← Book details Bonono Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 39

Sashe 29

Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yake sai dai ya kasa mata musu, wai aure shi ABDULHAKEEM ne zai yi aure kuma auren ma HEEDAY?. Wa annan tambayoyin ne suke masa kai kawo a birnin zuciyar sa, sai dai babu yadda zai yi ya yi musu. "To zan samu Abban " Ya fa a tamkar wani sakarai har lokacin kansa tamkar ana buga masa guduma. Hannu ta ora a ha ar sa ta ce "I luv you Ya ABDUL na da e ina aunar ka, ni na sani na fi kowa son ka tabbas idan ka aure ni zan saka ka manta da kowace a mace" Tamkar majigi haka yake kallon ta. ofar ta bu e ta fita shi kuma ya kifa kansa ya ma rasa wane kalar tunani zai yi. A guje ta shigo falon Ihsan da Mubashshar da suke zaune Mubashshar yana assignment ita kuma tana kallo sai gani suka yi ta shigo kamar an jefo ta, akin Umma ta shige ta danna mukulli Umma ta rungume tana ta tsallen murna, su duka dariya suke tamkar an musu albishir da kujerar hajji. "Kar ki kayar da ni" Umma ta fa a tana dariya. "Umma wallahi ya amince ko musu bai yi ba kuma ya yarda zai sanar da Abba" Ta fa a duk ta wani ru e ta zauce. "Haba yarinya boka fa aka ce kuma kar ki manta laya fa kika ha iya ai aiki dole ya ci" "Tabbas Umma ai wallahi ban ta a zaton zai amince cikin ruwan sanyi ba sai wani dafe kai yake" yale shi aikin ne ya ci shi ya sa kan yake sara masa ai ko nawa ne sai mun kashe, don sai kowa ya san ke kike auren sa musamman Hajiya Fati sai na nuna mata gaba da gabanta" Shiru-shiru suna jiran su ji magana ta kai kunne Abba amma babu amo ba labari sai dai sun yi if suna jiran tsammani. Tsawon sati uku shiru. A angaren Ya ABDUL kuwa sai ya yi kamar zai je ya sanar da Abba kawai sai tunanin Aunty RABEEYA ya hana shi sakat sai yake ganin bai mata adalci ba daga mutuwar ta ya yi aure shi ba ya ma son ya auri HEEDAYA sai dai babu yadda zai yi don zuciyar sa azalzalar sa take yi. A wani yammacin Litinin ne bayan ya dawo daga wajen aiki ya yi wanka da yake yanzu gidan su yake ya i zaman gidan sa saboda babu Aunty RABEEYA a ciki. Da sallama ya shiga falon Abba. Bayan ya amsa masa ya zauna a asan capet ya gaishe da shi. "ABDULHAKEEM ka i ka kwantar da hankalin ka ko? Duk ka yi ba i ka rame kar ka manta fa Allahn da ya bamu RABEEYA ya fi mu son ta kuma shi ya kar i abarsa ya kamata ka sawa ranka dangana kake mata addu'a" Shiru ya yi yana mai sunkuyar da kai sai yake ji tamkar wanda zai fa i wani sa o don a ganin sa tamkar abin kunya ne kuma cin amana sai dai ya kasa dakatar da kansa shi ma bai san dalili ba. "Ina mata addu'a Abba" "To Allah ya ara maka ha uri ha a da wuya samun irinka a wannan zamanin mai son matar sa haka sa anin wasu daga matan sun mutu shikennan sun manta da su" "Abba dama magana na zo mu yi" "Ina sauraron ka" "Am, dama, dama" "Dama mai?" "Ina son na auri HEEDAYA" Idanu Abba ya ance yana mamakin furucin nasa har sai da ya ce ya maimaita don shi Abba a iya sanin sa bai ta a zaton a kwana kusa ABDULHAKEEM zai nemi yin wani aure, tunanin sa ma sai sun za a masa matar za a masa auren dole don shi da yake fa in ya gama aure bare kuma wai HEEDAYA zai aura. Mamakin sa ya oye ya nuna masa jin da in sa amma a zuciyar sa tabbas ya yi mamakin hakan. "Ai ta kwana gidan sau i HEEDAYA ai anwarka ce sai dai kuma ka same ta ka ji daga bakin ta ni ma za mu yi magana da Daddyn ka da kuma Hajja" "Ai mun yi magana da ita ta amince" "Ikon Allah to, ba damuwa za mu zauna da Daddyn ka sai mu ji yadda za mu ullowa lamarin" Daga haka ya yi wa Abba godiya ya fito sai yake jin tamkar ya sauke wani nauyi don tun da HEEDAYA ta masa furucin nan bai samu nutsuwa ba sai da ya furzarwa Abba kalaman nan. Abba kuwa da mamaki ya cika shi sai dai hakan ma abin so ne ko ba komai Ya ABDUL in zai samu nutsuwa. Sosai aka sha fa i tashi da maganar auren aka iyo wa Ya ABDUL caaa musamman Ammie don a ganin ta yaushe ma matar sa ta mutu har zai nemi ara aure auren ma da HEEDAYA. Sai dai ta san ita bata isa ta hana ba domin sai da Daddyn ABDUL in ya garga e ta don ya san basa ga miciji da Umma. Hatta Momma sai da ta shiga ta fita ta hanyar kissa da kisisina a kan ganin ta hana auren amma abin ya ci tura. Saboda Umma da Hajiya Aisha su tashi hai an a kan lamarin auren kullum suna hanyar zuwa wajen bokan su don ganin an yi wa bakin kowa dabaibayi musamman wanda zai yi yun urin hana auren. Hajja kuwa da i ta ji na wannan ha in don a ganin ta gida bai oshi ba ba a kai daji ba. Aunty Hafsa kuwa ta san tabbas abin nan ba Ya ABDUL yana hayyacin sa ba ne tun da dama ta san udurin su Umma tun ba yau ba bare kuma yanzu da suka samu sarari ita dama an daina saka ta a sabgar an kuma daina shawara da ita tun da sun gane bata tare da su. Yau ya kama wata uku cif da mutuwar Aunty RABEEYA wanda ya yi daidai da saura kwana sati aya aurin auren HEEDAYA da Ya ABDUL. Zaune an gidan suke su duka a falon Abba da ya kira taro, sai dai bai ce komai ba, bayan mintina ka an Ya ABDUL da Abba ya kira ya shigo da sallama gaishe da Abba ya yi sannan ya shiga gaishe da Momma wacce ta amsa babu yabo babu fallasa don ita yanzu mugun haushin ABDULHAKEEM in take ji, na auren da zai yi wai ya rasa ma wa zai aura sai HEEDAYA , sosai take jin takaicin hakan don har maganganu Umma take yada mata, shi ya sa yanzu ko ganin Little RABEEYA ya zo sai ta ga dama take barin sa ya ganta wataran ma sai ta ce maaa bacci take ta hana shi ganin ta haka zai gaji ya tafi. Ko da ya gaishe da Umma faram-faram ta amsa da i duk ya cika mata zuciya ganin Momma tana ta muzurai. Yaran ne suka shiga gaishe da shi ya amsa ya samu waje ya zauna. Gyaran murya Abba ya yi ya fara magana. "Abin da ya sa na tara ku a nan ba komai ba ne sai magana a kan RABEEYA arama, wato ABDULHAKEEM ya same ni a kan cewa idan ya yi aure za ta koma hannun sa da zama" irajen mutum uku ne suka buga da sautin diririmdimmmmm. irjin Momma wacce ta ci alwashin azabtar da Ya ABDUL ta dalilin yarinyar don yanzu ta saka a ranta sai ta ringa zuwar masa da bu atun ku i don take tati e shi sannan take azabtar da shi ta hanyar hana shi ganin yarinyar don ta aga mas hankali ta hana shi kwanciyar hankali don kishi take taya arta duk da bata raye. Sai kuma irjin Umma uwar amarya jin wai za a auki yarinya a kai gidan arta kenan waye zai reni yarinyar da ko zama bata yi? HEEDAYA za a kaiwa wahalar ko wa?. Sai kuma irjin mai gayya mai aiki HEEDAYA da ta ji tamkar ana dakan sakwara a irjin nata jin wai za a mayar da ita ar raino ita da ta ci burin zuwa ta mi afa ta huta amma ake wani batu. "Haba Alhaji yarinyar da bata gama warewa ba, a barta mana a nan in ma zuwa gidan uban nata ne sai take zuwa bayan ta girma take zuwa da yawo" Momma ta fa "Kin san dai in na yi magana babu mai warware mini, ko arki ce? To mai ar ne ya bu aci haka kuma babu sauyi duk ranar da ya bu aci kar arsa bayan ya yi auren zai iya zuwa ya auke ta ni dai na sanar da ku na fita ha i shi ya sa na kirawo shi don ku ji daga bakin sa" Abba ya fa a cikin fa "ABDULHAKEEM idan ka yi aure duk ranar da ka ji ta raya maka ka zo ka auki arka ka tafi da ita" Abba ya ce yana masa umarnin ya tashi ya tafi. Fita ya yi ya tafi. "Bayan shekara biyar amma?" Umma ma da ta kasa ha uri ta tambaya. "In ma bayan shekara aya ne ruwan sa ne wannan, ni dai na s anar ne don ku kwana da sanin hakan watarana ku tashi na sallami kowa" Da wannan aka watse ran kowa yana suya. "Umma kin ji wani sabon tashin hankalin kuma ko? Wai mai ya sa komai idan za a yi sai an samu gargada ne ?" HEEDAYA ta tambaya ranta a ace don bata ta a kawowa haka za ta faru ba. "Kayya HEEDAYA ni ma abin ya aure mini kai amma ai tun da bayan shekaru ne ba ma nuna zalamar mu a fili ba kin ga sannan ma yarinyar ra zama ta dara moruwa ba sai ta zama ar aike da aikin ki ba" Umma ta ce tana dafa ta. Shiru ta yi sai kuma ta murmusa amma dai duk da haka ba hakan aka so ba anin miji ya fi miji kyau!. Duk da haka sai da su Umma suka ziyarci boka amma ya tabbatar musu da cewa babu ruwan su game da arsa don son ar a cikin jini da tsokarsa yake ba za a iya raba shi da son
Chapter 29 · 0% Book details