← Book details Bonono Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 39

Sashe 25

Bonono Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta koma ciki domin kuwa jini ne ya allewa Aunty RABEEYA an yj ta arin tsayar da shi sai dai abu ya ci tura don ana ara wani, wani yana fita. Tuni hankalin kowa ya tashi musamman Ya ABDUL da ya fi kowa shiga tashin hankali musamman da ya ga Aunty RABEEYA ta ri e hannun sa cikin galabaita tana fa in ya yafe mata tare da bar masa wasiyyar kulawa da jaririyar da ta bari don gaba aya ta sare da mutuwa za ta yi!. Kuka kawai yake tamkar mace tamkar ba likita ba gaba aya ya fita hayyacin sa ganin hatta magana ta gagare ta shi kuma ji yake tamkar dai idan har ajalin ne zai saukar mata gwara mutuwa ta auke su tare son har ya fara tunanin yadda zai rayu ba tare da RABEEYA ba a wannan duniyar!. HEEDAYA wacce da take jin tamkar ta yi wa Aunty RABEEYA addu'ar mutuwa wajen haihuwa amma ganin halin da take ciki sai ta ji zuciyarta ta yi rauni ta ji tana tausaya mata kai har ma ta ji da za ta warke da ta ha ura da aure mata miji sai dai kash! Abin da Allah ya rubutu babu mai gogewa a wannan lokacin ne rai ya yi halin sa Aunty RABEEYA ta amsa kiran mahalicci tana mai ambaton kalmar shahada dakyar don sai dai ka gane furucin bakin ta amma ba a jin sauti ko ka an. Allahu akbar! Rai ba on duniya. Ya ABDUL sai da aka rirri e shi Abba da Daddy suna ta bashi baki amma ina!. Sunan ta kawai yake ambato hatta su Abba sai da suka zubar masa da hawaye ri e yake da jaririyar yana ta kuka tamkar aramin yaro, HEEDAYA ma tausayin masoyin ta da kuma rabuwa da Auntyn ta mai aunar ta tsakani da Allah ya sa ta fashe da kuka tare da rungume Ya ABDUL da babyn suna kukan tare. Kwanan keso ta yi ana ta nema mata gafara ga mahalicci kamar yadda annbin rahma S.A.W ya ce a nemawa mamaci gafara. Da yake dama gidan Abba aka kai ta, bayan an shirya ta aka sallace ta tare da tafiya da ita makwancin ta!. Ya ABDUL wanda Allah ya dasawa ha urin danne zuciyar sa bisa ga wannan babban rashin da ya yi shi ne wanda ya sanyata a kabarin ta. *A gafarce ni da mutuwar Aunty RABEEYA haka labarin namu ya zo ne, sannan ita dama mutuwa a har kullum tana zuwa ne ba tare da an shirya ba. Sai dai ftn Allah sa mu cika sa imani ya mana kyakkyawan arshe.* MAMAN AFRAH 09013181851 [2/16, 7:55 PM] MOM MASHKUR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/F7TUZezpOWLKYnyTNFuy2Y BONONO (RUFIN OFA DA ARAWO) NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso. *SADAUKARWA* Daga farko har arshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya kai gare ki Allah lullu e rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah fatan alkairi. Daga marubuciyar: iyar igiya an adaidaita sahu Ungozoma ar zaman wanka ara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* PAGE 11 *MARYAMA* Tunanin inda za ta nufa ta gujewa ha uwa da mai muryar da ta ji yana jefo tambayar waye a nan. Don a halin da take ciki yanzu kowa ma tsoron sa take tun da ita bata da kowa, amma ina! Babu wata hanya da za ta bi ta fita sai inda ta shigo kuma ta nan ne take jin muryar mai maganar yana nufowa, sannan matsawar ta motsa ta ce za ta koma wani akin ta uya to tabbas zai iya cim mata don ya riga da ya zo dab. Hasken fitilar da ya dalle mata idanu ne ya sa ta yi tsuru-tsuru tamkar an tsamo era daga ruwa. "Wace ce ke? Kuma kukan mai kike?" Tambayar da ya guntso ya fesar mata ya sa gudun numfashin ta aruwa gaba aya ta ru e ta rasa bakin magana sai wani kukan da yake taso mata, a ganin ta ta samu ma oya amma ashe asirin ta zai tonu. "Na ce wace ce ke?" Ko aljana ce ke?" Ya ara jefo mini tambayar a zafafe. Da sauri na shiga girgiza kai ina cewa. "Mutum ce ni wallahi ba aljana ba ce" "Me kike a nan?" "Tafiya nake dare ya mini shi ne na zauna kafin gari ya waye in cigaba da tafiya" Bai ce komai ba ya shiga zagaya ta yana ara haske ta, tare da haske kayan nata. "Shi ne baki zauna a cikin gari ba, ko kin shiga wani gida kin nemi alfarma kika zo dokar daji cikin tsohon ginin nan da bashi da tsaro kika zauna bakya tsoron wani abu ya cutar da ke? Ko bakya tsoron matsayin ki na mace wasu mazan su far miki?" Kai ta sunkuyar hawaye suna zuba tun da ta tabbata maganar da yake yi ita babu wannan abin a ranta tun da ga shi ni cikin wata baiwa ta samu ciki a jikin ta ba tare da namiji ya kusance ta ba to gudun mai za ta yi?. "Daga ina kike?" Shiru ta yi tana tunanin fa a masa daga inda nake a ganin ta ba abin da ya shafe shi ba ne sannan daga ganin sa bai yi kama da mutumin auye ba don sai yanzu ta lura ma ashe ba fitila ba ce a hannun sa waya ce. "Suna na HAFEEZ ni mutumin garin Dutse ne ina zaune da Kakata a can sannan ni ma'aikaci ne a wannan asibitin na auyan nan, wannan gidan shi ne wanda nake zaune a ciki, tun da kin baro cikin gari ki zo ki shiga akwai aki ki yarda da ni ba zan cutar da ke ba kuma ki saka a ranki cewa Allah zai kare ki ko da na yi niyyar cutar da ke da safe sai ki tafi inda kika nufa" Cewar HAFEEZ mutum mai tausayi ha e da ri o da addini mutum ne da ya tsani zina da kuma duk wani aikin alfasha duk da kuwa bashi da aure. Idanu ta aga ta shiga kallon fuskar sa ganin ya haske mata fuskar tashi alamun ta gan shi. Ba i ne ba sosai ba irin ba in kyau nan, dogo ne sosai yana da an jiki don ba za a kira shi rammamme ba yana da fa irji duguwar fuska da dogon hanci ha e da kwantaccen gashin kansa da yake kwance luf kamar na mutanen asar indiya, sajen sa da ake kira da kwata million ya ara awata fuskar. oyayyar ajiyar zuciya ta sauke amma har cikin ranta sai ta ji hankalin ta ya kwanta da shi har zuciyar ta take ji ba zai cutar da ita ba!. Ba tare da ta yi magana ba ta auki kayan nata ta rungume, murmushi ya saki ganin kamar dai bata saki jiki da shi ba ya rasa ma daga ina take yanayin ta ya nuna masa tamkar tana cikin matsananciyar damuwa amma bata son ta fa a. A gaba yake tana bin sa a baya har suka arasa gidan ya bu ofar ya shiga hasken sola da ya haske gidan sannan gidan share al kamar akwai mace a ciki ginin siminti ne tamkar ba a auye da dama haka ake idan an gina asibiti sai a gina gidan ma'aikatan a gidan. Ciki da falo ne sai wasu akunan guda uku a jere sai bayi da kuma kicin. akin da ya nuna mata ta shiga ta zauna babu komai sai aramar katifa. Da sallama ya shiga akin. "Akwai abin da kike bu ata?" "Ina so zan yi sallah" Shiru ya yi yana bin ta da kallo yanayin ta babu nutsuwa akwai alamar damuwa, sannan kana ganinta ka san tana jin yunwa amma kuma sai ta ce sallah, ta birge shi sosai kasancewar yana lura da wasu matan auye basu damu da sallah ba sannan ma ya lura ita kamar ba auye ba amma suturar jikin ta ta yamushe da yawa. "Ga ban aki can a waje akwai ruwa" Yana fa ar hakan ya juya ya fita. Fitowa ta yi ta shiga ban akin wanke yake al sai amshi ma yake tsarki ta yi ta yi alwala ta fito tana komawa ta ga sallaya a ajiye da alama shi ya kai mata sallolin ta jero ta gama ta zauna tana ta jerowa Baffan ta addu'ar samun gafara ta gama ta shafa sai bata cire hannuwan daga fuskarta ba ta bari a haka hawayen tunanin Baffan ta yana zubowa tana ji a ranta bata san ranar da za ta daina kukan rashin sa ba gaskiya mutuwar Baffa tabo ne a zuciyar ta wanda ba zai ta a kankaruwa ba har abada!. Da sallama ya shiga bayan ta amsa, plate ya shigo da shi a rufe ya ajiye da cibi (Fork) A kan plate in ya ce "Ki ci abinci" "Na oshi" Da kallo ya bi ta sai lokacin ya lura da lema a fuskar ta kuma idanun jawur da alama kuka ta sake yi. Shiru ya yi yana nazarin ta sai ya ce "Amma akwai yunwa a tare da ke ba zan cutar da ke ba, wal lahi ban zuba komai a ciki ba, indomie ne na dafa miki" "Ba zan iya ci ba" "Baki isa ba ni babu wanda ya isa in ata lokaci na in girka abu saboda shi ya ce ba zai ci ba" Ya fa a cikin fa a-fa a don ya lura akwai yunwar a jikin ta cin ne kawai ba za ta yi ba. Yana gama fa ar haka ya zauna tare da bu e plate in ya ora fork in a kan indomien da take ta turiri ta sha attaruhu da albasa. auki ki ci" Ya ce cikin bada umarni muryar sa babu alamun wasa. Gaba aya yadda ya yi maganar sai ya bata tsoro duk sai ta ru e ta ma rasa mai za ta yi. "Ki auka ki ci na ce" Hannun ta har karkarwa yake ta au fork in ta auki indomie in ta nufi bakin ta sai dai tuno da Baffan ta sai kawai ta rushe da kuka. Jikin sa ne ya yi sanyi ganin tana kuka ko abincin bata kai baki ba. "Mene ne damuwar
Chapter 25 · 0% Book details