← Book details Bonono Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 39

Sashe 19

Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanin kan ki ne baki da gadon sa! Ai ni dama na san barewa ba za ta yi gudu anta ya yi rarrafe ba, yadda ta samar da ke ta arauniyar hanya shi ne ke ma kika akko naki cikin za ki samar da wani ko wata ta arauniyar hanyar" Inna da ta samu MARYAMA zaune a aki ta fa a mata. "Don Allah Inna ki yi ha uri wallahi ban san inda zan je bani da kowa kuma bani da komai" Ta fa a cikin ro o hawaye yana zuba don ganin ta tausaya mata amma babu wani tausayi ta ce ta bata minti ashirin ta fice musu daga gida ta tsani ganin ta. Kayanta ta ha a ta fito daga aki ta arasa gaban tabarmar da su Innar suke zaune ta ce "Inna Baffa ya ce mini in auki kaya a akwaitin arfen saman lokar sa" "Ba sai ki je ki auka ba indai wannan kayan ne da yake ajiye da su shekara da shekaru" Jiki babu wari ta je ta aukko ta fito ta saka a cikin kayan nata. "Inna zan tafi don Allah ku yafe mini wallahi ba ni... "Har duniya ta na e ba zan ta a yafe miki ba, kin yi silar rabani da mahaifina" Maimunatu ta fa a tana aika mata kallon tsana Inna kuwa ko kallo bata ishe ta ba sauran matan wajen ma maimakon su bada baki sai zuga suka shiga yi. Haka ta tashi auke da kayan a hannun ta har ta kusa fita ta juyo tana yi wa gidan kallon arshe tare da ficewa. A ofar gidan ta samu maza zaune a tabarma. Haka ta wuce tana sunkuyar da kai ta nufi hanyar bayan gari tana iya hango hanyar ma abartar daga nesa tana jin kewar Baffan ta maganin kukan ta, Baffan ta mai share mata hawaye Baffan ta mai yarda da ita mai fa a da kowa don ganin ya kare ta amma yau an wayi gari asa ta rufe masa idanu. Tafiya take a afafun ta bata san ina za ta dosa ba, bata kuma san ina za ta je ba sai dai ta san ko ina za ta je dole ta yi tazara da garin don daga garin nasu da ta baro har sauran auyukan wa anda suke ma otaka da shi duk sun san wace ce ita kuma ta san babu wanda zai yarje ta zauna masa a gida kai hatta gari ma sai an yi da gaske, can ma ana yamatar ta sanadin bata da iyaye ba a san su waye iyayen ta ba bare yanzu kuma ita ce mai auke da cikin!. *HEEDAYA* Bacci ya auracewa idanun ta, ranta a ace yake tana jin tamkar ta zama tsuntsuwa ta je gidan Ya ABDUL in ta hana su gabatar da komai ko ta samu saasuci amma ina!. Ba in cikin da take ji a zuciyar ta kwatankwacin ba in ciki da acin ran da wacce aka yi wa kishiya take ji a ranar da amaryar ta tare. Haka ta kwana da zulumin Aunty RABEEYA ta hau matsayin ta yanzu kam iyayyar da take mata ta zama biyu don ta kusanci mijin ta yanzu zafin yana damfare da zafin kishin Ya ABDUL da take jin hawa da sauka na farashin soyayyar sa tamkar wanda ake rura wuta haka wutar son sa take balbala a zuciyar ta so take ma ta yakice shi amma abu ya ci tura!. Wajen arfe hu u na asuba ta ji ta kasa jure yanayin da take ciki, ji take tamkar an akko dutse an ora a ashin irjin ta, irjin ya yi mata nauyi sosai. A arshe ta yanke hukuncin kiran wayar Ya ABDUL in don ko ta rage zafi da ra in da take ji na kishi fatan ta a zuciyar ta shi ne Allah sa dai babu wani abu da ya wakana a tsakanin ma'auratan biyu!. Don ko da su Umma suka ce bokan ya ce akwai aure tsakanin ta da Ya ABDUL sai ta ji ta ara ora rai a kansa duk da kasancewar sa miijn ar uwar ta kuma da a ce tana da iko da ta dakatar da komai don a jira lokaci a jira ranar da zai zama nata mallakin bata so ko ka an ya kusanci wata a mace matsawar ba ita ba ce. Cikin dakiya da rashin gudun abin kunya ta aga wayar ta kamo sunan sa ta shiga doka masa kiran. A can gidan amarya kuwa bayan komai ya gama wakana tsakanin su, cikin farin ciki da annashuwa kowa ya yi murna da kasancewa da abokin rayuwar sa Ya ABDUL sai albarka yake sanyawa Aunty RABEEYA ita kuma duk kunya ta dabaibaye ta ji take tamkar asa ta tsage ta shige ciki saboda nauyi da kunyar sa. Ganin dosowar asuba sai ya ce su je su yi wanka, da to ta amsa masa tana shirin sakkowa daga gadon sai ji ta yi an yi sama da ita, hannu ta sanya ta rufe idanun ta gaba aya kunyar sa take ji bata san dai ko don ranar farko ba ce kuma a daren farko amma dai ji take tabbas za ta dawwama da kunyar sa. Ruwan umi ya ha a ya saka ta a ciki ta gasa jikin ta. Sannan suka gabatar da wankan tare kamar yadda annabi S.A .W ya ce yana da kyau ma'aurata su yi wanka a tare hannayen su suna gwauraya a ruwan. Kasancewar tana ta jin kunya ta i sakin jiki da shi, sai ta riga shi gana alwala ta fito daga bayin ta bar shi zai yi alwalar. Towel ne aure a jikin ta sai wani arami da ta na a a kan nata tana tsane ruwan. Wayar Ya ABDUL da take ajiye a gefen bed side drower ta hanga tana kawo haske tana aukewa har ta banzantar da wayar ganin ba hurumin ta ba ne, kuma dai ta san an ce duba wayar miji tamkar mace tana yankan albasa ne wato tana gani idanun ta yana hawaye don ba lallai abin da za ta gani ya zama mai farantawa ba ita kuwa ta da e da sanyawa ranta cewa babu ita babu binciken wayar miji kamar yadda ta ji ana labarin wasu suna yi har a yi fa a a kan hakan wasu har igiyar auren su ake tsinkewa ta sanadiyyar hakan shi ya sa ta ga maganin kar a yi to kar a fara. Har hasken wayar ya auke sannan ta juya wardrobe tana son samu kayan da za ta sanya a jikin ta, amma sai ta ara ganin wayar ta kawo haske a karo na biyu, a wannan karon sai ta kasa ha uri ta nufi wayar ba don binciken wanda yake kiran ba sai don son ta ga mai kiran sabon ango a wannan lokaci. 'Ko dai Ya ABDUL yana da wasu an matan ne shi ne suke kiran sa wata ila bai sanar da su ya yi aure ba' Wani sashen na zuciyar ta ya kissima mata hakan. "HEEDAYA" Shi ne abin sa ta gani yana yawo akan screen in wayar, gabanta ne ya yi mummunar fa uwa tana ji a ranta anya lafiya kuwa? Sannan dama zuciyar ta tun jiya take cike da zulumin rashin samun wayar HEEDAYA kasancewar a kashe, sannan tana ta mamakin yadda ba ta zo kawo amarya ba, ta yi kewar ta, tabbas za ta so a ce ita HEEDAYA ta kira saboda ta san ta fi Ya ABDUL kewar ta sai dai zulumin kiran na lafiya ne kuwa shi ne abin da ya fi aga mata hankali. "Mene ne" Ta tsinkayi muryar Ya ABDUL ashe har ya fito daga bayin ya zo bata sani ba. "HEEDAYA ce fa take kiran ka" "Kuma mene ne na ru ewar?" "Kar fa ko ba lafiya ba" "Sai ka ce baki san rigimar HEEDAYA ba wata ila saboda ke bata yi bacci ba yau" "Amma a wayar ka ta kira fa" "Kuma ke take nema ba" Ya bata amsa tare da juyawa ya haura sama akin sa domin shiryawa. Shiru ta yi dai tana zulumi a zuciyar ta har wani kiran ya shigo, wayar ta auka ta zauna a bakin gado tare da manna wayar a kunnen ta. HEEDAYA wacce take jin bugun zuciyar ta yana sama da asa jin duk kiran da take ba a auka ba, ta fara tunanin suna can suna soyewa wanda tunanin hakan da ya fa o mata ba aramin ba in ciki ta unsa a ranta ba. Sai dai jin wannan karon an aga kiran sai da ta ara dubawa ta tabbatar an aga in kafin ta kai wayar kunnen ra bayan ta sauke oyayyar ajiyar zuciya. Ji take tana kewar sa sosai ji take tamkar ta shekara bata ji muryar sa ba. Idanu ta lumshe bayan ta gyara kwanciyar ta, tana jin damuwa da uncin zuciyar ta yana wankewa cikin wata muryar da bata san tana da ita ba ta ce. "Hlo Yayanah!" Aunty RABEEYA da sauri ta janye wayar a kunnen ta don yanayin yadda HEEDAYA ta yi furucin sai da ta ji wani iri da a ce ba HEEDAYA ba ce wata macen ce da ban da babu makawa za ta ce budurwar sa ce don yanayin yadda ta yi furucin ya nuna tamkar akwai wani abu a asan zuciyar ta. Amma sanin HEEDAYAR ta ce sai wani murmushi ya su uce mata ta ce "HEEDAYA tah" Da mugun sauri HEEDAYA ta cire wayar daga kunne ta, tare da tashi zaune gabanta yana fa uwa don bata ta a zaton za ta ji muryar Aunty RABEEYA ba duk da ta san za su iya zama waje aya a yanzun amma bata kawo cewa har an kai lokacin da za ta iya aga kiran ba sai dai wani ari na zuciyar ta ya tunasar da ita cewa yanzu fa matsayin matarsa take. Wani ululun ba in ciki ne ya tokare mata zuciya tabbas bata ara tabbatar tana da mugun kishi ba sai yanzu da ta ji Aunty RABEEYA ta aga wayar Ya ABDUL a take zuciyar ta ta shiga hasko mata huton su na wata ila ma kan Aunty RABEEYAR ma yana kafa ar Ya ABDUL Wani kuka ne ya wace
Chapter 19 · 0% Book details