Sashe 38
Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kin auka duk ba mu san abin da yake faruwa ba? To ki sani yanzu kiwon mutum ake kiwo ba dabba ba" Kamar ta sha e Hajja haka ta ji nan ta baro gidan ta rasa ya za ta yi. Sannan babu ma wanda ya fa a mata wace ce amaryar bare ta je ta auki mataki. Daga ita har Umma sun bi boka da Malam har sun gaji, sai kashe ku i suke amma babu biyan bu ata. Hajiya Aisha sai da ta raka ta wajen wasu manyan bokayen amma jiya i yau babu sauyi. Yanzu har aurin aure ya rage kwana uku. Part in Ya ABDUL wanda ba a arasa ba aka arasa sai kuma aya part in da yake a rufe dama an gama shi. Shirye-shirye ake ta yi don Umma har gida ta je ta yi wa Ya ABDUL wankin babba n bargo ta je ta yi wa Ammie da ko kallo ma bata ishi Ammien ba ta mayar da ita mahaukaciya. Duk ta zabgr ta yi ba i ta sa ba in kishi a zuciyar ta, HUSNA ce ka ai abokiyar shawarar ta duk wani shiri da take da shi a kan kishiyar take kwashe komai tana fa a mata. Tun da dai sun yj jimami sun yi iya ari ganin batun auren ya ruguje amma abin ya ci tura!. "Wallahi HUSNA na ji babu da i ga shi yanzu ko kula ni ba ya yi, a tawa wautar so na yi gobara ta one mu ni da shi urmus mu mutu kin ga ban barshi a duniyar ba ma bare ya auri wata ko kuma mu yi hatsari mu... "Haba HEEDAYA ki daina wannan tunanin, tun da dai har ta kusa shigowa ki mayar da hankali a kan zaman kishin da za ku yi kar ki bari ta zo ta wace miki fada" "Yo wacewa ta nawa kuma, ni yanzu gaba ma nake masa ba na masa magana, sannan ma ni duk magungunan matan da nake sha wa an da nake baki labarin yana santin su idan na yi amfani da su duk na tattara na ajiye kin san dai kaf sirrina ai na sanar da ke hatta magungunan mata da nake amfani da yadda nake amfani da wajen da nake siya da kuma yadda Ya ABDUL yake in ya kusance ni ai duk ina baki labari to mene ne ya yi saura wanda bana yi da zai mini kishiya" "Ki auki addara kawai kuma kin san dai wanda ya riga ka da kwana ya riga ka da tashi don haka ki maida komai ba k" Katse HUSNA ta yi don in ana maganar kishiyar ma unci take ji. A yau ne aka aura auren Ya ABDUL da amaryar sa, ranar da ta zama ba ar rana a wajen HEEDAYA babu wanda ta tara kuma babu abin da ta yi matsayin ta na uwar gida. HUSNA ce take kwantar mata da hankali tun ana gobe aurin aure. Kuma yau da ake aurin auren tun da safe HUSNA ta tafi wata ar uwar su HUSNA ta rasu suka tafi gidan makoki ba su sake waya ba. Da la'asar lis HEEDAYA tana zaune bayan RAUDA ta zo suna zaune kamar kurame abin duniya ya ha e musu goma da ashirin don a ganin HEEDAYA abin kunya ne su yi gayyata awaye za su rainata ita kuwa dama MEEMA bata zo ba. Sai Umma da take kiran ta a kai-a kai tana tambayar an kawo amaryar. Aunty Hafsa da ta zo da safe HEEDAYA ta mara rashin kunya wai ai da ita Ya ABDUL yake shawara amma saboda ta tsane ta bata bashi shawarar kar ya mata kishiya ba ita kuwa ta auki ar ta Ikram da Little RABEE suka koma gida. Zuwan Ihsan da Mubashshar tare da Na'eema ya yi daidai da shigowar motocin kawo amarya. Gu a ce take tashi ha e da bugun irjin HEEDAYA. An wuce da amarta part in ta da take a lullu "Aunty HEEDAYA wallahi duk an gayu ne baki gan su ba farare da su, amaryar tana lullu e da mayafi baki ga yadda aka mata unshi mai bala'in k... "Ya ishe ki Ihsan in zuzuta kyan kishiyata ne ya kawo ki ki auki afafun ki ki tafi" HEEDAYA ta fa a a harzu e don kuwa ta cika fam. Sai wajen takwas da wani abu RAUDA ta tafj su kuma su Ihsan sai da tara ma ta gota. Zaune take dirshan a asan akin tarasa mai yake mata da ofar aka turo jikin ta ya bata shi ne. A fusace ta ago jin amshin turaren sa ya gama ha akin. Farar shadda ce a jikin sa an mata aikin ba i sai farar hula mai ratsin ba i. Fuskar sa a washe kamar gonar auduga. "Uwar gida ran gida, uwar gida sarautar mata" Ya fa a cike da da in baki bata tamka masa ba don tana bu e bakin ta wata ila zagi ne zai fito. "Ni zan tafi sai da safe" Ya ce yana ajiye mata leda aya da yake ledoji biyu ne a hannun nasa. Yana fita ta yi cilli da ledar kaza da lemukan, takaici yana cika ta ganin ita a nata ranar amarcin ko tattabara bai kawo ba amma yau za ta ci albarkacin kishiya!?. Yadda ta ga safiya haka ta ga dare kuka kuwa har ta yi ta oshi sai dai tana ta udurtar sabon shiri don kuwa sai amaryar nan ta fita da afafun ta don Ya ABDUL nata ne ita ka Amarya da ango an yi kwanan farin ciki cike da farantawa juna, sun yi matu ar murnar kasancewa da juna. Misalin arfe tara suka sakko daga saman benen hannun su sar e da juna sanye suke da shadda ba a sun yi anko kasancewar su farare sai ta mugun kar i kikin su. Amarya kyakkyawa mai zubi da tsari na halitta ta sha aurin ankwali gashin kanta da ta tufke jelar har har gadon bayan ta. Ri e yake da ungunta bayan hannun nasa aya yana sar e cikin nasa ji suke ba ya su a fagen masoya. HEEDAYA wacce ba in kishi ya hana ta sakat ta baro part in ta ta nufi part in Ya ABDUL tun da yanzu ya koma nasa ya bar saman da yake a part in ta. Zuciya da take ta mata sa e sa e ce a kan wai har tare bai fito ba sun raina mata hankali. Babu zato suka ga an banko ofar wacce Ya ABDUL da ya dawo daga masallacin asuba bai kulle ba. Da yake sun bata baya da ta shigo sai ta yi mutuwar rsaye ganin su sar e da hannu sannan yana ma ale da ugunta sai wani amshin turarukan su mai sanyin amshi da ya cika falon. Wayar ta da take hannun ta wacce take ta faman kiran HUSNA tun jiya bata shiga, tana dab da shiga falon ta danna kiran HUSNA ashe dai kiran ya tafi kuma wayar tana ringin. Hakan ya yi daidai da fara aran wata waya da take kan kujera can wajen da suke tsaye. Ya ABDUL in ne ka ai ya juyo fuskar sa auke da murmushi. Ita kuma amarya bata juyo ba sai ta arasa gaban kujera ta auko wayar da take ara, lokacin kiran ya katse sannan da ta juyo ta taho bayan angon ya mata shamaki da ganin uwar gidan nata wacce bata ta a gani ido da ido a sai a yau take sa ran ganin ta. Tana dab da arasowa Ya ABDUL ya an kauce sai kuwa amarya da idanun ta suke kan fuskar HEEDAYA da ta yi mutuwar tsaye ri e da waya idanun ta suna kallon asa da alama dai ganin su ya daki zuciyar ta kishi ya motsa. Taku aya biyu amarya ta yi ta aga hannunta ta ora a kafa ar HEEDAYA da sauri HEEDAYA ta ago tana son ganin shin Ya ABDUL dafa ta in da ya yi mai zai ce mata har yana da bakin magana? Amma sai ta samu sa anin tunanin ta a kan fuskar da idanun ta ya sauka ta kusa samun ta in hankali tsabar ru un da ya ziyarci walwar ta. Sai dai tunanin ta ya i tsayuwa wuri aya saboda ta lura akwai bambanci da fuskar da take zato sai dai kama aya tamkar an tsaga kara wannan ta fi waccan haske kuma waccan tana da fa in fuska sannan wannan fuskar ta doguwa ce. "HEEDAYA!!!. Ki daina wahalar da kan ki wajen kirana a waya domin kuwa ga ni na dawo kusa da ke, kin ga wayar da kike kira a hannuna suna na HUSNA aminiyar ki ta online, ina so ki sani mu biyu iyayen mu suka haifa wato an biyu kuma, ni ce Hassana ake kirana da HUSNA ita kuma Husaina. Da ni kike chatting da ni kike waya da ni kike komai amma ba ni kika gani ba ranar da kika ziyarce ni gidan anwata Husaina kika je kuma da ita kuka ha u ba da ni ba" Bakin HEEDAYA tamkar ofar gari haka yake a bu e saboda mamakin da aka kashe ta da shi wanda tana tunanin tun da ta zo duniya ba a ta a bata mamaki irin na yau ba. Amarya taku aya biyu ta yi ta ce "Na kamu da son mijin ki ne tun lokacin da kike baje sirrin ki a faranti, kike kwashe komai kina fa a mini, kin san zuciya bata da ashi sai na ji ina ma ni ce Allah ya ba ni'imar nan kullum cikin fa a mini sirrin ki kike wanda ya dace da wanda bai kamata a ce kina fa a ba har son da nake yi wa mijin ki ya linku bila adadin sai dai kash auren wani a kaina ya hana ni aiwatar da komai. Kwatsam wata rana na kama HAMEED ya kawo mini mace gida lokacin na tafi Kano ganin gida da yake mu an asalin Kano ne to Husaina ta a Kano take aure ni kuma a Abuja. Ban sanar da shi dawowata ba da yake sai bayan na tafi ya zo Abujar sai a ranar na gane ashe manemin mata ne bu