Sashe 1
Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry WordDocument 0Table Data [2/5, 8:11 AM] MOM MASHKUR & AFRAH: *BONONO* (RUFIN OFA DA ARAWO) NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso. *SADAUKAR* Daga farko har arshe sadaukarwa ne ga MARYAM HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya kai gare ki Allah lullu e rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah fatan alkairi. Daga marubuciyar: iyar igiya an adaidaita sahu Ungozoma ar zaman wanka Da sauran su. PAGE 1 Da tsananin murna da farin ciki nake hango shi jingine da motar da ya zo aukana saboda a yau ne muka kammala karatun mu na secondry school da yake boarding school nake yi. Sai dai ina jin mummunar fa uwar gaban da take neman ta kawo mini cikas, a gaba aya tarin kalaman da na yi ta shiryawa zan yi amfani da su wajen tona masa asirin zuciyata, ina tunkarar sa bugun zuciyata yana tsanan ta. Duk da ina jin tsoro da fargaba a kan hakan amma dai na shirya tunkarar komai don na mallakawa zuciyata wanda take da buri, kuma shi ne dai wanda ta da e tana dakon soyayyar sa haka kuma tun zuciyata tana jaririya na raine ta da soyayyar Yaya ABDULHAKEEM sai dai kash!. Ban ta a furta masa ba. Yau kwana na yi ina tufka da warwara ina sa ar jaki a kan irin yadda zan furta kalaman tun jiya da Abba ya fa a mini a waya cewa Ya ABDUL in ne zai zo auka ta . "Oyoyo Ya ABDUL" Na ce ina ame shi ta baya da yake ya bani baya ne, ina sakin jakar da na ri o a hannuna don shi bai ma san na zo wajen ba hankalin sa yana ga waya. "Oyoyo HEEDAYA" Ya ce yana raba ni da jikin sa idanun sa kafe a kaina. "Ya ABDUL" Na ce ina jin wani yanayi na yadda ya kira sunan nawa sai in ke ji kamar duk duniya babu wanda yake kiran sunana in ji ya iya fa a, tare da ba kowane harafi ha in sa sama da Ya ABDUL. "HEEDAYA an girma an kammala school" Ya fa a yana ri o hannuna tare da lakato hancina, idanuna na lumshe kafin na bu e su tarrr na sauke a kan kyakkyawar fuskarsa da kullum take mini gizo tamkar ranar na fara ganin ta. Hannu na mi a na auki jakar sakin hannun nawa ya yi Sai da muka gama saka kayan nawa gaba aya a but ina ta masa mitar bai zo aukana da wuri ba, duk yawanci awayena sun tafi, haka dai muka yi sallama da sauran da suka rage wanda ba a zo aukan su ba, na shiga motar muna agawa juna hannu cike da kewa. Hanya ya nausa motar muka kama tafiya domin zuwa garin namu mai suna Dutse, dama a garin Gumel nake karatu. Tun da ya fara tafiya motar ta yi tsit baka jin komai sai aran A.C tafiya muke yana tu i cike da nutsuwa. A hankali na waiga na saci kallon fuskarsa gabana ya yanke ya fa i ganin tamkar duk sha uwata da shi ina jin nauyin furta masa kalmar so. Kasancewar Ya ABDUL an gidan anin mahaifina sannan gidanjen mu sun kasance ma otan juna. Tun ina arama ta na taso cikin kulawar sa saboda ya kasance mai son yara, zan iya cewa bayan iyayena a duniya babu wanda ya kai Ya ABDUL da Aunty RABEEYA sona da nuna mini kulawa Aunty RABEEYA uban mu aya da ita sai dai kowa da mahaifiyar sa. "Bakin surutu dai yau ya mutu mus, ko duk kewar rabuwa da awayen ne?" Ya ce yana an waiwayo ni tare da sakar mini murmushi. Ni ma kaina na samu da sakin murmushin amma na ya e wanda iyakar sa fatar baki, saboda yadda zuciyata take cike da son furta kalaman da suke nu usar ta. "Ya ABDUL, ina so na yi maka magana" Na fa a gabana yana fa uwa. Rage gudun ya yi, tare da an kallona kafin ya mayar da kallon nasa bisa hanya ya ce "Ina jin ki" Shiru ya biyo baya kalaman sun yi tsauri wajen furtawa, nauyi da kunyar sa nake amma ina gani wannan ce damar da nake da ita in furta masa daga ni sai shi a yau ba sai gobe ba, saboda na san a'idar Abban mu daga ka gama secondry school yake maka aure gwara in tanadi mijina a hannu kar in je in zauna a gida irin na Aunty RABEEYA. "Baka mini kayan candy ba" Na samu kaina da furta hakan ba don haka na yi niyyar fa a ba sai don na rasa ta inda zan fara ina son gane bakin zaren amma kuma na kasa, nauyi da kunyar sa nake ji. "HEEDAYA yanzu kayan candyn ne kike fa a dakyar ai kin san ke ta hannun damana ce, na shirya miki abin da zai faranta miki, kin san na je india lokacin da ya kamata na yi miki abubuwan da za ki rabawa awaye, jiya na dawo amma na ce ni zan akko HEEDAYANA" Ya fa a yana sakin murmushin nan da yake narkar da zuciyata. Wani da i ya baibaiye mini ruhi a rayuwa ina son ya ce mini HEEDAYAR sa duk da ba da manufar soyayya irin ta aure yake fa ar hakan ba amma hakan yana da a raina fiye da tunanin mai tunani. Na sani cewa yana ji da ni kowa ya san hakan a family namu, tun ina mitsitsiya ta wajen sa ne wurin share kuka na shi ne mai lallashi da lalla a ni idan ina kuka, wani lokacin ya sa ani a kafa ar sa har sai na yi bacci sai dai bai san cewa tun wannan aunar da sha uwar da na yi da shi daga lokacin da na yi wayo komai ya canja na yi nutso a kogin son sa tamkar dai a rijiya mai gaba dubu da za ta yi wuyar fitowa. Ta nuna masa farin ciki da jin da in furucin sa, amma ba haka aka so ba anin miji ya fi miji kyau!. Har suka shigo garin Dutse tana jin takaicin rashin sanar da shi udurin ta. Suna shiga get in tangameman gidan nasu tun kafin ya gama parking ta hango Aunty RABEEYA ta taho da murnar ta, sai dai HEEDAYA tana fitowa ta juya mata baya tare da zun uro baki alamar ta yi fushi. "HEEDAYATA!" Aunty RABEEYA ta furta lokacin da ta araso ta rungume HEEDAYA amma ta i cewa komai. "Ya ABDUL wa ya ta a mini ar lele" "Ba ruwana kun fi kusa" Ya ce yana dariya tare da bu e but in lokacin har Na'eema, Mubashshar, da Ihsan sun fito domin taryarta. "Bake ba ce kika i bin Yaya akko ni" "Ayya sorry kin ji na tashi da ciwon kai ne sannan Ya ABDUL in ne ya sa mu zauna don shirya abubuwan da za a tar e ki amma a yi wa Aunty afwa" Ta fa a tana rausayar da kai gefe. Murmushi ta saki tana rungume Aunty RABEEYA tana jin aunar ar uwar tata duk da iyayen su mata basa jituwa kuma basa son aunar nan da take tsakanin Kayan nata suka auka aka nufi cikin gidan kowa yana murna Ya ABDUL bai shiga gidan ba sai ya juya ya tafi gidan su domin zuwa ya watsa ruwa. Suna shigowa har lokacin hannun ta sar e da na Aunty RABEEYA, da Hajiya Baturiya mahaifiyar su Aunty RABEEYA suka fara cin karo ta fito daga part in ta ri e da plate za ta nufi part in Abba. Tun daga nesa ta fara aikawa da HEEDAYA mummunan kallo na tsantsar tsana. Ita ma ramawa ta yi a fakaice ba tare da ta bari Aunty RABEEYAR ta gani ba don sauran annen nasu tuni sun riga su yin part in Hajiya Zainab mahaifiyar su HEEDAYA. Amma a fili ganin sun zo dab da juna cikin kissa da nunawa Aunty RABEEYA girmama mahaifiyar ta sai ta ce. "Momma ina yini" Ko kallo bata ishe ta ba don dama tana zuwa dab da su ta auke kai bayan ta jefawa Aunty RABEEYA tata harara na ganin ta da HEEDAYA. an jim HEEDAYA ta yi na alhinin abin da Momma ta mata. "To mene ne na damuwar? Ai in da sabo kin saba da halin gidan mu, ba za su ta a canjawa ba suna nan a yadda suke sai dai mu tun da Allah ya ha a kanmu ai ba za su raba mu ba, HEEDAYA babu abin da zai raba ni da ke babu abin da zai kankare an uwantaka ta jini da nake miki ina aunar ki zan iya sadaukar da komai a rayuwa ko mene ne in har zai saka ki farin ciki" Aunty RABEEYA ta fa a tana sakar mata murmushi kasancewar ta fi aunar HEEDAYA sosai a kan anwar ta Na'eema wacce suke ciki aya. Sai da ta raka ta har ofar falon Hajiya Zainab wacce suke kira da Umma, sannan ta dakata ba don ta so ba za ta juya, ri e mata hannu ta yi ta ce "Haba Aunty ya za ki dakata daga nan mu je ki raka ni mana har akina" Ta ce tana zum ura baki. "Zan je mu arasa ha a miki kayan tar ar da muka shirya miki ni da Yayan ki" Ta fa a tana kallon ta, ba don ta gamsu ba ta saki hannun ta suna yi wa juna murmushi, Aunty RABEEYA tana juyawa HEEDAYA ta shige falon da gudu cike da murna da farin cikin dawowa gida gaba aya, ba da sunan hutu ba don ta tsani boarding school in nan kawai don ba yadda za ta yi ne ta san halin Abban su idan ya ce kulle dole ne mutum ya ce casss ko ba ya so. Su ma su Umma abubuwan da suke yi tsakanin su da na yaran sai a bayan idanun sa ne suke yi a gaban sa sai su dinga kissa da kisisina sai dai an abin da ba a rasa ba. Da murna suka rungume juna ita da Umma, bayan nan ta zauna suna ta hira ita da Mubashshar da Ihsan. akin ta