Sashe 35
Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kin manta a daren ki na farko ma ko inda kike bai kalla ba? In kin manta in tuna miki hatta malamai ni na kai ki kika san wajen su suje miki aiki amma ya dace ki watsa mini asa a ido, saboda wata ita fa online kuka ha u ni kuwa tun bamu san kanmu ba muje tare... "Dakata! MEEMA baki da hurumin da za ki fa a mini mai zan yi a rayuwtaa, kuma HUSNA ta fiki sau miliyan a wajena an fa a miki shi zumuncin online in ba ya fin na zahiri? Sannan da kike wani yanyanyayan in kin zama silar zamana wani abu a gidan miji mene ne yanzu kuma ina ne ban sani ba ni kawai ji na yi na daina ra'ayin awancen da ke " Tana gama fa ar hakan ta daina bu e sa on na MEEMA ma. Wannan abin ya yi wa MEEMA ciwo sai dai duba da butulci irin na an adam sai ta janye jikin ta daga wajen HEEDAYA ita kuwa HEEDAYA ko a kwalar rigar ta, yanzu wasu awayen ma ta sake a wasu groups in amma dai babu kamar HUSNA. *BAYAN SHEKARA AYA* Yanzu Little RABEE tana tafiya ga kuma tana cin abinci sanna yarinyar sai kyawun ta ha e da kamamnin ta da mahaifiyar ta suka ara bayyana in da yarinta ba sai ka ce Aunty RABEEYA ce idan ka ganta. Sai dai wani abu da ya fara ci wa HEEDAYA tuwo a warya yadda Ya ABDUL ya damu da yarinyar sosai yanzu ko gidan ya shigo sai ya ce mai renon ta ta kawo masa ita haka zai zauna ya yi ta mata wasa ko ma ya auke ta su fita. Sawun ta wajen manyan malaman ta da take ji da su uku a kan a yi farra u tsakanin Ya ABDUL da Little RABEE amma abin ya ci tura!. Kowa sai ya ce ba zai iyu a farra a su ba don a nata rashin imanin so take a saka masa tsanar yarinyar a ransa yake mantawa ma da ita amma sai take ganin tamkar wutar soyayyar ake rurawa a tsakanin su ba ta iyayya ba. Ta kashe ku i don cim ma wannan burin amma abin ya i ci ya i cinyewa hakan ya sa ita ta auki tsana da kishin yarinyar ta saka a ranta tamkar dai ta manta da karamci da halaccin mahaifiyar ta lokacin tana raye ita kawai sai ita da anta a da babu rana bare watan haihuwar su don babu haihuwa ma a ranta yanzu. Wani abu da ya fara kutso kai cikin lamarin zamanta da Ya ABDUL shi ne aurace mata, ya fi son kasancewa shi ka ai bayan ra san koyaushe muradin sa bai wuce ya gan shi tare da ita ba. Amma yanzu sai ya haura sama ya kulle ofa ta rasa mai yake idan ta tambaye shi sai ya ce hanyaniya ce ba ya so. Ta fa awa HUSNA wannan orafin amma sun kasa samo bakin zaren. Don haka sai ta auki aniyar bin wafin sa ko za ta gano dalilin sa don bata yarda da hujjar da ya bata ba ta cewa hayaniya ce ba ya so. Da dare misalin arfe sha aya na dare ta gaji da zama ita ka ai a akin ta tana ta juyi so take bacci ya auke ta amma ta kasa sai tunane-tunane take tana sa a da warwara. afafun ta ta sako daga kan gadon tana hamma, sanye take da riga da wando na bacci kanta da hula mai net. Saman ta haura cikin san a ta je ofar akin nasa ta tsaya. Kunnen ta ta kara sai ta ji dirin magana. Mamaki ya kamata ta rasa da wa yake magana . Kunne ta kasa a nan ta gane waya yake. "Ina son ki mana, ai ko duniya zan iya aga babbar murya na fa awa ina aunar ki" Wani irin bugu irjin HEEDAYA ya yi lokaci guda zufa ta ji ata jikinnta ya auki karkarwa ji da ganin ta ya auke na sakanni. Ta kasa gaskata kunnuwan ta abin da suka jiye mata. 'Mace?' Ta jefawa kanta tambayar zuciyar ta tamkar ta huda irjin ta ta fito. "Yaushe na yi wannan sakacin Ya ABDUL yake wayar soyayya da mace na shiga uku ni kam" Ta fa a a fili tana kama handle ofar ta mur a amma sai ta ji a rufe. Ya ABDUL da yake waya da masoyiyar sa jin an ta ofa alamar za a shigo sai ya ce mata yana zuwa zai kira. Tasowa ya yi ya bu ofar maimakon ya girmama ta ko dai ya matsa ta shiga akin sai ya kasa ya tsare. Mamaki al'ajabi suka cika mata zuciya. "Kina bu atar wani abu ne?" Ya tambaya a dake. Kallon sa take da idanun ta da suka kawo ruwa ta danne abin da take ji ta ce "Na ji shiru ne kuma na kasa bacci shi ne na ce bari na taho nan" "Ina bu atar kasancewa ni ka ai ba na bu atar takura" Yana gama fa ar hakan ya rufe ofar. Idanun ta kamar za su fa o a take ta ji komai ya sare mata lokaci guda ta tuna cewa Umma shekaran jiya ta ce mata ta ga ya shiga gidan su bayan ta san sai ta masa umarni yake zuwa gidan nasu to mai hakan ke nufi. Ba wannan ne damuwar ta, soyayya yake da wata a waya? Da bibiyu take taka matakalar asa ta dawo ta nufi akin ta tana zuwa ta auki wayar ta hannun ta har rawa yake ta kira HUSNA don ta san ita ka ai za ta tattauna da matsalolin ta. Sau uku tana kira amma babu amsa. 'Haba HUSNA ki auka mana ki ji danuwar da ta kutso kai cikin gidana' Ta fa a a zuciyar ta tana jin wani tashin hankalin yana baibaye zuciyar ta. A karo na hu u HUSNA ta auka muryar ta cike da bacci ta ce "HEEDAYA lafiya" Kuka HEEDAYA ta fashe da shi don ta kaaa furta komai. "Haba aminiyata ya da kuka kuma ko mutuwa aka miki?" "Yo ba gwara a mini mutuwa ba da bala'in da yake tunkaro ni" "Subhanallahi mene ne damuwar" "HUSNA Ya ABDUL ne na kama shi yana waya da mace, kin san ai na fala miki sauyin da ya fata shigo minj da shi cikin rayuwar auren mu to wallahi azu cikin kunnuwana na ji yana furta kalmar so ga wata mace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un wannan wace irin ba ar rana ce?" Ta fa a hankali tashe tana tashi zaune daga kwanciyar da take. "Shi ne da ya bu ofar ma wai ni HEEDAYA yake tambaya ina da bu atar wani abu, sannan na taho ke ma na zo ina kiran ki kika auka" "Ayya!. Ki yi ha uri bacci nake kin san gwauruwa da bata da miji a kusa da na yi isha'i sai na kwanta bacci baki ga yau ko chatting ba mu yi sosai ba tun wuri na sauk... "Bar wannan labarin anzon kuregen mene ne mafita wallahi kaina ya kulle na kasa kowane tunani ban ta a tunanin ko hasashen akwai irin wannan ranar za ta riske ni ba" "Ki bar wannan tada hankalin aryar sa ya ce zai aure ta ai" "Yo ko ba auren ta zai yi ba ni yin kalmar sa ta so ga wata mace ai bala'i ne me lasisi a wajena vana aunar komai ya ha a shi da kowace mace ki hatta arsa ta cikin sa Little in nan na tsane ta kishin ta nake wallahi dama arin ta aka yi ko kuma a take da aka haife ta ta bi uwar ta... "Ya isa haka HEEDAYA ar zumun naki, yarinyar da mahaifiyar ta ta so ki kamar mai to ko ba don mahaifiyar ta ba albarkacin uban ta bai kama ta kike fa ar wannan ba ai ba a kishi da "Ke kike ganin haka ke ni kishina hatta uwar sa bai tsallake ba sai da na musu farra u ko yanzu ma ina da niyyar ara farra a su don na ji ishin- ishin yana zuwa gaishe ta" Kai HUSNA ta gyara tana mamakin irin ba in kishin HEEDAYA bayan maza kuma ba tabbas gare su a kan mace ba tun da har ta ji yana furucin so ga wata to tabbas sai dai addu'a dama da wuya namiji ya aunaci mace ita ka Sosai HEEDAYA take kukan ba in ciki a cewar ta yau ba za ta iya bacci ba ita dai HUSNA ta bata baki daga arshe suka yi sallama ranta yana suya idan ta tuna furucin da ta ji Ya ABDUL ya yi wa wata sai ta ji tamkar ta yi aramar hauka. Washe gari da safe da ta tashi ko kicin bata kalla ba dama duk saboda ba in kishin ta ko masu taya ta aiki babu ta gwammace ta yi girkin ta da sauran ayyuka sai dai sauran na harabar gidan da ba fulawoyi ruwa maza su yi, sai sai renon Little RABEE ita kuwa ta haife ta ma ko yin jika da ita. Ko da ya fito ko kallon arzi i bai samu ba, shi ma kuma sai ya aure fuska ko sallama bai mata ba tana jin lokacin da ya tafi ganin Little RABBE. Tana jin fitar motar sa ta fito ta saka direba ya auke ta sai suka keta hazon shiga daji suna karo da ciyayi. Wurin bokan da MEEMA ta ha a ta da shi ta je bayan ta kora masa jawabin abin da yake tafe da ita sai ya ce ta kwantar da hankalin ta ko da ya yi soyayya ba zai ta a auren macen ba ai sun gama kama mata shi a hannu babu shi babu sha'awar wata a mace sai ita!. Kalaman sun mata da i inda ya bata wani garin magani ya ce ta saka masa a miya. Ku i ta biya shi ta shiga mota direban ya akko ta don har ya saba kawo ta wajen. Daga nan gidan su ta wuce ta je ta korawa Umma jawabi. Zare idanu Umma ta yi tana ta ambaton bai isa ya