← Book details Bonono Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 39

Sashe 23

Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana tunanin ko dai maganin ne bai gama bin jikin sa ba bare har ya fara masa aiki. Hakan ya saka take zaune tana danna waya wtsapp ta shiga ta bu e group in nan nasu wanda iya matan aure ne kawai a ciki, duk wata mace wacce ba matar aure ba ko ta shiga waje ake yi da ita, shi ya sa ma kana shiga group in za ka ci karo da dokokin group in wanda wa anda suka san su an mata ne ko zawarawa ma suna ganin dokokin suke fita daga group in shi ya sa ma yawanci duk sai ta dalilin wasu ake shigowa ma'ana sai kina da awa a cikin group in sannan idan za a saka ki sai kin bi ta hannun admin ta tsare ki da tambayoyi kamar ba gobe shi ya sa ma sun fi yin adding da wuya su fitar da link. MANYAN MATA shi ne sunan group in. Sa onnin ta hau duddubawa kamar kullum don bata yarda ta bar sa onnin group in MANYAN MATA bata bu e ba saboda abubuwan da ake gabatarwa a ciki. Hirar da ta ga ana yi ce ta ara mata damuwa a kan wacce take ciki, don dama matan group in basu da aikin da ya wuce banka a sirrin mazajen su da yadda kowacce take samun tarayraya da kulawa a wajen mijin ta wannan shi yake ci wa HUSNA tuwo a warya domin ita a wajen ta babban abu ne tun da ba samu take yi ba abu ne mai wahala shi ya sa ma ko hira ake sai dai ta ja gefe tana karantawa tana mamakin dama akwai irin wa annan mazan a duniya amma mai yasa ita bata yi dace ko gam da katar na samun irin su ba? Tana ala anta hakan da cewa addarar ta ce haka sannan ita bata iya arya ba wato ta zauna tana yabawa ha e da ko a miji a kan kulawar sa gare ta tun da ta san ba samu take yi ba. Ta yi nisa a cikin karanta sa onnin kafin ta ga kowacce tana yin sallama a kan cewa babyn ta yana bu atar kasancewa da ita haka kowa ya watse admin ta kulle gidan ya koma only admin can send message. Hakan ya sa ta sauka ma daga whatsapp in gaba aya ta ajiye watar tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, tagumi ta yi da hannu biyu tana tuna ita sai yaushe ne za ta samu waraka daga wannan damuwar gidan auren nata kowacce mace tana jin da i da kasancewa kusa da mijin ta amma ban da ita abu babu marmari koyaushe cikin wannan matsala shin sai yaushe ne za ta yi ban kwana da damuwar rashin kulawar miji? Ko a haka za ta are rayuwar ta cikin unci. Tun tana zaune har ta fara gyangya i bacci ya soma awon gaba da ita a zaunen ba tare da HAMEED ta ji ko da aran bu ofar ba ne bare har ya zo da haka ta zame ta kwanta wani arawon bacci ya yi gaba da ita. HAMEED kuwa tun daya kar i kayan da ta mi o masa ya ajiye zaunawa ya yi zai tsiyaya sai kawai wayar sa ta yi ara ganin budurwar sa sai ya washe baki ya koma bakin gado ya zauna, katse kiran ya yi don ba ya so ku in ta ya tafi gwara na shi ya tafi duk da shi yake saka mata katin. Kiran ta ya yi tana auka ta fashe da wani kukan shagwa ar da ya sa ya ja filo ya kwanta yana sauraron muryar ta da take rikita duk wata nutsuwar sa. Lalla a ta ya shiga yi ita kuwa ta shiga kashe murya tana mashe murya ta fara masa hirar don akwai wasu ku e da take son kar a daga hannun sa. "Sai in ji duk muryoyin matan duniya amon ta tamkar aran jiniyar an sanda suke idan suna magana, matsawar kika yi magana to fa taki tamkar busar sarewa ce" Ya ce yana wani ko ata tare da zuzutata jin haka sai ta ara zage dantse ta shiga masa yadda suka saba a arshe suka koma video call cikin hirar banza da nuna abin da ya haramta, nan suka raba dare suna haramtacciyar soyayyar da suke ganin more rayuwa ce kuma wayewa ya manta da matarsa ta sunna da take ta faman bibiyar ha in ta ma ya hana ta bayan wanda yake bi in babu abin da za su nuna mata tun da babu abin da ta rage sa da shi sai dai an magana suka ce abincin walama ya fi da Hakan ya sa ya mata al awarurruka da dama bayan ma udan ku in da ta tambaya. Yana kashe wayar ya yi wankan ibada ya yi shame-shame a kan gadon bacci ya yi awon gaba da shi ba tare da ya bi ta kan shayin da HUSNA ta sha wahala wajen dafa masa ba, tare da amfani da magani don samun biyan bu atar ta a matsayin ta na mace mai lafiya kuma wacce bata bibiyar mazan waje ta tsare kanta. Ko sallar asuba bai yi ba don sai wajen bakwai ya tashi shi ma kiran SUMY budurwar sa ne ya tashe shi. aga wayar ya yi yana kallon sunan ta da yake yawo a saman wayar ya ce. 'Kai sai ni HAMEED mai kala-kala mai buhu -buhun an mata' Ya fa a a zuciyar sa yana tashi zaune ya aga kiran. "Haba baby HAMEED ya haka za ka manta da ni kwana aya tal fa ka ce za ka yi" Ta arasa fa a cikin shagwa "Haba SUMY yanzu fa arfe bakwai amma kuma har kin fara orafi kin san dai yau ba za ta wuce ba komin dare a Lagos zan kwana" Wannan furucin ne ya sa ta ji da i suka gaisa cikin soyayya sannan suka yi sallama. Ajiye wayar ya yi tare da tashi ya shiga wanka ya auro alwala sai da ya shiya sannan ya gabatar da sallar asuba, jakar kayan sa da ya dawo da ita jiya ya zazzage a kan gado tare da akko wasu kayan a wardrobe ya shirya a jakar tashi da suk abin da zai bu ata sai kuma arama mai wasu takardu. asa ya sakko da su. HUSNA da take kicin tana ha a break fast sai jin ara gara akwati ta yi gabanta ne ya fa i da sauri ta le o daga kicin in, abin da ta zata ne ta gani wato jakar HAMEED shi kuma yana tsaye tana aura agogo. Tsabar takaici ma ta rasa bakin magana gas ta koma ta kashe don bata ga dalilin dafa abincin ba tun da wanda take yi don shi ba ci yake ba ko na jiya da dare ma bai ci ba. Falon ta fito zuciyar ta babu da i lokacin ya zauna yana waya, jim ka an direban da ya yi wa waya ya shigo ya auki jakar ta fita da su. "Akwai wani abu da kike bu ata a cikin gidan ne ko akwai abin da ya are? Cikin kayan store mene ne babu?" Ya tambaya ha e da akko 500k ya ajiye a gabanta. Hawayen da take ma alewa ne suka surnano mata ta ago ta tsare shi da idanun ta ce "Bana bu atar komai, akwai komai da komai, sai dai abin da na fi bu ata shi ne babu akwai shi amma bani da iko a kan sa" Ta arasa fa a muryar ta tana fallasa asirin zuciyar ta na raunin da ta yi. "Mene ne shi mene ne ya are da har kike so ai babu wani abu da baki da ikon ko nawa ne zan siya miki... "Kai ne HAMEED kai nake bu atata, kai ne bani da iko, sai yaushe za ka zauna da ni a gida? Kullum kai hankalin ka a bussines babu ruwanka da ni da ha ina ka yi wata biyu baka nan amma ka zo ka yi kwana aya ka ce za ka tafi kuma ba tare da ko makwanci ka ha a da ni ba, shin dutse ce ni? Ko ka fi son na fara siyar da mutunci na ga wasu mazan ko kuma in fara holewa da mazan banza a socila midea... "Wace irin magana ce wannan HUSNA sau nawa kike so in maimaita miki gida kike so in dawo in zauna kin sani da cewa kamfanina nake zuwa aiki nake ko zan fasa al'amurana ne saboda ke shin ni mace ne da zan dawo gida in zauna ai zaman gidan sai mata, ko nusarin namiji zan mayar da kaina saboda in da awa mace? Na zo a jiya saboda da ke na dawo yau an mini waya da sassafe ana bu atata a kamfani domin saka hannu a wasu takardu shin sai in bar komai in zauna a gida in ke soyayya shin soyayyar za mu ci?" Ya katse mata hanzari cikin hargagi. Gaba aya sai ta ji ranta ya aci a nata ganin yana sane amma yake take gaskiya. "Shikenan bari na shirya kayana mu tafi tun da ai kana da gida a can" "Babu inda za ki bini wallahi, ke da kika samu ma kina ganina mata nawa ne wata sai ta shekara da shekaru bata sanya mijin a idanun ta ba kuma take zaune amma ke sai rashin ha uri, da kike batun bamu ha a makwanci ba jiya in ce dai a gajiye nake ko bakya duba nisan tafiyar da na yi? Ko cewa aka yi soyayya dakusantar juna ne zaman aure? Abu da zamani ma ya zo ga waya nan sai ka ji muryar mutum" Ya fa a yana tashi tsaye sai wani muzurai yake tamkar ta zagi iyayen sa. "Ni na tafi sai mun yi waya" Ya fa a tana dosar ofar fita. "Allah tsare" Ta furta tana arin danne kukan da ya taho mata. Da amin ya amsa ko a kwalar rigar sa ya fice. Da an gudu ta haura sama ta je jikin window tana kallon sa har mai gadi ya bu e musu get suka fice tana jin haushi da ciwon abin da HAMEED yake mata
Chapter 23 · 0% Book details