← Book details Bonono Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 39

Sashe 20

Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mata wanda ta kasa iya ri e shi. "Auntyyyy" Ta fa a cikin kukan, wanda a zahiri HEEDAYA ta nuna wa Aunty RABEEYA tana kukan rashin ta ne da kewar ta a ba ini kuma tana kukan kishin Aunty RABEEYAR ne. "HEEDAYA tah mene ne wa ya ta a mini ke?" Ta tambaya hankali tashe. "Ba ke ba ce" "Mai na yi kuma?" "Tun jiya ba na samun wayar ki kwana na yi ina tunanin ki na yi kewar ki Aunty shi ne yanzu da na ga asuba ta yi sai na ce bari na kira Ya ABDUL ya ha a ni da ke" Akiyar zuciya Aunty RABEEYA ta sauke sai yanzu ta tabbatar da cewa lafiya sannan ta ara tabbatar da aunar ar uwar ta gare ta tamkar dai ba an uba suke da HEEDAYA ba suna aunar junan su. ",Tuba nake HEEDAYA ni ma na yi cigiyar ki har na gaji kuma bana samun wayar ki" "Matsalar network ne ina Ya ABDUL?" Ta tambaya don ta matsu ta ji ina yake har ta auki wayar kafin ya auka. "Ya fito wanka ne yana shiryawa ne da na ce masa kina kiran wayar sai ya ce ni kike nema" 'Dole sai na tashi tsaye na zage dantse kenan dai har wayar ma ta koma hannun ta? Kuma da ta ce yana shiryawa da alama wanka ya fito to ma in ba wanka na ibadah ba wankan mai za a yi da asubar farin nan?' Ta jefawa kanta tambayar a zuciyar ta. "To Aunty ki gaishe da shi tun da na ni lafiyar ki hankali na ya kwanta" Tana gama fa ar hakan ta datse kiran ba tare sa ta jira cewar Aunty RABEEYA ba, don ba za ta iya jure cigaba da magana da ita ba wata ila ma in aka jima tana iya jin abin da zai fi wannan ona mata rai. Aunty RABEEYA kuwa murmushi ne kwance a saman fuskar ta tana jinjina aunar sa HEEDAYA take mata kuma ita ma haka ne a nata angaren. *BAYAN SATI UKU* Kwance take a akin ta tana ta tunanin mafita don yanzu sai ta yi kwana da kwanaki bata sanya Ya ABDUL a idanun ta ba wanda ta kasa jure hakan. So take a kullum a ce tana tozali da kyakkyawar fuskar sa mai haifar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali. Yau kwana uku kenan rabon da ta saka shi a idanun ta tun ranar da suka zo gaishe da su Abba da daddare shi da Aunty RABEEYA yadda suka murmure suka yi wani kyai daga shi har Aunty RABEEYAR shi zau nuna maka tare da tabbatar maka suna ba juba kulawa kuma suna cikin kwanciyar hankali. Wannan abin da ta gani ya da a rura soyayyar Ya ABDUL a zuciyar ta, kullum abin cigaba yake a maimakon ci baya ga kishin Aunty RABEEYA da take ji yana aruwa tare da nu usar zuciyar ta. Babban abin da yake damun ta ma bai wuce yadda ta ga Ya ABDUL tun da ta yi aure sha uwa ta ragu a tsakanin su idan ba arya idanu da zuciyar ta suka mata ba sai take ganin ma yanzu kamar ya daina son ta da tarairayar ta kawai daga asibitin sa sai matar sa ne ka ai yake ba kulawa sai kuma iyaye. Zuwan ta gidan sa aya wansa sai da ta yi da na sanin zuwa domun mummunan angamon da idanun ta suka mata a tsakanin masoyan biyu. Amma dai yanzu so take ta samarwa kanra mafita. "Hajja ta furta a fili tare da tashi ta auki jakar ta ta saka wayar ta a ciki Umma ta sanar wa za ta je gidan Hajji baki Umma ta ta e ta ce sai ta dawo. Abba kuwa tana fa a masa ya yi murna da hakan jin za ta je gaishe da mahaifiyar sa. Direba ya sauke ta a ofar gidan na Hajja ta shiga da sallama. "Lale marhabin da awata" Hajja ta fa a tana tafa hannu tare da yin dariya a lokaci guda. HEEDAYA ma dariyar ta yi ra samu waje ta zauna suka dasa hira bayan ta bata lemo da bakilawa da alkaki tana ci suna ta a hira. "Hajja wata magana nake son fa a miki ki fa awa Abba ni tsoron fa a masa nake" "Kin samu mijin ne?" Hajja ta tambaya baki washe. "Ba wannan ba ne mijin ma yana nan zuwa in sha Allah lokaci kawai ake jira" "Allah kawo shi amma mene ne" "Amin Aunty RABEEYA ce ta ce mini bata jin da i in je gidan ta in mata kwana biyu to ina tsoron tunkarae Abba da maganar kin san halin sa" "Ayyiri-yiri" Hajja ta carara gu "Kai na fi kowa farin ciki yo ki ce an samu an baba, ai rashin lafiyar mai dalili ce kuma dole a je a taimaka mata da wasu ayyukan kafin cikin ya yi wari " "Wallahi kuwa Hajja kin san ta bata son an aiki suke mata komai" HEEDAYA da maganar cikin ta doke ta duk da ta san maganar ba haka ba ce Hajja ce ta fa a amma sai da ta ji wani iri, sannan ta san wani udurin ta ne zai kai ta gidan don ita Aunty RABEEYA ma bata san da maganar ba. "Ai Abban naku zan kira in masa jawabi" "Barka da yamma Hajja" Abba ya fa a bayan ya aga kiran Hajja. "Barka Bashir ya gida da iyalin" "Kowa lafiya" "Ma sha Allah, Allah yi albarka" "Amin Hajja" "Wannan yarinya RABEEYA ce bata jin da i shi ne ta kira ni a waya rake so HEEDAYA ta je gidan nata ta yi kwana biyu kafin ta ji arfin jikin ta ka san aramin ciki akwai laulayi" Shiru ya yi yana an nazari ya yi mamakin da RABEEYA ta fa i maganar nan kasancewar ta santa da alkunya amma in ya duba cewa Hajja kakar ta ce sai ya ga hakan ba komai ba ne. Amsa mata ya yi da cewa HEEDAYA za ta je. HEEDAYA kuwa ta ji da i sosai don za ta cim ma udurin ta ga kuma komawa kusa da masoyin ta take sanya shi a idanun ta a kullum. Sai magriba ta baro gidan Hajja, bayan isha'i Abba ya kira ta a waya part in sa ta nufa ta same shi a falo yana duba news. "HEEDAYA mai ya samu Aunty naki?" Dumm gabanta ya buga sai dai ta yj gaggawar saita nutsuwar ta ta ce "Abba bata fa a mini ba sai dai ta ce mini kawai in je bata da lafiya" Bai yi magana ba ya shiya latsa waya gabanta sai fa uwa yake bata ankara ba sai jin muryar Aunty RABBEYA ta yi tana cewa "Ina yini Abba" Ta fa a bayan ta yi sallama. Idanu HEEDAYA ta shiga zarawa tana jin fa uwar gabanta yana tsananta muddin aka tabbatarwa da Abba gaskiyar magana ta san kashin ta ya bushe. "Lafiya alau ina ABDULHAKEEM in?" "Yan lafiya Abba" "Madalla!. Ya jikin naki?" Aunty RABEEYA da take kwance kanta a cinyar Ya ABDUL ta ma rasa abin cewa tun da ita dai ta san lafiyar ta alau kuma babu wanda ta cewa bata da lafiya. "Alhamdulillah!." Ta samu kanta da fa a saboda bata son tambayar Abba wanda ya ce bata da lafiya kuma hakan tamkar tuhuma ce. HEEDAYA wata oyayyar ajiyar zuciya ta sauke jin ba a aryata ta ba. "Gobe za ta dawo nan in ai HEEDAYAR har zuwa ki samu ki warware Hajja ai ta kira ni a waya ta bani umarnin in bar HEEDAYA ta je ta taya ki zama kamar yadda kika bu ata baka jin da in jikin ki" Shiru ta yi don zuwa yanzu ta kasa magana ma mamaki ya kashe mata jiki. "To Abba" Ta ce don bata san mai za ta ce ba. Sallama suka yi ya kashe wayar tare da cewa HEEDAYA gobe sai ta je. Da farin ciki ta koma akin ta. Aunty RABEEYA kuwa dakyar ta iri murmushin ya e wanda iyakar sa fatar baki, duk da ta san HEEDAYA anwar ta ce amma ta yi girma ta zo suna da sati uku da tarewa ba za su sake ba idan tana nan amma sai ta danganta hakan da cewa HEEDAYA ce ta kasa jure rashin ta a gidan shi ya sa har ta ullo da wannan batun. MAMAN AFRAH 09013181851 [2/16, 7:55 PM] MOM MASHKUR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/F7TUZezpOWLKYnyTNFuy2Y BONONO (RUFIN OFA DA ARAWO) NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso. *SADAUKARWA* Daga farko har arshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya kai gare ki Allah lullu e rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah fatan alkairi. Daga marubuciyar: iyar igiya an adaidaita sahu Ungozoma ar zaman wanka ara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* PAGE 9 "Hayati mene ne?" Ya tambaya yana ran wafowa yana le en fuskarta da ya ga ta lunshe ido da alamar kamar an fa a mata wani abu da bai mata da i ba sai dai ya san ta da zurfin ciki ba lallai ta bari ma ya fuskanci damuwar ta ba. "HEEDAYA ce ta kasa jure rashi na shi ne ta cewa Abba za ta zo ta mana kwana biyu" Fuska ya yamutsa cike da mamaki yana kallon idanun ta da har lokacin suke a rufe sai gashin idanun da suke zare-zare sun rufe saman idanun. "HEEDAYA ce za ta zo nan ta yi kwana biyu?" "Eh" Ta fa a cikin sanyin murya tare da tattaro jarumta a jikin ta ta tashi zaune tana an kallon cikin wayar idanun sa ta sakar masa murmushin nan da yake tafiya da shi. "Ko baka so ta zo?" Ta fa a tana rausayar da kai tare da an jujjuya idanun ta. Dimm ya an yi shi dai ya san RABEEYA da kunya iya su ma sai yana an dagewa wajen ganin ta sake jiki da shi saboda matsananciyar kunyar da take da ita duk da kunyar tata tana birge, shi amma kuma dai ya san matsawar HEEDAYA za ta dawo ba lallai take iya nuna masa so da auna ha e da kulawa ba saboda alkunya
Chapter 20 · 0% Book details