← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 88

Sashe 87

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake jeho masa tambayar Akai wadda ta Saka BB zamewa daga cikin Taron Yana hada zufa sbd da alama abubuwa sun fita a Lokacinda basa tsammani.

"Alh lameenu seelah shin da gaske ne Kaine kake bibiyar rayuwar 'yar Omar jaden Ameeenatou jden wanda ya hakan ne ya kawo rabuwar familyn biyu,
Sbd ankama maaikatan asibitin datai zama wainda suka bada tabbacin Kaine kake Basu alluran d suke mata har haukanta tayi tsanani,
Sannan Audio na maganarka da Dr Dee wanda kuke maganar yaci gaba da aikin dayake Yi karshe yanzu an tabbatarda kashesa Akai ba mutuwar da ake tinanin yayi bace,
Meye ne gaskiyar wannan maganganun??
Shin gaskia ne ko kanada abinda zaka fada Akai??

Jiri ne yafara diban lameenun sbd haka securities ne take suka fara korar Yan jaridar Dan shigar dashi gida.

Yana shiga da sauri 'yarsa daya data rage masa siyam tayi saurin taresa tana karesa daga hotinansu da ake dauka tana riqe hawayenta sbd radadin da zuciyarta ke make harya wuce abinda zuciyarta zata iya dauka.

Suna shiga Kai tsaye gawar datake shimfide a harabar gidan ya dosa kafafunsa na kasa daukansa kaman zai zauce yake Jin kansa da kwakwalwansa.

Kafin ya iso kan gawar Mam dayake tsaye tareda duka familyn SEELAHs din ya Bude gawar wadda ta tashi daga Aliyah ta koma wata halittar daban.

Duk Mai imanin daya kalli gawar Aliyan sai yaji firgita da tsananin tsoron Allah ya kamasa tareda hawayen tausayi me tsananin gaske Dan haka kallo daya Ayesha da siyam sukaiwa gawar suka zube qasa gwiwoyinsu na sarewa Cikin tsananin tashin hankali da Kuka Mai tsananin gaske.

Mum Sarat kuwa kallo daya tayiwa gawar ta tabbatarda Aliyah ce Dan haka bugawa daya zuciyarta tayi take zuciyarta ta buga a gurin.

Lameenu ma zuciyarsa kusan bugawan tayi sbd yanke jiki yayi ya Fadi a gurin baya ganin komai bayajin komai.

Take Mam ya ce a daukesa ayi Ciki dashi Cikin bayyanarda tsananin damuwa da tashin hankalinsa.

Mum Sarat kuwa Saida aka tabata aka gane zuciyarta ta buga a gurin.

Da sauri aka Nemo likita wanda ya iso Mansion din Yana dubata ya tabbatar musu da ta rasu.

Take gabaki daya mansion din suka qarasa shigewa Cikin mummunan tashin hankalin daya girgixa mutane.

Lameenu take ya fice hayyacinsa ya koma abin tausayi sbd numfashin da baya iya ja ma da kansa saida oxygen wanda oxygen din kansa ba lafiyayye bane sbd Mam so yake ya gama da case din lameenu kwata kwata kafin dawowan Jamaal yasan shine ya qara daukan Wani ran.

Dr Aleena da familyn jdens gabaki dayansu Saida suka halarto SEELAHs mansion din sbd janazah din mum Sarah da Aliyah wanda aka yanke shawaran Yi ba sai an kwana ba.

Lameenu yanaji Yana Gani daga kwance Mam ya Saka Akai janazah din yarsa dayafi so fiyeda komai tareda matarsa batareda shi ba
wanda yayi ajalinsu shine yake karban gaisuwan rasuwarsu.

Tashin hankalin da SEELAHs suke Ciki ya Saka Yan jarida dakatawa sbd Babu wanda Bai girgixa da wannan rashin daya samesu lokaci daya ba da Kuma yanda Akai Aliyah take asibitin batareda sanin iyayenta ba.

Zuwa dare BB ya gama hada duk abinda zai buqata Dan barin qasar gabaki daya ya bace sbd yasan dole akwai abinda yake faruwa a boye Dan kuwa Mam yasan Wani abin da lameenu yayi ya masa hakan Dan ko zai mutu ya dawo yasan wannan hukuncin Mam ne yakewa lam kisan mummuqe.

Bullet dayasan Shirin BB tini ya sanarwa Mam
Mam ya sanar dashi abinda yakeso.

Karfe 9 na dare bayan Yan zaman gaisuwan duka sun watse mansions din sunyi tsit motar bullet ta Sako Kai Cikin mansion din lameenu yayi parking ya wuce ciki sbd securities basa hanasu sunsan matsayinsu sosai a gurin uwayen gidan.

Office din lameenu ya isa ya Bude sbd Mam daya fada masa code.

Yana Cikin office din karfe dayan dare ta buga koina ya sake daukan shiru Dan haka ya fito ya nufo motarsa ya dauko BB Dake kwance a Ciki a sume.

Cikin office din ya kawosa tareda zaune dashi a kujera ya daure hannuwansa.

Wayarsa ya fidda zai kira Mam sai ga Mam din ya Bude kofar office din ya shigo Mum Atee daya Saka ta biyosa tana banyansa suka shigo.

Rufe kofar yayi bayan sun shigo
Kallan bullet yayi

take bullet yasan abinda zaiyi ya juya ya fice.

Kai tsaye sama ya nufa inda bedroom din lameenu yake kwance kaman Wanda yayi shekara ashirin Yana jinya.

Babu Imani ko kadan a ran bullet ya daukesa cak bayan ya fizge oxygen dayake hancinsa ya sauko dashi.

Duka Mansion din Babu kowa daga lameenu din sai siyam sai Yan uwan mum Sarah su biyu Dake kusa sauran duka Suna nesa Basu isoba sai gobe Dan haka duk sunyi bacci Banda Siyam data kasa ko kwanciya sbd quncin datake Ciki
Dan haka tasowa ma tayi Dan tafiya sake dubo mahaifinta.
#MAMUH
[29/05, 10:08 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
126
Tana fitowa palon qasa Taga wucewan Bullet da Dad dinta dauke a kafada Dan haka bayansa Yana tabi da sauri tana kokarin Kiran sunansa ya Bude kofar office din daddyn ya shige.

Wanda ta Gani a Ciki ne ya sakata Sako Kai da sauri sbd sanyin dataji na ganin Dad Mam.

Shigowanta yayi daidai da budewan Idanuwan BB Dana daddynta da aka jefar qasa.

Ambatar sunan Mam tayi ahankali Cikin matsanancin mamaki da tsoro.

Mum Atee ma mummunan tsoron ne ya rufeta jikinta na tsananta rawar gaske tareda tashin hankali mafi Muni sbd tsoron Mam daya taso mata.

Mam kuwa da bullet har da mum Atee din juyowa sukai suka Kalli Siyam.

Mam ya rinte Ido ya Bude sbd yaso barinta Amma Kuma hakan yanzu beme yiyuwa bane.

Fizgota bullet yayi ya jefa kan mahaifinta wanda ya tashi zaune daqyar Yana Neman numfashin ja Cikin tsananin azabar gaske ya Bude Idanuwansa da basa Gani sosai Yana kallan Mam Idanuwansa na gangarowa da hawayen radadin dayake ji a zuciyarsa sbd Tino su kasim da Jameel Dan Bai dauka yanda suka dauko ransu ba haka Shima Mam zai dauki nasa.

Mam baida lokacin batawa BB ya fara kalla Yana hango yanda bullet yayi masa bayanin ya samu labarin abinda sukaiwa Haroon a gaban idon yaron BB din.

BB na ganin hakan Idanuwansa sukai jajir sbd yasan me hakan ke nufi,
Mam ya gama sanin komai
Kuma bazai taba barwa Allah ba Dan haka rintse Idanuwansa yayi gashi anriga an masa alluran da bazai taba iya motsawaba ta Yan tiyata.

Siyam Mam ya kalla wadda jikinta yake tsananin rawa tana qanqame daddynta wanda Shima hawayen yakeyi Yana kallan Mam daqyar ya iya Bude Baki Cikin azabar Ciwo da rashin kuzari yace

"Mamman Dan Allah kabar Siyam,
Banda kowa sai ita a yanzu kabarta ko addua zata ringa mun tinda Banda Mai tinawa Dani bare adduar,
Yarinya Dan Allah kabarta ta samu Gina rayuwarta duk da batada kowa Amma Dan Allah Mam Kabar Siyam.....Ina rokonta ka dauki tawa rayuwar data gama Aiki Amma kabar Siyam"

Wasu hawaye ne masu radadin gaske suka gangaro masa Yana Jin radadin rashin Aliyah da Mum Sarat da Kuma tausayin 'yarsa da batada haqqin komai.

Bullet ne ya miqa hannu zai fizgo Siyam din lameenu ya rintse Idanuwansa Kuka mara sauti me Ciwo Yana kufce masa Amma baida abinyi sbd ko hannunsa baya iya dagawa.

Syringe Mam ya karba daga hannun bullet ya daga a gaban idon lameenu ya sokawa Siyam wadda ta qanqame daddynta zafafan hawayen na gangaro mata Idanuwanta a Bude tana kallan daddyn har Mam ya gama tsiyaye ruwan cikinsa gabaki daya a jikinta take jikinta ya fara saki ta sake daddynta ta zube a gurin har lokacin Idanuwanta a Bude sedai jini daya fara biyo hancinta Yana fitowa.

Lameenu rintse Idanuwansa yayi zuciyarsa na kokarin Dena bugawa kaman yanda zuciyar Mum Atee take Dena bugawa sbd tsananin tsoro da tashin hankali mafi Muni.

BB ma jijjiga jikinsa ke farawa yanason Bude Baki Amma ba dama kafin ya motsa Mam ya daga wata mummunan scroll driver me tsini ya Tura masa daga qasan wuyansa zuwa zamansa ta fito ta hancinsa take jininsa yayi feshi a gurin Yana wata irin jijjiga ransa na fita.

Mayafin jikin Mum Atee data Sako ya fizgo Yana goge hannunsa sbd wannan shine karo na biyi dayayi kisar jini daga tasu kasim sai wannan,

Kwata kwata baya taba jinin kowa
Baya aikinsa ta hakan a saukake Ciki qazantacciyar tsafta yake aikinsa
Jinin BB shine jini na biyun da hannunsa ya taba.

Ko daya gama goge hannunsa mum Atee takai qasa tana Wani irin Kuka me qarfin gaske da tsananin Dana sani tana rokonsa akan ya yafe mata tana tonawa kanta asiri har Wanda Bai saniba akan abinda sukaiwa Haroon da yanda ta juyar da rayuwarsa zuwa mahaukacin gaske da Kuma karshen yanda lameenu ya sama aka kashesa da mota bayan yasan Yana tareda Omar a ranar.

Bata game bayaninta ba Bullet ya soka mata syringe din hannunsa ya sakar mata alluran datafi wadda sukaiwa Aliyah Muni take ta fasa fizga tana fidda jinin ta hanci da Baki.

Lameenu rintse Idanuwansa yayi yanajin abinda Bai taba sanin hakan yake ba sai ayau da a gabansa aka illata rayuwar 'yarsa.

Tabbas su kasim sun huta da suka tafiyarsu Tim farkon tashin hankalin batareda sun shedar da wannan ranar ba da suke gama kashe junansu akan dukiyar da haryanzu basu sameta ba sun Kuma lalata duniyarsu da lahirarsu akanta
Gashi shi dai yanzu zai barta a Cikin radadi da baqin Cikin zuciya tareda Dana sani mara amfani.

Daqyar ya Bude jajayen Idanuwansa numfashinsa na kokarin tsayawa sbd rashin oxygen ya kalli Mam Bai iya furta komai ba sbd Babu abinda zai iya fada din.

Alluran da Mam ya dago daga hannunsa ya Saka shi lumshe Idanuwansa Yana ganin mutuwar kasim da Jameel a Idanuwansa tareda Jin mummunan danasanin da batada amfani da tsanar kansa akan shine ya fara karya alkwarin amintar SEELAHs sbd shine ya fara kashewa kafin Mam din
Dan haka shima yau layin ya zagayo kansa.

Saukan syringe din yaji a Cikin tsokar wuyansa ruwan na shigewa ahankali har suka gama shigewa.
Chapter 87 · 0% Book details