Sashe 5
Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da take kwance a doguwar kujera a falo gaba aya hankalin ta yana kan HEEDAYA da ta yi fushi kuma babbar damuwar ta bata san mene ne dalilin fushin ba, ga Momma ta dame ta da maganar shirye-shiryen biki. Kiran da ya shigo wayarta ne ya dawo da ita hayyacin ta daga nutson da ta yi a kogin tunani. Ganin sunan Ya ABDUL har sai da numfashin ta ya yi barazanar kufce mata saboda yadda ta tsorata kiran ya zo mata a bazata, tunani barkatai suka cushe mata walwa a kan ko ya kira ta ne ya kora mata garga Kasa agawa ta yi har sai da ta tsinke wani kiran ya shigo, Ya ABDUL kuwa har ya fitar da ran za ta auka sai kuma ya ga ta auka. Aunty RABEEYA wayar ta kai kunnen ta hannunta yana karkarwa tana jiran jin abin da zai fa a mata. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke wanda har sai da ita kanta ta ji aran saukar ajiyar zuciyar. "Ganin nan zuwa in same ki a falon ba i" Haka kawai ya ce cikin bada umarni ya kashe wayar. Duk da bata gama tantance dalilin zuwan nasa ba amma a alla ta ji sanyi da rangwame don ta auka da fa a zai balbale ta. "Ina za ki je?" Momma ta jefa mata tambayar. "Ya ABDUL ne yake kirana" Ta fa a cikin sanyin murya. Wani murmushi Momma ta yi bata ce komai ba. Jikin ta sanyi alau ta nufi falon, ko da ta je shiga kawai ta yi ta zauna da yake ma falon hanyar get yake zamanta ke da wuya ko minti uku warara bata yi ba ya shigo da sallama. Kanta a sunkuye har ya shigo ya yi wa kansa masauki a kujerar da take dab da tata. HEEDAYA kuwa tana ta arin ha a kalmomin da za ta yi amfani da su wajen sanar masa damuwarta har kiran ya yanke wayar ta ajiye zuwa can ta ara akkowa ta bi kiran lokacin yana falon ba in tare da Aunty RABEEYA kiran nata ya shigo. "Hlo Ya ABDUL" " Gani a gidan ki zo ina falon ba i akwai magana mai muhimmanci" Haka kawai ya ce ya kashe wayar. Bata san ta aka yi ta tashi ba amma dai ta ganta a tsaye am ko wayar bata auka ba ta fito gabanta yana fa uwa ta nufi falon ba in tana rayawa a ranta wata ila ya zo ya ce yana son ta ne, ya zo ya furta mata kalmar so ne... MAMAN AFRAH 09013181851 [2/6, 10:12 PM] MOM MASHKUR & AFRAH: BONONO (RUFIN OFA DA ARAWO) NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso. *SADAUKARWA* Daga farko har arshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya kai gare ki Allah lullu e rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah fatan alkairi. Daga marubuciyar: iyar igiya an adaidaita sahu Ungozoma ar zaman wanka ara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* PAGE 3 Gaba aya zuciyar ta ta kwa aitu ne da son jin furucin sa a gare ta, ba furucin komai ba face na so da auna tana fatan hakan, idan kuwa har ya furta to ai shi ba mace ba ne da za a ce za a masa dole, kin ga ita Aunty RABEEYA sai ta ha ura wannan ne abubuwan da take rayawa a ranta har ta araso falon. aga labulen ta yi tsabar hankalin ta ma ba ya tare da ita saboda zumu i da fargaba ta manta da yin sallama. Sai dai abin da ta gani wanda idanunta suka yi tozali da shi, ya so zautar da ita domin kuwa ta ki ima. Ganin Ya ABDUL zaune a kujerar dab da Aunty RABEEYA da ta sunkuyar da kai tana wasa da hannun ta shi kuma ya ura mata idanu yana jifan fuskarta da wani irin kallo mai unshe da ma'anoni da dama, ko wanda ba shi ake yi wa kallon ba idan ya gani ya san so ne mai zallar cike da auna bare kuma wanda ake yi wa kallon. "Ina son ki RABEEYA ina aunar ki ina son na aure ki a kwana kusa, domin ki dawo kusa da ni mu rayu a inuwa aya... Wannan furucin da yake fa a yana wani murmushi su ne suka daki kunnuwan HEEDAYA ta ji tamkar wanda aka watsa mata tafashashshen ruwa a jiki, karkarwa ta shiga yi jin jikinta ya auka tamkar mazari, lokaci guda wani abu ya zo ya tokare a zuciyar ta walwar ta ta toshe ta ma rasa wane abu ya kamata ta yi, a hankali ta saki labule ba tare da sun san da zuwanta ba bare har su ganta juyawa ta yi da gudu ta nufi part in su. akin ta ta shiga ko rufewa bata yi ba ta kwanta tare da sakin kuka mai cin rai, tana jin wayar ta tana ta ruri bayan jimawa ka an amma ko agowa bata yi ba ta san ba zai wuce Ya ABDUL ba, wanda a yanzu take jin haushin sa don ya mata gagarumin laifi, laifin kuwa bai wuce na furtawa wata a mace kalmar so ba kalmar da ta yi ta dakon ranar da zai furta a gare ta amma hakan ya gagara ta ci burin furta masa ita ko da ba zai amince ba, amma yau ya furtawa Auntyn ta RABEEYA wannan wace irin ba ar rana ce? Sai dai abin mamaki sai ta ji duk duniya babu wanda take jin tsanar sa sama da Aunty RABEEYA ba don komai ba sai don wanda take so wato Ya ABDUL ta furta kalmar so a gare ta. Ya ABDUL kuwa bayan ya gama kiran HEEDAYA ganin bata zo ba sai ya yanke shawarar isar da sa on nasa tun da ji yake ya agu ya furta mata. Shirun Aunty RABEEYA da yadda take sakin wani sassanyan murmushi ya tabbatar masa da maganar sa ta samu matsugunni a wajen ta, hakan ya sa bayan ya isar da sa on ya ara kiran HEEDAYA jin bata auka ba sai suka shiga tattaunawa tana fa a masa abin da Abba ya fa a mata azu sosai ya ji da in jin wannan batu sai ya shiga godewa Allah. A can su Ya ABDUL bayan Daddy ya fa awa Ammie abin da suka yanke shi da Abba na ha a Ya ABDUL da Aunty RABEEYA sosai ta ji da i tamkar ta zuba ruwa a asa ta sha. Umma kuwa abin duniya ne ya ha e mata goma da ashirin, sosai take jin ba in cikin wannan auren da za a ha a saboda ta san sai sun ara ha e mata kai. Wani irin takaici take jin don yanzu in akwai abin da yake ci mata tuwo a warya bai wuce ha in kan Hajiya Fati da Hajiya Baturiya ba. Jin ta kasa jurewa da sauri ta shanye damuwar ta akko wayarta ta shiga dokawa Hajiya Aisha awarta kira, bugu aya biyu ta auka tamkar wanda take jiran kiran dama. "Barka da dare awata kin wuni lafiya?" "Ba lokacin gaisuwa bane babu lafiya" "Subhanallahi! Mai yake faruwa ne awata?" "Wani bala'i ne ya tunkaroni" Nan ta kwashe abin da yake faruwa ta fa a mata, har furucin HEEDAYA a kan soyayyar ABDUL in. Wani uban ashar mai mai o Hajiya Aisha ta narka kafin ta ce. "Amma ke dai wallahi ban san ranar da walwarki za ta fara aiki babu gargada ba, yanzu a ce HEEDAYA ta miki wannan furucin maimakon tun kafin shi Alhaji Bashir in ya tara ku ki je ki tunkare shi da maganar, da a ce kin kirani a lokacin kin fa a mini da na baki shawarar yadda za ki yi, ai shi ya sa a rayuwa ba a so mutum aya ya yanke hukunci da kin ga idan ya ji wannan furucin dole ya dakatar da maganar shegiyar kwantan yarinyar can RABEEYA amma yanzu kin bari komai ya ca "Haba Hajiya Aisha ya ana nuna miki annabi kina runtse idanu? Ina nuna miki gabas amma kina kallon kudu? Maganar yaron can an gidan Hajiya Fati fa nake miki amma kina batun in amince da batun HEEDAYA. Shin har kin manta butulcin da Hajiya Fati ta yi wa awance na da ita? Kin manta yadda kishi ya rufe mata idanu ta turbu awa idanun ta toka ta shuka mini rashin mutunci a kan abin da bani da masaniya tun daga nan sai ba ar gaba ta koma suka jone da kishiyata, amma yanzu kike batun amincewa da auren su in ce na aurawa ata wa? an ma iyata k... "Don Allah dakata Hajiya Zainab, duk kin harzu a sai zuba kike ba comma ba fulstop mai ya sa wani lokacin tunanin ki irin na yara ne? " if Hajiya Zainab ta yi ranta yana una wai ita ce mai tunani irin na yara Hajiya Aisha bata jira ta amsa mata ba don bata ma bata damar ba ta cigaba da fa "Ita Hajiya Fati ba saboda mijin ta Alhaji Mukhtar ya ga awarki Hajiya Bilkisu ya ce yana so ba ne asalin rigimar, duk da ke baki san ma sun ha u sun ulla soyayya ba amma da batun aure ya tashi ta ora laifi a wuyanki tana ganin da ha in bakin ki za a ci amanarta a mata kishiya, duk irin amincin da yake tsakanin ku amma ta sa afa ta yi fatali da su, ta shuka miki rashin mutuncin da kika biye mata kuka kwashi an kallo, kuma daga arshe auren bai yiwu ba saboda masifar fa an da aka sha yi ba sai ta koma ta jone da kishiyar ki ba?.. "Sai wani maimaicin abin da ya wuce kike na fi so kawai ki fa a mini abin da zai rage mini zugin da nake ji a zuciyata amma kina mini lissafin abin da na sani" Hajiya Zainab ta katse ta. "Ki cigaba da saurare na za ki ji bakin zaren, to idan yanzu HEEDAYA ta auri ABDUL kin ga mun jefi tsuntsu aya da dutse biyu. Na farko an ta ya dawo hannun mu tun da yana auren HEEDAYA a nan ne za a