← Book details Bonono Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 39

Sashe 2

Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta nufa ta shiga don ta watsa ruwa har ta cire kayan, ta auki towel ta aura za ta shiga ban akin sai ta nufi jakarta da aka shigo mata da su, aukan jakar ta yi ta fito da hoton Ya ABDUL ta tsaya kallo tana rayawa a ranta. 'Da sannu ba da gajiyawa ba zan sanar da kai sirrin da yake raina, ina son ka ina mugu-mugun kishin ka, zan iya komai a kan ka zan iya fafatawa da kowa a kan ka, babu wata da zan bari ta ra e ka idan kuwa wata ta yi gigin yin hakan sai na koyar da ita darasin da har arshen rayuwar ta ba za ta manta ba' Ta fa a tana sakin murmushi tare da shafo hoton ta mayar da shi cikin jakar ta ajiye ta shiga wankan tare da auro alwala ta fito. Shiryawa ta yi ta saka doguwar riga sanna ta yi sallah. Wajen arfe biyar Aunty RABEEYA ta zo part in su ri e da wata atuwar leda, ko da ta samu Umma a babban falo ta gaishe da ita ko kallon arzi i bata samu ba bare ta saka ran za ta amsa sai ma nuna mata hanyar waje da ta yi tana cewa "To ba ar munafuka annamimiya wato ata ta dawo za ki fara mini diddibtun munafurci kina nan zaune a gida ke ba karatu ba ke ba auren ba, kin rasa mashinshini ga shi nan har anwar bayanki ta gama karatu ta dawo gida za ku jera har ma ta samu miji ta tashi, to kar ki kuskura ki zo ki goga mata ba in jini irin naki ta rasa mijin aure ko ki hure mata kunne" Umma ta fa a cike da bala'i. Ihsan da fitowar ta kenan ta samu wuri ta zauna tana ta e baki ta ce. "Umma ni ma da nake zuwa day school yanzu saura shekara biyu na kammala" "Yo ai sai ku duka ku tashi kun barta sai dai ko Alhaji ya bada sadakarta don bana jin za ta auru" Kai Aunty RABEEYA ta sunkuyar tana jin unci da ra in maganganun da take ji tamkar ana watsa mata ruwan dalma a zuciya, duka shekarun nata ashirin da aya ne fa, kawai don dai Abba ba ya bari a cigaba da karatu sai dai mutum ya yi a gidan miji shi ya sa ake ganin hakan amma da karatu take zaman gidan ma ba zai gundure ta ba bare har ake ganin ta kasa samun miji duk da samarin suna ziryar zuwa amma dai daga ta musu maganar aure sai su daina zuwa ita ma bata san mene ne dalili ba sai dai ta san Allah ba ya bacci kuma yana sane da ita. HEEDAYA da take akin ta tana gyara kayanta take jin tashin maganganu a falo hakan ya sa ta fito tana fitowa ta ga Aunty RABEEYA ta juya za ta fita, da sauri ta arasa tana kiran sunan ta tare da ri o hannun ta, cak ta tsaya sai dai bata juyo ba kuma bata ago fuskarta ba sai hawaye da yake tsiyaya. "Haba Umma kin san dai ai wurina ta zo ko? Ko don aunar da take mini ta cancaci ta samu rangwamen wasu abubuwan daga gare ki" HEEDAYA ta fa a tana kallon Ummar, tare da juyawa ta shiga aikawa Ihsan sa on harara. "To uwata fa a mini abin da ban sani ba, ke ai wawiya ce don ana nuna miki farin ha ori shi ya sa kike ganin soyayya ce, bayan ta ciki na ciki so take ta gama shiga jikin ki sai ta ida nufinta, in kin manta in tuna miki ar kishiyata ce fa, an fa a miki kishi wasa ne? Ko an fa a miki iyayyar kishi wasa ce, za su iya duk yadda za su yi su shiga jikin mu kafiin cim ma burin su" "Haba Umma bai kamata ba wanna abin da kike tun ban kai haka ba take nuna aunarta da kulawar ta gare ni, da a ce tana da wani nufin a ganina da ta da e da bayyanawa... "Ga shi in ji Ya ABDUL sar a da ankunne da agogon ni na baki, ki shirya ki same mu a gidan Ammie" Aunty RABEEYA ta fa a cikin muryar kukan da ta kasa dannewa. "Aikin banza shi ma ABDULHAKEEM in ai munafuki ne, ai wallahi tun da uwar sa ta munafurce ni to babu yarda tsakanina da shi gaba ayan ku lumbu-lumbu ne wutar ayi bata kama ba ta ha e wuri da haya i" Umma ta fa a tana jin zafi da ra i a zuciyarta kasancewar ta uwar gida, sannan kafin a auro Momma mahaifiyar su RABEEYA wacce ita ce amarya, to Umma bata da awa kuma abokiyar shawara sama da Hajiya Fati wato mahaifiyar ABDUL kamar ba facaloli ba haka kan su yake a ha e, amma daga bisani da aka auro Momma suka yi wani rikici da Ammien da Umma shikenan sai ala a ta inke tsakanin Ammie da Momma aka dawo ana zaman doya da manja da Umma da Ammien wannan dalilin ne ya sa Umma ta tsani ABDUL gaba aya bare kuma RABEEYA da dama kishin da yake tsakanin iyayen yake tasiri har kan an su. Kowa ya tsani an kowa, basa duba zama ya ha a sun girma babu wacce za ta fitar da kowacce amma kullum kishi yana nu usar su sun kasa ba zuciyar su ha uri su yi zama cikin salama da aminci. Aunty RABEEYA bata jira cewar HEEDAYA ba ta dam a mata ledar ta juya da sauri jin kuka mai sauti yana neman wace mata. HEEDAYA rasa bakin magana ta yi ta juya fuuuu fa tafi akin ta. Duk da tana jin abin da aka yi wa Aunty RABEEYA har asan ranta amma jin wani sassanyan dadda an turare mai narkar da zuciya ya ziyarci hancin ta gaba aya sai ta shagala da son ganin turaren tun da dai in aka auke sar a da ankunne da agogo sauran duk Ya ABDUL ne ya bata kenan turaren nan daga gare shi ne. Wasu turaruka ne guda uku masu bala'in amshi sannan daga ganin su masu tsada ne, sai wani leshi da aka yi wa riga da skirt inkin ya tsaru daidai jikin ta da mayafin su, sai takalmi sai kwalin waya iphone 16 sai kuma sar a da ankunnen da agogon wanda Aunty RABEEYA ta bata. Da i ya cika mata zuciya a duniya in akwai kyautar da ta fi so ita ce ta Ya ABDUL sai kuma ta masoyiyar ta Aunty RABEEYA. A gaggauce ta shirya, kayan sun yi matu ar kar ar ta, wayar ta jona a caji bayan ta mayar da sim in ta na cikin wayarta da take amfani da ita idan ta zo hutu. Fitowa ta yi tana bu amshi, lokacin da ta fito babu kowa a falon sai TV tana aikin ta. Duk can ta samu sauran an uwan nata har da Ya ABDUL da ya shirya shi ma ya yi matu ar kyan da ya sa ta shagala da kallon sa, bata ba kanta wahala wajen shiga gaishe da Ammie ba don ta san ko ta je ma dakyar ta amsa. warya- waryar fatin da aka shirya mata na kammala karatun wanda ya faranta ranta matu a, har da aton cake aka mata mai auke da sunan ta a jiki wannan duk aikin Ya ABDUL da Aunty RABEEYA ne . Sai da aka kira magriba suka tashi, an ci an sha an yi hotuna, gida suka dawo akin ta ta shige bayan ta gabatar da sallaha ta kwanta tare da kunna wayar. Ta fara danne-danne sai ta jiyo muryar Umma tana wala mata kira. Fitowa ta yi ta same ta a falo ita ka ai ce. "HEEDAYA" Umma ta kira sunan ta amsawa ta yi tana mayar da hankali kan Ummar. "Ina fata kin fitar wanda kike so, kin san dai halin Abban ku ni bana son duk abin da zai zama matsala kuma bana son ki bar mini abin gori daga kishiya da facala. Ina so cikin wanda suke neman ki, ki tabbatar kin samu wanda za ki fa awa Abban ku a matsayin abokin rayuwar ki idan an tambaye ki, bana so a ce kin zauna a gida na fi so kamar yadda dokar sa take daga an gama secondry a yi aure ina fatan ba za ki bani kunya ba" Murmushi HEEDAYA ta yi tana jin da in hirar nan dama ta da e tana son fa awa Umma muradin ta amma sanin tsakanin ta da Ammie ya sa take ta dakon son a ranta amma dai yanzu za ta yi arfin hali ta tari aradu da ka, ta fa a mata za in ta in ya so ko mai za faru ta shiryawa hakan in ya so sai ta tunkari Ya ABDUL in da hujja tun da dai ta san ba zai ta a maido mata da on barar tayin soyayyar ta ba, kuma duk runtsi ta shiryawa kowane alubale domin cikar burin ta na auren sa. "Umma ina da wanda nake so, na da e da za ar sa a matsayin abokin rayuwata kuma uban ana" Wani murmushi Umma ta saki tare da dafa kafa ar HEEDAYA ta ce. "Dama ni na san ba a rasa nono a ruga, tabbas! Na san da cewa ba za ki ta a rasa mai auren ki ba, ai ke ta daban ce babu mu babu barin abin gori a dangi na yin kwantai, shin wane ne shi? an gidan waye?" "Umma ba shi ya ce yana sona ba, bai ta a sanin ina son sa ba sai dai na san ba zai guje ni ba duk runtsi" Galala Umma take kallon ta jin kalaman da suka raunata arfin gwiwar da take ji na samun mijin da arta ta yi sai dai shin wace irin mgana ce wannan. "Kina da hankali HEEDAYA wanda bai san da matsayin son da kike masa bane za ki fitar a matsayin mijin aure!? Yanzu a an lokacin nan soyayyar sa za ki nema ko fitar da shi ga Abban ku a matsayin miji? Kin san Abban ku
Chapter 2 · 0% Book details