laluben inda take, can ya samo ta kwance male-male, bai yi wata-wata ba ya kwashe ta don ya gano suma ta kara yi. Kai tsaye dakin baccinsu ya wuce da ita ya kwantar da ita ya kara dauko ruwa ya yayyafa mata yana kiran sunan ALLAH. Zafi da duh un dakin nan kansa azaba ce. A hankali ma'u ta bude idonta, tana yin ido hudu da shi ta kau da kanta gefe hawaye na zubowa daga idonta don jikinta yayi lakwas. Ba zata iya yin komai ba. Ya durkusa a gabanta idonsa ya ciko da kwalla kamar zai fashe da kuka yace "ma'u don ALLAH ki taimaka ki rufa min asiri, idan na rasa ki ina zan tsoma rayuwata, na miki alkawari na bar maganar Nana daga yau ma na bar kamfaninsu da gidansu, ba zan aureta ba koda zata mutu, ALLAH ya gani ba zan yarda na rasa ki ba, ki hakuri ma'u ki yafe ni" Yanda ya gigice yake sambatu ya dan sanyaya zuciyarta har ya bata tausayi tayi shiru amman fuskarta ta nuna ta dan sauko, wannan ya sanya yaji dadi yace "na kawo miki fresh milk ki sha? Ta dage kai alamar eh, ya mike da sauri ya dauko mata ya tallafota ya dinga bata tana sha har sai da ta shanye, sai ga idanuwanta sun dan fara dawowa daidai, ya kara daukarta cak kamar wata 'yar baby ya nufi bandaki da ita ya hada musu ruwan wanka cikin baho suka shiga mai dumi. Haka ya rinka tattalinta har sai da ya tabbatar ta dan huce, a kirjinsa tayi bacci. A daren ma shine ya kula da yaransu, duk wanda yace ruwa ko fitsari shine yake kai su. Fatanshi dai ma'unshi ta samu. Da safe ya makara zuwa aiiki, sai wajen karfe goma na safe ya fita saboda sai da ya tabbatar matarshi ta samu nutsuwar zuciya da ta zahiri. Fitar tashi ma kiran Alhaji Nura Kwangila ne ya ishe shi. Ma'u tace yaje kawai ta warware. Dakyar ya samu ya fita yana tunanin halin da zata shiga. Sai dai yana fita ta kara komawa daki ta haye gado ta dinga kuka don tana jin kamar ta rasa mijinta ne kawai. Malam da bai zuwa makaranta shi ya haye kanta yana mata gwaranci da surutu, sai ta rungume shi kawai tana kuka don bata san me zata gaya masa ba. A can ofis aiki ya san Ahmad a gaba amman a ranshi yana jin kamar aikin karshe yake yi don babu makawa dole zai bar ofis dinshi. ALLAH dai ya sanya yana dan adana kudi a cikin account dinsa, zai Iya kama hayar gida kafin Musa ya samu damar tashi daga nashi har ya nemi Sana'ar yi ma, lokaci yayi da ya kamata ya samu gashin kansa ma yanzu. Yana ta sakawa da warwarewa yaji an kwankwasa ofis dinsa Alhaji Nura Kwangila ne ya turo kofar ya shigo, Ahmad ya mike tsaye da sauri don girmamawa, Amma Alhaji Nura Kwangila ya Mika masa hannu da alamar ya samu guri ya zauna, babu musu ya samu guri ya zauna jikinsa a wannan karon har rawa yake don fargaba. Alhaji Nura Kwangila ya kalle shi yace"Ahmad jiya Nana bata yi bacci ba, don ban gaya mata yadda muka yi ba, nayi mata karya abunda ban taba yi mata ba tsawon rayuwata, nace mata kace ka amince zaka aureta, wannan dadin ya sanya ta kasa bacci har likita ya ba da tabbacin zuwa yanzu jininta ya sauka, ina fatan zaka taimaka min ka fitar da ni daga karyar da nayiwa diyata" Ahmad yayi shiru da damuwa yana kada kai, sannan yace "kayi hakuri kamar yadda baka son rasa diyarka haka bana son na rasa matata, halin da Nana ta shiga kadan ne akan Wanda matata ta shiga. matata da iyayenta sun min abunda ba zan iya saka musu ba, ba zan iya biyansu ba, ba kuma zan so rayuwar diyarsu ta halaka ba saboda ni. Kayi hakuri Alhaji kamar yanda na fada naka ba zan iya hada rayuwar ma'u da ta kowa ba har yanzu ina kan haka, na san mutane da yawa zasu ga wautata domin dole zan rabu da aikina da gidana da motata, amman WALLAHI hakan yafi min kwanciyar hankali don ba zan yarda na rasa ma'u ba, ba zan iya yiwa iyayena butulci ba, ka baiwa Nana hakuri ka sanar da ita ba zan manta da ita ba, ba zan manta da taimakon da tayi min ba, ka dan bani lokaci ko zuwa gobe ne zan hada kayana duk na ofis dinka" Jikin Alhaji Nura Kwangila ya mutu lakwas, hankalinsa ya tashi, ya kada kai da damuwa yace "Ahmad ka ji nace na sallameka aiki ne? Kada ka dauke ni karamin mutum, kin auren Nana bai da alaka da aikinka, sai dai ka sani idan na rasa Nana ta sanadiyyar sonka ba zan yafe maka ba har abada" Ya mike a fusace ya fita daga ofis din. Ahmad ya koma ya jingina jikin kujera, maganganun Alhaji Nura Kwangila na dawo masa. Shin da gaske ne Nana zata iya rasa ransa saboda shi? To wai rayuwar wacece tafi daraja a gurinshi tsakanin Nana da Ma'u, ban da Ummi dake can gefe tana hauka kamar ita ma zata mutu akan sonshi? Kai dole ma'u ta fi su muhimmanci a gurinshi, ita ce matarshi uwar 'ya'yanshi, 'yar uwarshi, diyar ummanshi. Da wannan tunanin ya karasa yininsa. Da ya koma gida bai tayarwa da Ma'u zancen ba, ita ma kuma bata tayar masa ba, kowa ya ja bakinsa yayi shiru. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. A bangaren Nana ta dan samu sauki har an sallameta, sai dai tana mamakin rashin zuwan Ahmad gareta indai har da gaske ya amincewa aurenta amman dai ta bar abun