Sashe 15
Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune take a tangamemen falon ta sanye take cikin riga da wando wanda suka kama jikin ta, sun yi matu ar mata kyau! Duk wata sura ta a mace ta bayyana kasancewar ta mai cikar halitta da duk wani abu da namiji zai bu ata ta mallake shi. Sauke idanun ta ta yi daga kallon TV take arewa kanta kallo tana jinjina irin kyan da ta yi don kawai ta birge mijin ta wanda a alla yau wata biyu kenan bata saka shi a idanun ta ba, kullum yana yawon garuruwa wanda a koyaushe yake fa a mata cewa bussines in sa ne yake sanya shi tafiye-tafiye. Waya ta aga ta duba arfe biyar da an mintina na yamma amma bai samu arasowa ba daga Lagos in da ya ce zai taho. Ta yi nisa a cikin tunanin makomar rayuwar auren ta sai ta ji aran bu e get in gidan kafin walwar ta ta gama sa unta mata tunanin dalilin bu e get in, aran dirin motar ya tabbatar mata da cewa mijin ta HAMEED ne ya iso. Duk da akwai damuwa a zuciyar ta amma sai ta ji wani sanyi a ranta ko ba komai dai ta san za take ganin mutum a kusa da ita tun da ita bata ta a haihuwa ba sai an aikin gidan kawai da suke kai kawo. Da sauri ta nufi window ta le o ai kuwa ta hangi direba ya bu e masa ofa bayan ya fito ya rufe ofar. Ganin ya nufo part in da an hanzari ta shiga sakkowa daga saman domin tar ar sa tana fatan kuma kada ya mayar mata da murnar ta cikin ta. A tsakiyar falon ta cim masa, tun kan ta arasa sakkowa take sakin murmushi sai dai ganin ya cunkushe fuska, duk da ta ji babu da i na ganin yanayin sa amma haka ta arasa gaban sa tana ari rungume shi amma ya ja da baya tamkar ya ga wani abun tsoro, yana kuma aga mata hannu saroro ta tsaya tana kallon sa dama ta san wannan rubutaccen abu ne yana kallon ta tamkar ya ga kashi a daidai nan direba ya shigo masa da jakar kayan sa amma ganin direban bai sa ya yi sassauci ga abin da yake son fa a ba. "Sau nawa zan ce miki bana son wannan al'adar turawan baki san irin wa annan abi'un lalata tarbiyar yara yake yi ba, yanzu idan kika saba da wannan abi'un ba za ki fasa yi ba ko da mun haifi yara kin ga kenan yaran mu za su taso suna koya!." Ya arasa fa a a harzu e direban jakar ya ajiye da girmamawa ya juya ya fita. Kallon sa na tsaya yi tamkar na ga sabuwar halitta ina rayawa a zuciyata. 'Shin sai yaushe ne zan fita daga wannan ba angin? Shin sai yaushe ne HAMEED zai faranta raina a matsayina na matar sa mai ya sa ya gwammace kullum yake nuna mini kansa a tukunya yake bai waye ba amma yanayin sa da yadda yake gudanar da al'amuran sa ya nuna shi wayyayyan mutum ne, amma ba ya son ko ka an ya nuna hakan a kaina ya fi so kullum ya yi fatali da duk wani abu da ya shafi auratayyar mu. "Haba HAMEED yau tsawon wata biyu ban sanyaka a idona ba, shin laifi ne don na tunkare ka, ko kewar ka da na yi a matsayina na matarka ka bari in ji umin jikin ka" Ta furta tamkar ta yi kuka saboda takaici da kuma yanayin yadda ya nuna. "HUSNA!. Sau nawa kike so in fa a miki ni bana son irin wannan rayuwar turawan ko so kike kullum nake biya miki kamar karatu sannan ne za ki haddace wane ne ni? Mai ya sa ku mata a koyaushe bakwa tsayawa ku yi tunanin halayyar abokin rayuwar ku, mai ya sa bakwa amfani da kalmar nan da bahaushe yake fa in in an san halin mutum sai a ci maganin zama da shi?" Ya kai arshen maganar yana mata wani kallon rainin wayo. "Su turawan wasu mutane ne da ban? Su turawan sun fi mu son farantawa junan su ne da suke halayyar ai a ganina don ma'aurata sun yi wani abu a tsakanin su hakan ba yana nufin laifi ba ne tun da komai aka gabatar matsawar bai sa awa addini ba to halal ne... "Idan kuma ya sa awa al'ada fa?" Ya katse mata hanzari da jefa mata wata tambaya da take ganin da yin tambayar da rashin ta duk uwar uban su aya. "Baki da amsar tambaya ta, abubuwan da kike sun sa awa al'adar malam bahaushe kuma wannan ata tarbiyar yara ne iyaye suke rungume -rungume ko sunbatar junan su matsawar ba a lokacin kusantar junan su ba wato a ke antaccen wuri" "HAMEED, da addini da al'ada wanne ne a gaba?" Bata jira cewar sa ba ta ora. "A cikin gidan nan daga ni sai kai sai an aiki, shin mun haihu ne da za ka fara maganar ata tarbiyar yara... "Ya ishe ki HUSNA, mai ya sa kike uzzurawa rayuwata? Daga shigowata gida ko hutawa ban yi ba kin tsare ni da yawan magana to ki dakata!. Ni HAMEED ba ni da lokacin atawa" Yana kai wa nan ya wuce ya bar ta baki sake, sama ya haura ai kuwa bata daddara ba ta take masa baya. Sai dai kamar yadda ya saba hakan ya mata yau ma yana shigewa akin sa ya banko ofar tana zuwa ta tura ofar ta ji ya saka mukulli ya kulle. Jingina ta yi da ofar tana jin yadda zuciyar ta take suya tana jin yadda ruwa ya taru a kwarmin idanun ta, ta rasa sai yaushe ne za ta yi farin ciki kamar yadda kowace mace take yi a gidan mijin ta sai yaushe ne HAMEED zai sauke nauyin ha in ta matsayin ta na matar sa ita duk wani jin da i da mace take samu na dukiya da sauran abubuwan more rayuwa a gidan aure ta mallake su, babu abin da HAMEED ya rage ta da shi idan ta ce komai tana nufin komai da komai, sai dai a cire abu aya wanda shi ne ginshi in aure kuma shi ne kashi saba'in cikin ari na aure wato HA I duk abin da yake na ha in auratayya ne to ita bata san shi ba duk abin da yake kulawa ce daga namiji ga matar sa sai dai ta ji a labari ko wajen awaye ko ta karanta littafin hausa kai ita har bata son kallon film saboda duk inda take ganin ana soyayya ko ba mace kulawa wanda ita ta rasa sai ta ji hankalin ta ya tashi sai ta ji da tana da ikon sauya HAMEED da ta sauya shi amma kash!. Ta da e a jingine a ofar tana jin sa har ya shiga bayi ya da e kafin ya fito hakan ya mata alama da wanka ya yi, bayan wasu mintuna ta fara jiyo dirin maganar sa da alama waya yake. Kunne ta ara kasawa a jikin ofar. "Haba Baby ni ma ai ban ce na gaji da ke ba, ke kin sani bakya ta a ginsa ta a rayuwa iya magana da taushin kalaman ki ka ai sun isa ki janye alakar duk wani a namiji da yake jin kansa domin ke ta daban ce" Wa annan kalaman ne ta jiyo su a cikin dodon kunnen ta, wanda ta ji shigar su tamkar tafashashshen ruwan zafi a hankali cikin sanyin jiki ta bar jikin ofar dakyar take aga afafun ta har ta sakko asa a aya daga cikin kujerun ta yi wa kanta masauki, tare da saka hannuwan ta biyu ta rufe fuskar ta hawaye masu umi suka ci gaba da wanzuwa a dakalin kyakkyawar fuskar tata. 'Sai yaushe ne? Mai na rasa a halitta? Wane irin gyaran jiki ne bana yi? Tsafta kwalliya tatttali tsara kalamai duk don in ja hankalin mijina, duk wani abu na gyara da mace za ta bu ata don gyaran auratayyar ta ina yin sa amma sai dai ban yi dace da mijin warai ba. Shin dama duk matar da mijin ta bai damu da ita ba bata da wata dama a wajen mijin ta? Duk namijin da hankalin sa yake kan matan waje matar sa ta gida bata dame sa ba? Duk ha uwa da ladabi da biyayyar ta? Mai ya sa matan irin mazan nan suke tamkar duwatsu ko bishiyoyi a cikin gidajen su? Mai ya sa suke rayuwa tamkar ba ma'aurata ba kuma duk gyaran da za su yi basa birge mazajen su, sai ki ga macen marar aji marar galihu wacce ma kina mata kallo aya za ki mata kallon raini wacce bata ma kai su yi ko da gaisuwar fatar baki da namijin ba saboda rashin kamun kai da aji amma sai ta auke masa hankali, shin kowace macen ce take fama da irin ciwon ko kuwa ita ka ai ce?' Ta shiga rattabowa kanta wa annan tambayoyin duk da har yanzu zargin sa take bata tabbatar da cewa yana neman matan ba amma dai abubuwa da dama suna mata kama da hakan. Ai shi ba dutse bane kuma ba icce ba ne da za a ce matarsa bata dame shi ba, to don mai aka y auren, tun da yana da lafiya amma kullum maganar sa aya ce shi yana da raunin sha'awar mace ne, wanda tana ganin amsar nan tashi rainin wayo da rainin hankali ne kawai. Duk da ta san mafi yawan maza kashi casa'in cikin ari basa zama ba tare da suna da an mata ko zawarawa ba, tun da kowane namiji arya yake ya ce bashi da budurwa ko bazawara sai dai in munafurtar matar yake, kai ko da a ce akwai su a cikin mazan to basu da yawa, sai dai ita irin yadda yake banzantar da ita ya yi yawa irin yadda yake waya da sauran su da wasu mazan ya sha bamban kuma irin yawan tafiye-tafiye da yake ya yi yawa kai ko da a ce yana tafiyar ai kamata ya yi yake yi da ita in ba zai yi ba a alla idan ya