Sashe 25
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya mike DA sauri yana yi mata barka da shigowa taja kujera ta zauna tana murmushi, shima ya koma ya zauna yana murmushi. Ta kalli office din nasa sannan ta kalle shi. "Ya kaga office din naka ahmad, yayi maka? Yayi murmushi "yayi mana Hajiya. Na gode ban zaci samun wannan matsayi ba, nayi interview da tunanin za a dauke ni a matsayin ma'aikaci ne wanda bani da mukamin komai, sai kuma gashi offer ta fito da babban mukami. Na gode kwarai da gaske." Tayi dan murmushi sannan tace "mahaifina Alhaji Nura Kwangila ALLAH ya hore masa dumbin dukiya, yana da kamfanoni kala-kala, amman wannan shine yafi alfahari da shi a rayuwarsa, don silar arzikinsa, asalin kamfanin na yayansa ne wanda yake kwance cikin halin jiyya a kasar saudiyya tsawon shekaru, yakan dan samu sauki lokaci zuwa lokaci ya dawo, amman da ya dawo Sai ciwon ya dawo, daga karshe ya sayi gida a can saudiyya inda ya ajiye 'ya'yansa da mahaifiyarsa a can, bamu da yawa a cikin family dinmu, don bamu da yawan haihuwa hakan ya sanya muke da karanci. Nayi karatuna tun daga primary har jami'a a kasar waje, bayan na dawo mahaifina ya damka min ragamar kamfanin a hannuna, kasancewar tsawon karatun da nayi na degree da masters duk a kan harkar kasuwanci nayi, kafin nazo kamfanin nan yana hannun wani dan abokin yayan mahaifina ne wanda daga baya muka gano yayi sama da fadi da kudi masu dama don haka aka kore shi lokacin da ya kasa kare kansa akan kudin da akan kudin da ake tuhumarsa da shi. Manajan na yanzu Alhaji Sani shima mataimakinsa aka matsar dashi gaba zuwa manajan aka baka kujerarka ta mataimaki. Kalle ni da kyau bani da shekaru amma ina da sani da gogewa akan duk wata harka da ta shafi kasuwanci da kamfani, ina fatan yanda nayi zatonka haka kake, kuma ka cigaba da kasancewa a haka domin nice na ba da shaidar waye kai da halayyarka" tayi shiru tana kallonsa. Ahmad yayi doguwar ajiyar zuciya yana fadin "na gode insha ALLAHU zan yi kokarin ganin na fidda ki kunya na gode" Ta mike tana murmushi "ayi aiki lafiya, amma za a kawo maka sabuwar laptop ta nan zamu dinga magana akwai wi-fi a ofis din zamu dinga tattauna komai ta sky-pe gmail da sauransu, sai an jima" Ta juya ta fice. Ahmad ya bita da kallo, sai yake ganin kamar mafarki yake yi wanda zai iya farkawa kodayaushe amma dai ya san zahiri ne wannan ba mafarki bane illa ikon ALLAH da bai da iyaka. Duk wani dake da alaka da ahmad ya taya shi murnar wannan cigaban da ya samu, ALLAH ya daga rayuwarshi lokaci guda, ka'idar kamfanin ce su baka gidan da zaka zauna da motar zuwa aiki indai kana babban ma'aikaci, ahmad ya so kin karbar wadannan abubuwa amma Alhaji Nura Kwangila dole ne ya karba ba wai alfarma ba ce, don haka aka bashi mukullin gida da motar hawa, dole ahmad ya karba yana godiya. Ahmad bai taba iya mota ba, don haka dole ya fara koya a ranakun da babu aiki, gidan dai bai yi saurin tarewa ba don sai yayi siyayyar da yake bukata, da wata ya kare yaji alert ya shigo ya cika da jin dadi, shi da yake daukar dubu ashirin da biyar a wata sai gashi yanzu ya koma dubu dari da hamsin, me ya fi wannan jin dadi? Umma har sai da tayi kukan jin dadi lokacin da ya isa gidan da siyayyar kayan abinci da komai na bukatarsu sannan ya bata kudi masu kauri ita da mahaifisa, 'yan uwansa ma sai da ya rarraba musu kudade. Ma'u kam tafi kowa cabawa ita da yaranta, kusan rabin albashin nasa a kyautatawa iyayensa da iyalinsa suka kare da kuma kansa, don dole sai ya sayi 'yan kayan zuwa aiki. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. BAYANA SHEKARA GUDA Shekara daya tamkar kwana ce a rayuwar dan adam! Amma ga ahmad sai yake ganinta tamkar shekara dari, don ta sauya masa abubuwa da yawa cikin rayuwarsa, hatta fatarshi da ta matarshi da yaransa ta sauya, rayuwarshi ta zama abar sha'awa ga kowa, ya samu wadataccen gida da abun hawa, sannan yana iyakacin kokarinsa a gurin aikinsa har ya shiga zuciyar Alhaji Nura Kwangila kwarai da gaske, sannan shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsa da nana. Wannan shi ne abinda ya fara taba rayuwarsa, domin nana bata shakkar kiransa ko tura masa sako ta gmail ko WhatsApp ko skype, wanda hakan ya fara damun Ma'u tun yana boye mata wacece nana har ya gaya mata gaskiyar komai. Hankalin Ma'u ya kasa kwanciya da nana, duk da mijinta yana iyakacin kokarinsa wajen nuna mata ba kowa bace nana bayan abokiyar aiki kuma uwardakinsa, amma gareta hankalinta ya kasa kwanciya, don bata son ko kalle mata miji ayi balle wata doguwar magana. Ga lami da amina kuwa, abin yafi karfinsu, sun yi hassadar sun gaji sun sallama. Amma suna cikin takaici mai yawa. Yau ya kasance ranar asabar ce babu aiki, Ahmad yana falo yana kallo, Ma'u tana ta kaiwa da komowa gurin hada musu abincin rana cikin kananun kayan da suka amshi jikinta, ba zaka taba yin zaton tayi aure ba balle ace har ta haihu bama sai idan ka sani, saboda yanzu kuruciyarta da yarintarta ke kara fitowa. Wani lokacin idan Ma'u tazo wucewa ta gaban Ahmad yakan jata jikinsa, sai ta kwace kanta dakyar ta dangwale masa hanci sannan ta wuce, ko kuma ya tsikareta yana tare mata hanya da kafa, ko dai wani abun, ma'ana ba dai zata wuce batare da yayi mata wani abun ba suna yin dariya. Ma'un tana daga kicin cikin gyara manyan kifi wanda aka fi sani da ragon ruwa, don yau farfesunsa take son yi masa don yana son farfesunsa. Ta jiyo wayarshi yana kara daga inda take, tana jiyo shi yana magana "Hajiya nana an tash shi lafiya" "Eh ina gida...aiki?... Oh my God, ba za a daga min kafa manaja yayi ba... Ok shikenan gani nan zuwa" ya kashe wayar da damuwa akan fuskarsa. Ran Ma'u ya baci amma bata motsa daga inda take ba ta cigaba da aikinta, daga can falo ahmad yayi tsaye yana sakawa da warwarewa, bai san ya inda zai tunkari Ma'u da maganar fitarshi ba, musamman yanda yaga tana cikin shirin faranta masa rai, tun jiya ta kai yaran gidan umma hutu saboda kasancewar an yaye malam sai ita daya a gidan da shi suna ta sha'aninsu. Ya dai daure yayi ta maza ya nufi kicin din. Ta jiya baya tana ci gaba DA aikinta ya lallabo ya rungumeta ta baya yanda ya saba yi mata, amman ga mamakinsa sai ya ga bata yi dariya ba yanda ta saba, sai ma cewa tayi "kada ka jefa ni cikin ruwan kifi" Ya juyo gabansa da ita yana fadin "ke yarinya bana son tsiwa" Ta lakuta masa ruwan kifin akan hanci, ganin yanda yake tsokanarta yaja da baya yana fadin "na tuba kada ki bata ni, zan dan fita na dawo yanzu" "Ina zaka je?" Ta fadi ranta a bace. Gabansa ya fadi bai son yi mata karya bai kuma son ganin ranta ya baci, wai me ya kamata yayi? Ya dake dai yace "zan fita ofis ne, yanzu aka yi kirana wasu kaya sun zo" "Amman babu wanda zai je sai kai yaya? Ina sauran ma'aikata suke?" "Dukkan abinda kika fada sai da an fada amman daga karshe an gani nine din dai ya kamata naje dole, ki yi hakuri ba zan jima ba, kin yarda? Tayi kokarin danne fushinta tace "a dawo lafiya amman kada ka dade don ALLAH yaya?" Ya sumbaci goshinta yana fadin "na gode matata" Ya juya ya fice da sauri yana murmushi. Ta bishi da kallo zuciyarta tana tafarfasa kamar zata fashe da kuka. ALLAH ya sani bata son alakar mijinta da matar nan sam. Ya isa ofis din, cikin 'yan mintuna suka kammala yin abinda zasu na shigar da kaya da komai, yana ta sauri cikin ransa ya wuce gida. Nana ta shigo ofis dinsa taja kujera ta zauna. Ya kalleta da mamaki "Hajiya baki wuce gida ba daman? Ta bata fuska "amma nace ka daina ce min Hajiya ko? Sunana nana ka fadi haka kawai" Yayi murmushi "zan kwatanta hakan" Tayi murmushi tana kallonsa "yau fa kaine zaka sauke ni a gida ahmad" Mamaki ya kama shi. "Baki zo da mota ba ne" "Na tashi da ciwon baya, direbana ya kawoni ya kuma koma nace sai na kira shi, ko akwai wani Abu da zaka yi ne? Da sauri yace"a'a daga nan gida kawai zan wuce, karki damu zan sauke ki. Yanzu zaki wuce ko sai an jima?" "Eh akwai wani dan aiki da zan karasa zaka jirani? Ta karasa maganar DA shagwaba. Yayi murmushi "ba fa Alhaji bane ni da zakiyi min shagwaba" Tayi murmushi ta mike "waye ya gaya maka shagwaba nake yi, bari dai naje na karasa na dawo" Ta fice daidai lokacin da wayarshi ta fara kara alamar kira ya shigo, tun bai dauka ba ya san wacece, don ringing din na mutum daya ne a duniya ya dora. Ya kara wayar a kunnensa bayan ya danne OK yana fadin "ya ya aka yi ne babyna?" Daga can bangaren Ma'u ta bata rai tace "wai kana kallon agogo kuwa? Ya dan yi yake, ya san meke damunta kishi ne yace "ban duba karfe nawa ba baby" Ta kuma bata rai "ka daina ce min wata baby sunana Ma'u malam, idan baka da lokacin da zaka iya kallon agogo to shikenan sai an jima" Cikin dariya yace "sorry ma'una bari na duba agogon" Ya kalli agogon da sauri sannan yace "yanzu nayi hours da fitowa, amman ki dan kara min one hour kin yarda? Idan ma ban yarda ba ya zan yi da kai. Ta kashe wayar. Ya dafe kai yana murmushi, ya fara kokarin kiranta amma bai sameta ba, da alama ta kashe wayarta ne gaba ki daya, sai yaji ransa ya sosu, sam bai son damuwar ma'u balle bacin ranta, ya kuma san ba zata kunna