← Book details Bonono Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 39

Sashe 22

Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ranta. Amma sai ta hau neman tsari da shai an mai sanya wasi-wasi son ta san sharrin sa ne . "Ai kuwa yana dab da dawowa" Ta ce ita ma tana dariya tare da wucewa ta je tana jera masa kayan abinci a dining. Da wani kallo mai cike da harara HEEDAYA ta bi Aunty a fakaice ba tare da ta bari ta gani ba, don ganin yadda ugun Aunty RABEEYAR yake juyawa a cikin skirt in bare Aunty RABEEYA mai hips sosai sa anin HEEDAYA da take shafal. Suna zaune suna an ta a hira wayar RABEEYA ta yi ara a aki tafiya ta yi tana dubawa ta ga Momma. Bakin gado ta zauna tana amsa kiran bayan sun gaisa. "Da baki kira kin fa a mini ba ai na ji" "Mai Momma?" Ta tambaya cikin sanyi murya. "Ban sani ba, wai ke mai ya sa RABEEYA kamar wata nusara kike yanzu HEEDAYA ce za ta aura gidan ki amma kika saki baki shameme kike zaune" "To ina zan je Momma, kuma HEEDAYA fa anwata ce sannan shi ma Ya ABDUL ai ba bare ba ne an uwanta ne sannan ma Abba ne fa ya ce ta zo kin... "Ya isa haka RABEEYA sau nawa zan fa a miki an uba kuke da HEEDAYA ni kuma kishiyoyi muke da uwar ta kuma ba zaman lafiya ba ne a tsakanin mu a kan mai za ki yarda ta zo ta tare miki a gida ai da Abban naku ta kira da kin sanar masa cewa kin ji sau i ba sai ta zo ba" Ta fa a a harzu "To Momma za a kiki gaba" "Kar ma a koka" Ta ce tana datse kiran. Ajiyar zuciya ta sauke tare da tashi ta saka wayar a caji. Fitowa ta yi a daidai lokacin kuma Ya ABDUL ya shigo falon auke da sallama a bakin sa. Da an gudu HEEDAYA ta nufe shi tana masa oyoyo tana zuwa ta kama hannun sa aya da yake ayan yana ri e da jakar wajen aikin sa. Aunty RABEEYA da ta araso tsakiyar falon sai suka zame mata hoto jin shai an yana neman kissima mata jin kishin anwar ta sai ta yi saurin kawar wa tare da irar murmushin ya e wanda iyakar sa le anta, ta sani cewa HEEDAYA tana iya kama hannun Ya ABDUL a baya duk da ba muharramar sa ba ce amma tun sabon yarinta har yanzu bata daina ba, amma ta auka tun da ya yi aure yanzu ita ma kuma ta mallaki hankalin kanta za ta daina sai dai kuma ga shi bata daina ba.Yana ar dariya yana kallon HEEDAYA don shi ko ka an bai kawo cewa hannun sa da HEEDAYA ta kama zai ona ran Aunty RABEEYA ba. Ganin ta yi turus a gefe aya sai ya ce "Yau ba oyoyo Hayati?" Ya ce yana jifanta da wani kallon wanda ya sa fuskar HEEDAYA sauyawa tamkar dai mijin ta ne ya yi wa kishiyar ta kallon, hatta sunan da ta ji ya kira Aunty RABEEYA da shi sai da ya sosa ranta ta ji babu wanda ya dace ya kira da sunan sama da ita. "Oyoyo sannu da zuwa" Ta fa a da baki tana dariya a maimakon da tana zuwa sai ya rungume ta amma yau ga shi an samu sauya sai ya fara tunanin ko ganin HEEDAYA ne ya sa ta i masa hakan. "Na i wayon" Ya ce yana arin janye hannun sa daga ri on da HEEDAYA ta masa amma sai ya ji ta i saki kallon ta ya yi sai kuwa ta saki hannun nasa, wajen Aunty RABEEYA ya nufa yana sanya hannu ya janyo ta tare da ma alo ugunta aya hannun ri e da jakarsa. "Mu je ki ha a mini ruwan wanka" Ya ce yana kallon fuskar ta. Bata masa musu ba don ta ji da in yadda ya nuna kulawar sa gare ta hakan yana nufin zai iya nuna soyayyar sa gare ta a gaban kowa tuni ta shagala da cewa HEEDAYA tana wajen. Sama suka haura har lokacin yana ri e da ugunta ita kuma ta an kwantar da kanta a gefen kafa ar sa. Tun da suka nufi matakalar benen take kallon bayan su ranta yana matu ar suya tana ji tamkar ana watsa mata ruwan barkono a idanun da take kallon su. Har suka acewa ganin ta tana tsaye a wajen tamkar an dasa dutse. Hawaye ne suka shiga sintiri a fuskar ta da gudu ta yi hanyar akin da aka sauke tana zuwa ta fa a kan gado tare da fashewa da kukan ba in ciki da kishin da ya cika mata zuciya. Tana tunanin wata ila ma yanzu sai sun yi wani abu kafin ya yi wankan, tana ganin ta zo gidan don samun warakar abin da take ji a zuciyar ta ashe dai ta zo inda za a ke fama mata ciwon ne... *MARYAMA* Tana tafiya gaba aya jikin ta ya mata nauyi saboda mutuwar Baffa ga damuwar rashin sanin takamaiman inda za ta je, sannan ma uwa uba abin da za ta tarar a inda za ta je in. Tana tafiya tana ha uwa da mutane wa anda suke tahowa don zuwa wurin mutuwar wasu a afa wasu kuwa a mashina. Wasu mata da ta ha u da su tana ji da za ta gifta su suna cewa an ce ita ce silar mutuwar mari in nata ba in cikin, abin da take auke da shi ne ya sa ya ha iyi zuciya ya mutu!. Wannan furucin nasu ya tabbatar mata da cewa zance har ya fara yawo daman ya a jita-jita ai ba aramin abu ba ne ga mutane bare kuma aramin auye da ko ina dama ba wani tazara ne da garin nasu ba. Ta wuce gari uku kenan a afafun ta ga gajiya zuwa yanzu dakyar take aga afafun ta sai ogwaron ta da ya bushe saboda bu atar ruwa don ita bata ji ko abinci za ta iya sakawa a bakin ta saboda mutuwar mahaifin ta. Tana dab da shiga auye na hu u ta ga wasu yara suna aukan ruwa a famfo ta ru i su bata ruwa za ta sha, a marfin bokiti wani yaro ta taro ya mi a mata kar a ta yi sai dai tana kur a ta ji aci ruwan kawai Baffa ne a ranta hakan ya ta ji wani kuka ya taho mata ruwan ta watsar ta mi a musu marfin ta ce ta gode ta cigaba da tafiya. Tana dab da fita daga garin can arshen garin ganin wani tsohon gini na asibiti ganin magriba ta yi kuma babu mutane wajen da yake arshen gari sai wani gida da ta gani daga can gefe shi ka ai. Cikin asibitij ta shige duk sai ura kasancewar ma duk an ciccire windoji da ofofin haka ta shiga wurin ta ajiye kayanta sai kuma tunanin yin sallah ya fa o mata don babu sallar da ta yi ba azhar ba la'asar ga yanzu magriba ta yi. Tsoron kar a ganta duk da bata zaton garin za su iya sanin wace ce ita tun da akwai tazara sosai da auyen su tun da gari uku ne a tsakani sai shi auye na hu u. Tana zaune a kan kayan nata ta dafe fuskarta da hannu biyu kuka take marae sauti ji take tamkar ta koma auyen su ta yi tozali da kabarin Baffa kewar sa take ji sosai tana jin ciwo da ra in rashin sa. Tabbas!. Shi ne gatan ta ga shi yau aya da ba ya raye har ta fara maraici ta shiga wani hali wanda ko wurin zama ya gagare ta hasali ma bata san ina za ta je ba ha a idanun sa ma mashi ne tun da ga shi idanun sa suna kawa har ta yi ban kwana da gatan da take jin ya rage mata a duniya. 'Mai ya sa? Mai ya sa aka haife ni a haka? Mai ya sa mahaifiyata ta samar da ni ta makauniyar hanya? Ashe tana tsoron abin kunya amma ta yadda ta same ni ba ta hanyar aure ba, amma duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubar da ruwa. Shin mene ne laifina? Yanzu ga shi ni ban san ba ma shin tana raye ko ta mutu? Idan tana raye mai ya sa ta haife ni bayan bata sona shin ta jefar da ni, ina mahaifin nawa? Su duka basa bu atata, bani da laifin komai bani na za i zuwana duniya ta wannan hanyar ba amma mai ya sa nake girbar abin da ba ni na shuka ba?. Bayan wa annan abubuwan ga wata oyayyar addarar da ban san ta yaya ta wanzu a jikina ba, ya aka yi nake da ciki ba tare da na yi zina ba? Ko wannan yana cikin biyan bashin da iyayena suka ci na zina? Dama ko baka kusanci namiji ba kana iya samun ciki anya? Ko dai a kaina ne hakan ta faru ga rashin Baffa wayyo ni!. Tabbas ni kaina tausayin kaina nake' Ta arasa fa ar hakan a zuciyar ta wani kukan tausayin kanta yana wace mata ta shiga rera shi a fili ba tare da ta shiryawa hakan ba. "Waye a nan?" Ta tsinkayi ana tambayar ta wata fa uwar gaba ce ta ziyarce ta da sauri ta saka hannu ta dam e bakin ta da hannu biyu tana zare ido ta cikin an duhun magribar da ya fara yi wa wajen awanya... MAMAN AFRAH 09013181851 [2/16, 7:55 PM] MOM MASHKUR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/F7TUZezpOWLKYnyTNFuy2Y BONONO (RUFIN OFA DA ARAWO) NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso. *SADAUKARWA* Daga farko har arshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya kai gare ki Allah lullu e rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah fatan alkairi. Daga marubuciyar: iyar igiya an adaidaita sahu Ungozoma ar zaman wanka ara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* PAGE 10 *HUSNA* Tana nan zaune amma babu alamar HAMEED zai fito daga akin bare har ta saka ran za ta samu biyan bu ata sai dai bata karaya ba domin kuwa a ranta
Chapter 22 · 0% Book details