Sashe 6
Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi amfani da shi a untata mata, anta ya zama mijin ta ce ya manta da ita yake bautawa sirikar sa wato ke kenan da matar sa wato arki kenan, takaici ba in ciki duk za su taru su mata rubdugu, sannan na biyu kin aurawa arki muradin ta" Tun da ta fara fa ar maganganun Umma ta yi tsai tana jin yadda take zaro magana tamkar wata computer sosai take jinjinawa walwar awar tata saboda kaifin basira tana kuma mamakin ya aka yi ita bata yi wannan tunanin ba ya aka yi tun da HEEDAYA ta fa a mata tana son ABDUL sai kawai ta hau dokin zuciya take ta sukuwa?. "Kai awata gaskiya walwar ki tana ja" Umma ta ce tana jinjinawa lamarin. "To ai shi ya sa nake fa a miki mugu shi ya san makwatar mugu, ai in ita sakarai ce bata amfani da tunani wajen yanke hukunci to wallahi da sannu sai mun nuna mata shayi ruwa ne, sai mun zame mata ciwon ido sai ta yi da na sanin ci miki mutunci a rayuwa. Ban san mai ya sa mata wasun su basu da tunani ba wai duk lokacin da za su samu labarin mijin su yana da budurwa ko zai ara aure, ko ka an basa duba cewa shi fa mijin nan nasu shi ne ya je ya ce yana son macen ba wai macen ce ta ce tana son shi ba, amma sai su hau dokin zuciya su ringa kiran budurwar a waya suna mata barazana da cewa ta rabu da mijin su ko su mata wani mummunan abu, wasu ma har gidan su budurwa ko bazawar suke zuwa su yi cin mutunci. Shin mai ya sa ba za su gane cewa mazan ne masu laifi ba? Su ne suke cewa suna son matan, sannan mai ya sa ba za su hana mazan nasu zuwa wajen matan ba sai dai su ringa tadawa macen hankali bayan ita ma zuwa aka yi aka ce ana son, shin sai yaushe mata za su gane cewa arfe aya ba ya amo?, Kawai don mijin ta zai auri awar ki sai ta ce da ha in bakin ki wato shi ba shi da laifi sai ke da ita ne masu laifi bayan baki san hawa ba baki san sauka ba" "Ai in kika ji abubuwan da mata suke yi a kan maza sai kin kama baki, kullum mata suna arar da gishirin su a dahuwar aho ne, yawanci mace ce ta fi damuwa da namiji a kan shi mijin ya damu da ita. Kullum mata ne suke shan magungunan mata don su farantawa mazan su, wasu ma basa duba da rashin ingancin maganin ko illar da zai yi wa lafiyar su, sai dai su yi ta bankawa cikin su da asan su abubuwan don kawai su birge namijin a arshe kuma ya shuka musu rashin mutunci, ko su ha u da wata cutar sanadin amfani da maganin a asan su, ke hatta planing da mata suke na haihuwa kin ta a jin namiji ya saka abin planing? Ko ya sha wata waya ta hana haihuwa, sai dai mata su sha, sai dai mata su saka a dantsen hannun su kai wasu har da wanda ake saka musu a bakin mahaifa komai dai mata ne suke yi don su birge maza amma kuma kullum matan ne a cikin damuwa da taskun rayuwa da tunane tunane da saka kishi a rai da hana zuciya sakat mazan kuma ko a kwalar rigar su sai shegen wula anci" "Wallahi" Hajiya Aisha ta fa "Yanzu dai wani hanzari ba gudu ba kin san dai Alhaji idan ya shata layi babu mai etarawa, yanzu tun da har ya yi wannan maganar to babu makawa sai an yi kin ga kenan mun bar kashi tun ran kwasa" Umma ta fa a tana jiran jin abin da Hajiya Aisha za ta ce. "Hahahaha, shi Alhaji Bashir in shi ya yi kansa? Ko dole ne aka ce miki sai mutum ya zauna jiran dama, ai mutum shi yake samarwa kansa dama" "Kamar ya?" Umma ta tambaya cike da son jin bakin zaren. "Wurin malami za mu je a gobe mu sa ya hargitsa komai ta ata komai ya mayar da komai kan HEEDAYA a yi auren da ita kin ga za ta yi farin ciki sannan za mu nuna wa Hajiya Fati a tafin hannun mu take" Wata dariya Umma ta yale da ita kafin ta ce. "Kai wallahi kin biyani Hajiya Aisha gaba aya na ji damuwata ta wanke, amma da baki ji yadda nake cikin unci da acin rai ba, ke kin ga da muka fito daga part in Alhaji yadda Hajiya Baturiya take wani aga kai tana fankama ita ala dole za su yi tuwona maina da aminiyar zancen ta" "Rabu da an iska, za su ga yadda ido zai juye da mujiya" Haka suka sha tsare-tsaren su kafin su yi sallama a kan cewa gobe Umma za ta je ta auki Hajiya Aisha su wuce wajen malamin. HEEDAYA sai da ta sha kuka tamkar ranta zai fita kafin ta tashi da luhu-luhun idanun ta, ta shiga dokawa Aunty Hafsa waya. "Hlo ar gatan anwata" "Aunty" HEEDAYA ta fa a tana fashewa da kuka. "Subhanallahi mai yake faruwa ne?" Ta tambaya hankali a tashe. "Aunty ina cikin damuwa" Ta fa a tare da kwashe komai ta fa a mata cikin kuka. "HEEDAYA dama ABDUL ne kike so? " "Wallahi Aunty ji nake zan iya mutuwa in ban same shi ba" "Haba HEEDAYA yanzu ai sai ki ha ura tun da dai Auntyn ki RABEEYA za ta aure shi... "Ni ba Aunty ta ba ce kuma wallahi na tsane ta zan iya yin komai don ganin na mallaki Ya ABDUL ciki kuwa har da kisan kai... "Kina da hankali HEEDAYA kina cikin hayyacin ki kuwa?" "Aunty na mutu a kan son shi wallahi, da aunar sa nake rayuwa komai nake zuciyata tana ha e da tunanin sa, komai na rayuwata da na tsara da shi nake tsarawa sai yanzu a rana aya a dare aya a ce zan rasa shi ba zan iya ba Aunty" "Ki nutsu ki dawo hayyacin ki, maganar RABEEYA fa ake ko walwar ki ta samu ta uwa ne kin manta cewa ar uwar ki ce ta jini uban mu aya da ita babu yadda za a yi ku auri miji aya kuma Abba ba zai ta a janye maganar sa ki auri ABDUL in ba... "Aunty ki bar ambata Ya ABDUL zai auri wata, ni ka ai ce matar sa bana son ya auri kowace mace sai ni kuma ita ma Aunty RABEEYA na tsane ta yanzu saboda ina kishin sa kishi irin wanda ban san wane iri ba ne" "Bari kawai zan yi magana da Umma" Aunty Hafsa ta ce tana yanke kiran jin tana ta mata magana tamkar ba a hayyacin ta take ba. HEEDAYA kuwa Aunty tana kashe wayar ta jefar da ita a kan gadon ta cigaba da kuka. Umma zaune take bakin gado tana ta doka murmushin jin da in shawarar da suka yanke ita da Hajiya Aisha, har ta fara hango irin mulkin mallakar da za su yi wa Ya ABDUL. Kiran Aunty Hafsa ne ya shigo wayar ta. "Hafsa" "Umma barka da dare ya gida" "Lafiya lau yau duk bamu gaisa ba ma ina kishiyar tawa Ikram" "Ta yi bacci" Shiru ya an biyo baya kafin Aunty Hafsa ta ce. "Umma wai mai yake faruwa ne HEEDAYA ta kira ni tana kuka?" "Wayyo HEEDAYA da ta yi ha uri ma burin ta yana dab da cika" "Ta ina Umma?" Kwashe komai ta yi ta fa a mata. "Haba Umma wannan ba daidai ba ne... "To uwar an wa'azi da nasiha kin fimu sanin ya kamata ne, ke mai ya sa bakya kishin uwar ki sai ta wasu? Bakya kishin ar uwar ki sai wata" "Ba haka ba ne Umma kin ga HEEDAYA yanzu ta yi candy kafin ta an huta ai mijin ta zai fito kuma duk furucin nan da take yi zafin so ne daga ta ga ya auri RABEEYA za ta ha ura" "Hafsa babu ruwanki a cikin maganar nan sai inda arfina ya are dama ban hango kyan wuri a kunnen jaka ba sai yanzu da aka bu e mini komai na gani tangararai" Aunty Hafsa jin Umma ba fahimtar ta za ta yi ba ta mata sallama ta kashe wayar tana fatan Allah ya ktauta ya ganar da su. Suna yin sallama akin HEEDAYA ta tafi a falo ta samu Mubashshar da Ihsan suna kallo, tana shiga ta mayar da ofar akin ta rufe, zaunawa ta yi a bakin gadon ta ago HEEDAYA tana lalla a ta. "Kar ki kuskura ko a mafarki ki cire son ABDUL a ranki ko ki saka dangana, ai kawai ki arawa wuta fetur na tsaye miki sai mun ga abin da ya turewa buzu na i" Sosai HEEDAYA ta ji da in wannan albishir. Washe gari Umma ta tambayi Abba a kan cewa za ta je gidan Hajiya Aisha ta duba ta ba lafiya, amma idan direba ya kaita a can zai baro ta" Nan ya amince tare da cewa ta mata sannu, lokacin da ta fito rataye da jakar ta da ta lodowa ku e za ta tafi sai ga Hajiya Baturiya ta fito daga part in ta ganin Umma sai Momma ta aga murya ta walawa RABEEYA kira fitowa ta yi Momma ta ce. "Na tafi gidan aminiyata kuma surukar ki Hajiya Fati" Ta fa a tana dariya da gayya don ta onawa Umma rai. Umma ko kallon urar da ta akko ta bata yi ba, don ta ga ko mayafi babu a jikin ta ba ma fita za ta yi ba kawai neman magana ne ita ma RABEEYA da ta fito ta gane mai Momma in ta yi juyawa kawai ta yi ta koma ciki. Direba yana sauke ta ya koma tana shiga ta ga Hajiya Aisha har ta shirya a motar ta suka fito suka tafi Hajiya Aishar ce take tu a su saboda zuwa wajen sirri ba a aukan direba. Tafiya mai nisa suka yi har sai da suka fita daga garin na Dutse, sun yi