← Book details Bonono Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 39

Sashe 34

Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

haka don wani ya san sirrin wani ba wani abu bane duk da cewa gaba aya sirrin da suke fa a a group in abu ne na da in da suke fuskanta a gidan aure. Kaf group in MANYAN MATA yanzu sun yarda cewa HEEDAYA ta fi kowa yin yadda take so a gidan mijin ta kowa tana bashi sha,awa don nata samun ya zarta hankali gaba aya ta mayar sa mijin ta sauna ko kuma shashasha bashi da burin da ya wuce faranta mata don ita ka ai yake kallo, ya manta da mahaifiyar sa da sauran duk wasu abubuwa komai nasa HEEDAYA sai dai duk abin nan da ake abin bai yi tasirin rabuwa da arsa ba yana bata kulawa duk da hakan ma HEEDAYA ta saka a ranta sai ta saka Little RABEE ta zama tarihi a zuciyar sa don da ita take kishi a yanzu ita kuma ta fi so ya zamana daga ita sai an da za ta haifa nan gaba ne take so su kasance a zuciyar sa, tun da a halin da ake ciki yanzu babu haihuwa a tsarin ta a cewar ta sai ta gama cin duniyar ta da tsinken tsire don haka ma take yin tsarin haihuwa wato planning. Umma yanzu babu abin da take sai turawa Momma haushi saboda ta san Momma ta auki son duniya ta ora a kan Little RABEE amma kuma an wace ta a hannun ta yanzu tana hannun su tun da HEEDAYA ce a gidan ita kuma wannan abun yana ci mata tuwo a warya. "Aminiyata Husna wallahi sha uwata da ke na auke ki tamkar ar uwata shi ya sa nake kwashe duk wani abu da ya shafe ni nake fa a miki, yanzu ina so ma in saka rana in zo har garin kano domin in ganki a zahiri ba kamar yadda muka san juna a hoto ba" HEEDAYA ta tura mata sa on lokacin suna chatting. "Allah sarki ai ni ma na matsu mu ha u yadda muke in nan babu abin da bamu sani ba da ya shafi rayuwar mu ya kamata wani ya ziyarci wani" "Kar ki damu tun da shi HAMEED ba zai kawo ki ba tun da ba shi da lokacin ki ni zan saka ABDULHAKEEM ya kawo ni" "Ka ji matar so wallahi aminiyata soyayyar ku tana birge ni kin tsinci dami a kale a yanzu ba duka maza ba ne suke ba mace kulawa da soyayya ta zama tana cikin jin da in rayuwa kamar yadda kike ji, kina gani dai hatta uku bala'in da kika aiko mini na yi amfani da shi a banza duk da dai an samu sauyi amma dai ke kam ta dabance ina fatan Allah ya ara ora ki a kan mijin ki har arshen rayuwar ku" "To amin amma dai ni kin san ba zan ta a yarda na zauna namiji ya ci abinci a kaina ba duk wani cin kashi ya mini ba" "To ai ba daga macen ba ne kowace mace za ta so ta samu komai na rayuwar aure da kwanciyar hankali da kulawa da soyayya sai dai idan bata samu ba ya za ta yi?" HUSNA ta jefa mata tambayar. "Ni ai kin san bana zama kullum ku ina suna wajen malamai da bokaye ai kuwa ina ganin biyan bu ata don ga shi da orafin gidan aure sai dai in ji ana yi" "Haka ne amma ni ba zan iya bin malamai da bokaye ba a kan namiji in ata lahirar ta don hakan shirka ne" "Yo ai sai ka nemi gafara ni kam gwara in gwara kan namiji yanzu fa Ya ABDUL ko uwar da ta haife shi sai na ga dama nake barin sa ya je gaishe ta in ma ya je sai dai in ni na masa umarni in bam bashi ba kuwa wallahi ko za a auki watanni ko gidan su ba zai je ba ke ko kallon gidan ba zai yi ba ga shi dai zai je gidan mu gaishe da uwata amma ba zai shiga gidan su ba sai in ni na ce kin ga kuwa ai kwalliya tana biyan ku in sabulu don in ba haka ba da yanzu na zama sorry a gidan nan" "Kina yadda kike so aminiyata" "To ke ya kika gani, ai shi ya sa daga ni babu ari ke ni fa na saka a raina dama a duniya dai babu wata mace da Ya ABDUL zai mata kallo na so ke har jaddada masa nake cewa ko fita ya yi kar ya yi wa kowace a mace kallo sau biyu, ya kan ce mini ai in ma daina tunanin zai ga wata mace da sunan so don daga ni ya rufe ofa har gaban abadah" "Kin ciri tuta ai nake fa a miki matsalar mata kishiya ce don baka ara sanin mene ne zaman aure sai kana da abokiyar zama" "Hahaha! Ai ni dama don ma na san babu ita a tsarina ba zan ta a ma yarda ba Ya ABDUL nawa ne na ni ka ai!. Don ni aka halicce shi, wallahi duk ranar da na bu i ido na ga an mini kashiya ko ta iyar kara ce na tabbata mutuwa zan yi" "Ai shi ma ba zai ma fara ba kawai ki cigaba da gashi kuma ki saka a ranki baki da kaishiya a gidan auren ki don kin kasa kin tsare aminiyata" Wa annan kalaman ne suke sanya HEEDAYA ta ji kanta ya fashe a duk lokacin da HUSNA ta mata su awa aya tamkar da miliyan a cewar ta kenan yanzu yadda take baje sirrin ta na gidan aure hatta magungunan mata da yadda suke mu'amalar aure da mijin ta babu wanda take ragewa sai ta fa awa HUSNA ko MEEMA bata sanin wasu abubuwan kamar yadda take kwashewa take fa a mata, hatta magani in ta yi amfani da shi da yadda mijin ta ya yaba a kan yadda ya same ta sai ta fa awa HUSNA. Ita kuma HUSNA baiwar Allah babu wani abu da take auka a gidan HAMEED sai takaici kamar dai yadda aka saba don shi har yanzu bai damu danita ba ita kuma da a ce zai nuna mata kulawa ko yaya ne da sai ta ji babu ya ita a duniya kai ita ko dai zai auro mata uku ne babu ruwan ta amma dai ga shi ita bata samu komai ba daga gare shi na ha in auratayyar shi ya sa ko a group in idan ana hirar mazaje take jan bakin ta ta yi shiru saboda ita ko gutsuren abin da suke samu ba samu za ta yi ba ha urin man dai shi take yi tana neman za i da mafita daga ubangiji. *BAYAN WATA BIYU* Yau ne HEEDAYA ta shirya domin zuwa garin Kano ta kaiwa HUSNA aminiyar ta ta online ziyara kowa cike yake da oki da murnar ha uwar sa da wacce ya saba. HEEDAYA tana ta Alla-alla su isa Kano kawai so take ta ga HUSNA. HUSNA ma a nata angaren haka ne ta shirya musu tar a ta musamman suna waya da HEEDAYA har suka iso ofar tangameman get in gidan in da mai gadi ya wangale musu get in Ya ABDUL ya kutsa hancin motar ciki. HUSNA da ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda farin ciki tana tsaye a harabar get in, motar tana tsayawa ta taho wajen da sauri, Ya ABDUL ne ya fito ya zagaya ya bu ewa HEEDAYA ofa hannu ta mi o masa ya kamo ta ta fito da sauri suka rungume juna ita da HUSNA cike da tsananin murnar ha uwa. Shi kuwa yana ta musu dariya a haka suka saki juna HEEDAYA da HUSNA suna ri e da hannun juna suka shige cikin gidan Ya ABDULA yana biye da su tana fa in an nuna masa wariya. Bayan an gaisa ta gabatar musu da abinci suka ci sai Ya ABDUL in ya ce zai je wajen wani abokin sa ya dawo nan HEEDAYA ta ringa fa a masa ya kiyaye ban da kallon mace sau biyu don hakan ganganci ne da wasa da ranta sumbatar ta ya dawo ya yi a gaban HUSNA yana fa in ai shi nata ne babu wata mace da zai iya kalla da sunan so don sauran mata ma kallon muciya da zani yake musu ita ka ai yake wa kallon mace. HUSNA dariya take ra musu bayan fitar sa ta ringa cewa gaskiya sun dace da juna mijin ta rana aunar ta. Hira suka cigaba da yi har sai da ta dawo kafin ya fito da tsarabar da suka kawo mata tana ta godiya bayan kayan matan da HEEDAYA ta jibgo mata. Tata tsarabar ta bayar wanda kayan yara ne masu kyau ta tsada ta ce su kai wa Little RABEE da kewar juna suka rabu HEEDAYA da HUSNA suna ta agawa juna hannu. Ha uwar da suka yi a zahiri ya ara dan on zumuncin su tare da sha uwar su. HEEDAYA da take aga kai da hanci a group tana nuna ta fi kowa shawo kan mijin ta musamman da wasu daga cikin matan group in suke fasa mata kai. Yanzu tsabar jijji da kai ma har ta fara share MEEMA idan ta mata magana sai ta ga dama za ta amsa. "Wai HEEDAYA mai na miki ne kwana biyun nan na ga ko a group na MANYAN MATA in kika yi magana na yi magana sai ki wa kowa replay ki share magana ta anya hakan daidai ne kuwa amma in wani abu na miki ki yi hakuri" Haka MEEMA ta rubuta ta tura mata amma sai bayan kwana biyu ta mata replay da cewa "Babu abin da kika mini ra'ayi ne kawai kin san kuma hausawa sun ce ra'ayi kukan jaki" "Ban gane ba, ai na ce ki yi ha uri ko na miki wani laifin cikin rashin sani" "Ni fa babu abin da kika mini" "Wai yanzu don a kan HUSNA na ne kike share ni kar ki manta ni fa awar ki ce ta kusa tare muka yi karatu kuma duk wani mataki da kika taka a gidan ABDULHAKEEM ni ce sila ko
Chapter 34 · 0% Book details