Sashe 28
Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sakin jiki. "Gidan mu ne nan ba siyar da ke zan yi ba" Ya ce yana kallon ta auke da kurmushi. Bata ce komai ba fuskar ta ta yi fayau da alama har lokacin damuwa tana nu usar zuciyar ta. Gaba ya yi ta bi bayan sa. "Kin saka ni a gaba sai ka ce wani an ki" Ya ce lokacin da ya ja ya tsaya yana kallon ta tana tahowa da sanyin jiki da yake akwai tazara daga get zuwa cikin gidan, ga shi kuma ya an bar ta a baya sosai. "Ai da yake ni ban san gidan ba" Ta fa a cikin sanyin muryar ta. "Tun da baki sani ba sai ki ago afa don in na ace miki va samun hanya za ki yi ba" Da sallama suka shiga gidan wata mata ta amsa musu tana musu marhabin. "Likita bokan turai" Ta ce cikin zolaya tana dariya. "Wannan dai bokan auye ne, tun da a can yake aiki" Ya fa a shi ma yana dariya. "Duk aya dai" Dariya ya yi suka shige falon bayan MARYAMA ta gaishe da ita. Zaune take a falon farantin kankana da lemon fata a gabanta tana sha, bayan ta amsa musu sallamar ta ago ta kalle su. "Zauna MARYAMA ya ce bayan ya samu waje ya zauna kusa da Kaka, tare da aukan kankana ya kai bakin sa. "Sai zuwa ba sanarwa" Kaka ta ce tana kallon sa. "Ni da gidan mu?" Ya ce yana aukan lemon ya sha. "Barka da rana, ina yini" MARYAMA da ta samu wuri a kan carpet ta zauna ta fa a cikin girmamawa. "Lafiya alau an mata" Kaka ta ce tana bin ta da kallon rashin sani. "Sunan ta MARYAMA mun ha u a auyen da nake aiki jiya da dare marainiya ce bata da kowa ma a ta aice" Ya kai arshen maganar yana kwashe komai da MARYAMA ta fa a masa ya fa a wa Kakar yana fatan Allah ya sa ta amince da maganar don ya santa wani likacin butsuwa ce. Kallon ta Kaka take yi tana nazartar ta, MARYAMA kuma ta sunkuyar da kai idanun ta suna cikowa da walla, don babu abin da yake saurin karyar mata da zuciya irin ta ji ana batun bata da kowa musamman da ya ce shekaran jiya mari inta ya mutu. "Daga wane auyan kike?" Kaka ta fa a tana kallon ta. auyen KANYA" Bayan ta bata amsae ta shiga mata wasu tambayoyin da har sai da ta gamsu da gaskiyar ta, sannan ta ce ta amince ta zauna da su. aki aka saka Mero ta raka ta, wacce aiki take yi kuma dai a gidan take zaune ita da Kakar sai kuma sauran ma'aika maza. Bayan sun ke e da Ya HAFEEZ in take ta masa fa an kar ya ara mata kwashe-,kwashe sannan ma ta ce sai ta saka an binciko mata can auyen KANYA a oye a kan abin da MARYAMAR ta fa a duk da ta fahimci iya gaskiyar ta ne ta fa Bayan kwana biyu, zaune take a gidan Kaka hankali kwance don babu kyara babu tsangwama ga shi sai suke ta jan ta a jiki ko kuma jan ta da zance, hakan yana rage mata unci sai yanzu take jin tana rayuwa ta anci tamkar wata mai gata ko mai iyaye a raye ba irin rayuwar gidan Baffa ba da take yin ta cikin tsangwama da rashin galihu sai ta angaren Baffa ne ko Goggo kafin ta mutu take samun salama. Ya HAFEEZ ya koma auye tun washe gari tana jin sa in suna waya da Kaka yana tambayar ta ita. Yanzu Kaka ta ce ma idan ya dawo za a saka ta a makaranta tun da ta kusa kammalawa tana ss 2 ne. *BAYAN WATA GUDA* Kaka zaune take tana kallo sai MARYAMA da take moppin a falon kasancewar bata son zama sai take aiki ko da an hana ta an ce da masu yi. Kaka ce ta yi tsai tana arewa MARYAMA kallo mamaki da fargaba cike a zuciyar ta ganin fuskar MARYAMA ta sauya duk ta ciko hatta jikin ta duk ya sauya tamkar dai mai ciki haka Kaka take mata kallo don dama wani lokacin tana yi mata kallon hakan sai dai yau abin ya ru a ta. Bata san ya aka yi ba urawa marar MARYAMA ido da ta yi sai kuwa ta yi kici is da ganin tudu a marar MARYAMA, yawun bakin ta ne ya afe lokaci guda zufa ta wanke mata fuska ta shiga gangarowa zuwa wuyan ta. Dakyar ta samu kalmomin da ta ha a haruffan wajen kiran MARYAMA. MARYAMA jin Kaka ta kira ta, sai ta ajiye mofa ta taho wajen Kaka, sai dai kallon da ta ga Kaka tana jifanta da shi ya saka mata tsoro da kuma ru ani. Saboda gaba aya ma ita shagala take da cewa akwai wani ciki a jikin ta, saboda yanzu bata da damuwa sosai tun da dama ita gorin da ake mata ne yake damunta na cewa ita shagiya ce tsintacciya yanzu kuwa babu mai mata gori sai kuma damuwar mutuwar Baffa duk da tana masa addu'a kuma hakan yana sanya salama a ruhin ta. "Tashi tsaye" Kaka ta fa a tana kallon ta don tana zuwa gaban Kaka ta dur usa alamar girmamawa, ita Kaka ta rasa ma mai yake mata da i fatan ta dai zaton ta kar ya zama gaskiya. Ta san ta aika an binciko mata cewa akwai wata MARYAMA da take ar tsintuwa kuma mari in ta ya mutu, mai binciken ya dawo mata da amsar cewa tabbas akwai ta, amma dai matar mari in ta kore ta daga gidan don haka yarinyar bata garin ma. Wannan ne ya sa ta yarda da gaskiyar MARYAMA amma bayan wannan babu abin da aka binciko mata dangane da ita ashe dai akwai sauran rina a kaba. MARYAMA tsaye ta tashi ai kuwa Kaka da ita ma ta mi e tsaye ganin abin ba na yi ba ne ta saka hannu ta gwale idon MARYAMA gabanta ne ya buga da mugun arfi. Da sauri ta saka hannu ta ama rigar MARYAMA ai kuwa ta ga marar ta ta yi tudu kana gani kuma ka san ba timbi bane tun da a mara ne ba a ciki ba. MARYAMA gabanta ne ta doka da arfi jikin ta ya shiga karkarwa da za a tsaga jikin ta ba za a samu jini ba ko ka an, saboda ru ewa da kuma fargaba. "Ciki ne da ke ko?" Kaka ta tambaya muryar ta tana karkarwa. MARYAMA wacce hawaye ya fara ambaliya a dakalin fuskar ta, cikin sanyin jiki ta shiga gya a kai tamkar adangaruwa don ta san aikin gama ya gama tun da babu wani abu da za ta oye, tunanin ta aya ma da bata sanar da Ya HAFEEZ ba tun a ranar da ya bu aci jin labarin ta, yanzu za su ga ta munafurce su. Kaka ganin MARYAMA tana kuka kuma ta gya a kai alamar eh ce amsar tambayar da ta mata, sai hankalin ta ya ara tashi tana ta ambaton innalillahi wa inna ilaihir raji'un a zuciyar ta don a ganin ta tun da har MARYAMA ta san da cikin to tabbas shi ma wanda ya kawo ta wato HAFEEZ ya san da hakan nan take zuciyar ta ta shiga sa a da warwara a kan cewa HAFEEZ ya yi wa yarinyar ciki ne shi ne ya kawo ta gidan duk da ta yarda da shi a kan tarbiya da tsoron Allahn sa amma dai ta san shai an shi ne mugun mai yin jagoranci wajen aikata alfasha. Ko ta kan MARYAMA bata bi ba, don yanzu gaba aya ta fi ganin laifin HAFEEZ da ya akko yarinya auke da cikin shege ya kawo mata gida tun da dai a kaf tarihin yarinya babu inda aka ce an mata aure. Waya ta auka ta doka masa kira, yana kishingi e yana an danna laptop kiran Kaka ya shigo zaune ta tashi yana sakin murmushi don ko ba komai idan sun yi waya zai tambayai lafiyar MARYAMAR shi wacce a yanzu yake jin ko ai yake da tunanin ta yake ya san kuwa babu makawa da son ta zuciyar sa ta kamu. "Assalamu alaikum Kakata ta kain... "HAFEEZU ni za ka rainawa wayo ka manta ni na haifi ubanka? Tunanin ka na yi tsufan da za ka yaudare ni, ka akko yarinyar da ka irkawa ciki kuka raina mini hankali ka kawo mini ita gida.... Kalaman da ta masa suka daki walwar sa, gabansa ya buga da arfi mamaki al'ajabi suka taru suka cushe masa zuciya, shi kansa bai san lokacin da ya tashi tsaye ba daga zaunen da yake, tambayoyi barkatai suna cika masa kwanya... *HEEDAYA* Da idanun ta ta kafe shi tana jiran amsar sa. Ya ABDUL da bakin sa ya masa nauyi ga wani irin azababban ciwo da kan nasa yake masa, so yake ya musa wannan maganar sa take tambayar sa sai dai ji yake ya kasa, ji yake tamkar zuciyar sa za ta kama da wuta idan ya yi musu saboda wani zafi da yake ji zuciyar tana masa da alama ba zai samu salama ba har sai ya yi na'am da abin da ta zo masa da shi. Kai ya shiga gya a mata yana kallon ta da rinannun idanun sa da har yanzu basu washe ba na kukan rashin Aunty RABEEYA da ya yi wanda ya zame masa jiki. Wani shu'umin murmushin cin nasara HEEDAYA ta yi kafin ta ara jefa masa wata tambayar. "Kana so na? Za ka aure ni?" Ta tambaya tambaya tana wani ha e rai don yanzu gya a kan da ya yi hakan yana mata nuni da ta kama shi a hannu don haka dole ma ta fara yin yadda ta ga dama. Kan dai ya ara gya a mata a karo na biyu. "Ba na son auren nan ya auki wani lokaci ina so ka sanar da Abba za ka aure ni domin in maye maka gurbin Aunty RABEEYA, sunan Aunty RABEEYA ka ai da ya ji ta ambata sai da ya ji zuciyar sa ta motsa, sai dai tantamar kala anta