← Book details Bonono Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 39

Sashe 37

Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*HEEDAYA* "Mai kake fa a ne wai Ya ABDUL ka san dai ko ana mini wasa a duniya ba na son wasan kishiya amma mai ya sa ka za i mini shi a yau baka san za ka iya tarwatsa walwata ba?" Ta ce lokacin da ta arasa gabansa don ta san tabbas! Sai dai in wasan yake mata amma ta san wannan ba iyayyiyar magana ba ce ko a mafarkin ta bare a zahiri. Kalaman sun yj tsauri da yawa. "Ni sa'an wasan ki ne da zan miki wasa?" Ya jefa mata maganar cikin dakewar muryar sa babu ko alamar wasa ko sassauci a furucin sa sai ya koma mata Ya ABDUL in na asali wanda ya canja mata bayan auren sa da Aunty RABEEYA. A hankali ta sulale ta dur ushe a kan gwiwoyin ta ta ora hannuwan ta a kan gwiwar afar sa hawayen nan sha e-sha e kamar an ce mata Ummar ta ta mutu cikin rawar murya ta ce "Aure Ya ABDUL? Ni za ka yi wa kishiya?" "Aure mana ba a auren ke aka aure ki? Ina so ki sani aure babu fashi, sannan ki sani ha ar ki bata cim ma ruwa ba domin kuwa ABDULHAKEEM ya da e da hango tubalin ginin da kika yi wa rayuwar sa shi ya sa ya nemar wa kansa mafita ni na fi arfin juyawa a wajen ki HEEDAYA kar ki manta za ina RABEEYA ce wacce Allah ya kar i abin sa amma ni kaina ba zan ce ga yadda aka yi na aure ki ba na san dai ni na yi furucin kuma ina tuna komai amma babu takamaiman dalilin. A yadda RABEEYA ta tafi ta barni tafiya ta bazata a shekaru alilan ban tama kawo zan kalli wata mace da sunan so ba sai ga shi a watanni alilan na yi aure auren na wai ke HEEDAYA?Abu bai tsaya a nan ba har kike rabani da uwata da ta yi silar wanzuwata a duniya ta sha wahala ta ta raine ni shin adalci ne wannan ke za ki so a raba ki da taki uwar? Ko so ne wannan ki kai ni hanyar shiga wuta tun da wofintar da iyaye ai hanyar wuta ce to ki sani ko don Abba ba zan saki ki ba amma kuma ni ma zan auro muradina sai ku zauna zaman kishi tare da ita wata ila ita ta aunaci jinina Little RABEE ta bata kulawar uwa wacce ta rasa a wajen ki kuma matsayin kina anwar mahaifiyar ta ki ji tsoron Allah kuma ki sani shi ramin arya urarre ne" Yana gama fa ar hakan bai jira cewar ta ba ya tashi tare da janye hannuwan nata da take ri owa tana ro on sa don ta kasa furta komai sai zancen bebaye take hawayen nan kamar an bu e famfo. Bai saurare ta ba ya haura sama abin sa yana ri e da mukullin motar sa. Bizigir ta yi a tsakiyar falon ta kwanta reran tana kuka tare da ambaton ta mutu ta lalace. Gaba aya duniyar take ji tana juyawa mata ta rasa makama da tunanin abin yi ta kwashe sama da minti ashirin tana kukan kafin ta tashi zaune ta fara jidar akwatinan tana jefa su kan benen. Ya ABDUL da ya watsa ruwa fitowar sa kenan bayan ya shirya ya ga kiran wayar masoyiyar sa yana shirin auka ya fara jiyo ara abu hakan ya ankarar da shi wani abu yana faruwa da alama HEEDAYA ce take masa hauka shi kuma ba zai jura ba kuma ba zai auka ba. A fusace ya fito tamkar kumurcin zaki lokacin HEEDAYA ta aga aramin kit in za ta yi jifa. "Ba na son hauka HEEDAYA ki sani nan gidan ABDULHAKEEM ne ba turun mahauka ta, ki sani ba zan lalla a ki ba idan kin ga ba za ki iya ba hanya a bu e take dama kara na miki saboda su Abba wallahi da a ce wata bare ce a yau sai na yanke igiyar aurena duka uku a kanta don ba matar zama ba ce za ta yi abin da kika yi" Yana fa ar hakan ya juya ya koma. Da ido ta bi shi har ta acewa ganin ta jin maganar sakin da kuma cewa ofa a bu e take sun razana ta. Tana ta mamakin yaushe Ya ABDUL ya zama haka ko dai aikin ta ne ta karye da wannan tunanin ta ajiye kit in hannun ta ta tafi aki tana zuwa ta aga waya ta kira Umma ta zayya ne mata wannan ne abin da ya ru a su gaba aya. Tun da ta kira HUSNA take rusa kuka gaba aya aun shiga tashin hankali suna jimantawa ita ma HUSNA kukan take taya ta tana mamakin ashe dai duk kanwar ja ce duk mazan haka suke. "Ya zan yi HUSNA Ya ABDUL ya shammace ni, a lokacin da nake tsaka da sakin jikin ni ka ai zai rayu da ni ashe dai ba haka ba ne ashe dai akwai wani oyayyan shiri da yake a bayan fage, ashe dai da ya nuna mini ya daina kula kowace mace sannan boka ya tabbatar mini da cewa ba zai ta a sha'awar aure ba an fitar masa shi a ransa ashe dai arya bokan yake yi na shiga uku hankalina ya kai ololuwar tashi mafita kawai nake neman ko ta wane hali" "To mai zai hana ki dage da addu'a ni ma in taya ki tun da aikin bokayen da malaman ba su ci ba?" "Haba HUSNA kin san dai ana jinkirta kar ar addu'a ni kuma wuri ya ure mini tun da yau saura sati guda fa ya ce wannan wace iriyar ba adsara ce da raba tsaka ta kunno kai" HEEDAYA ta fa a cikin kukan da ya i tsaya mata. "To yanzu ya kike ganin za a yi ni ma wallahi kaina ya kulle na rasa mafita da a ce ina da iko ina da yadda zan yi da sai na dakatar da auren nan haba wace ce wanna mai rawar kan za ta shigo cikin gidan ki, da a ce ma za mu san wace ce da sai na zo mun je har gida mun tsoratar da ita don ta janye udurin ta na auren sa" HUSNA ta kai maganar ranta yana una. "Ai ni ban san ma wace ce ba da alama abin an yi shi ne a munafurce don Umma ma da na kira ta yanzu hankalin ta ya tashi don bata sani ba, ni na fi zaton wata ila wannan ashshshiyar uwar tasa ce za ta saka shi yin auren wata ila ma ita ta sama masa matar ko ma ar gidan awarta ce wa ya sani" "Amma na yi mamaki bayan bokan ya ce miki ya makantar da ido da zuciyar ABDUL in daga ganin duk wata a mace" HUSNA ta ce cike da jimantawa. "Bari ke dai ina zuwa zan kira ki wallahi zuciyata zafi take ji nake tamkar na ha iyi zuciya ba mutu ko na kashe kaina" "Haba aminiyata musulma kike fa duk komai ya yi tsananj maganin sa Allah" Tsabar ma kuka ya ci arfin ta kashe wayar ta yi. Tana kwance tamkar matacciya ta rasa abin yi kamar an tsikare ta ta auki waya ta kira MEEMA dakyar ta auka bayan ta tsinke. "Ya aka yi ne?" Ta jefawa HEEDAYA tambayar HEEDAYAR tana jiyo aran taunar wani abu da alama wani abu take ci. Kunya ce ma ya kama HEEDAYA don sai ta rasa ma bakin magana gani ta daina kula MEEMA sai yau da komai ya ca "MEEME wai Ya ABDUL ne zai yi aure nan da sati aya" Ta fa a cikin muryar kuka. "Ayyiriri" MEEMA ta saki gu a sannan cikin nuna jin da i da bayyana farin ciki a muryar ta ta ce "Ya mini daidai Allah sa nan gaba ya rufe ofa wato ya auri mata hu u kin ga kishiyoyin ki uku" "Haba MEEMA don Allah ki manta da komai ki tausaya mini zan zo gidan ki ki daure ki raka nj wani wajen bokan mai aiki sha yanzu magani yanzu ya mini aiki ko nawa zan biya don a janye maganar auren nan in ya tabbata mutuwa zan yi" "Allah suturi bu wai in ji kishiyar mai doro, ai ba mutuwa ba wallahi ko mushe za ki sai dai ki yi amma ni babu ni babu ke marar mutunci da bata san halacci ba. Da kin manta da halaccin da na miki har yau baku bani amsar sa on da na tura miki ba saboda kin sake awaye shi group in MANYAN MATAN ma na ga ni na kai ki to ki are alau da sabbin awayen naki" Tana gama fa a ta kashe waya jifa ta yi da wayar a kan gadon ta kwanta ta rushe da kuka jim ka an ta akko mayafi da jaka ko ta kan Ya ABDUL in bata bi ba ta fita ta hau napep sai gida. Falon Abba ta nufa tana share hawaye Abba kuwa ganin ta ya san mai ya kawo ta amma sai ya nuna bai san mai yake tafe da ita ba. Kwashe komai ta yi ta fa a masa a ganin ta zai dakatar da Ya ABDUL daga auren amma abin mamaki sai ta ji ya fara mata nasiha a kan ta rungumi addara ta zauna a akin ta dama namiji mijin mace hu u ne. Ko cikin gidan bata shiga ba ganin ha ar ta bata cim ma ruwa ba a wajen Abba ta nufi gidan su Ya ABDUL in ra kwashe komai ta fa awa Daddy nan ya lallashe ta a kan ta yj ha uri Abba ne a cikin maganar kuma Abba ne gaba da shi. Gidan Hajja ta wuce tana zuwa ta fashe da kuka ta shiga fa a mata. "HEEDAYA auren ne sunnar ma'aiki bakya so a raya? Ita uwar ki ita ka ai take zaune a gidan ta ko kuwa tana da abokiyar zama? To ni ba na ciki da fa an rashin gaskiya, babu wanda zan fa awa a fasa aure ke da aka ce ar marainiyar nan ma baki bari ba HEEDAYA ko
Chapter 37 · 0% Book details