← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 88

Sashe 40

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

***************
Rayuwar su Babbah yanzu ta rufin asiri ce sbd Basuda Wani abin riqe Kai sai Yan dubaru da aikin da Hafiz yayi ya samo kudi,

Lallaba rayuwarsu sukeyi duk da Babu ranar da Babbah Baya tsinewa hada zuria da jinin SEELAHs sbd sune sanadin lalacewan ahalinsa Dake zaune cikin zaman lafiya da Kwanciyar hankali gasu yanzu sun qare kullum a sauyin guri yake da boyo,

Yariga ya dauki kaddarar rashin Abdul sbd yasan shikam ya huta inshallah Yana cikin rahamar Allah Amma a duk lokacinda ya Kalli yanda suke fama da Ameenatou idan rikicin ciwonta ya tashi akan sai ankaita gurin Jamaal ko sister Ashley sai yaji ya sake tsanar duka wanda yake ahanlin seelahs.

Sunsha fama da tashin hankali da damuwa akan Ameenatou da ciwonta farko farkon dawowansu da ita har suka Saba suka fahimci abubuwan datake so da Wanda bataso,

Kullum duk tsanani duk rintsi sai Hafiz ya shigo mata da kayan tea da fruits sbd sune abinda take ci Sam sam Bata Wani son abinci sai an hada da dubaru da Kiran Ashley take ci..

Duk Wani tsananin so da kulawan da suke Bata a abaya a yanzu data koma haka sai suka ninku sbd ko quda da sunada hali bazasu so ya sauka a jikinta ba,

Tattalinta sukeyi tareda tsananta nema Dan hada abinda zasu samar mata lafiya,
Hafiz aiki yakeyi tuquru tareda Neman Aiki da takardunsa,hakama Babbah ya sake ya qara samun lafiya sosai yafara fita Neman Shima.

An dauki lokaci Dan haka itama Ameenatou din tini ta sake a cikinsu hankakinta ya kwanta Kuma ahankali ahankali sai tana samun sauki kanta na sakewa harma kaman tana tinawa Kokuma kokarin Tina abubuwa da dama na rayuwarta.

Hafiz ya Dade komawa mutum me Tsananin zuciya da son 'yanta Kai,
Abinda ya samesu ya tabasa sosai tareda sauya masa rayuwa,

Rayuwa yakeson shi da iyayensa da yar uwarsa suyi kaman kowa,
Rayuwa yakeson suyi ta yanci da tsayawa Kai,
Rayuwa yakeson suyi batareda tsoron kowaba ko shakkar kowane lokaci Wani abu zai iya samunsa,

Bazai taba iya yadda suci gaba da boyo suna yawon garuruwaba sbd suna tsoron rasa rayuwarsu ko Kuma 'yar uwarsa,

Radadi da zafin Hakan sune suke cinsa Akoda yaushe dasu yake kwana dasu yake tashi,

Idan Yanason bawa rayuwarsu cikakkiyar kariya da yanci to dole ya Tara nasa abin duniyar Shima Dan haka bayaji Baya Gani bayan aiki da Neman kudi kawai.

*******Dadah tinda suke indai zataiwa Ameenatou wanka a zaune take zaunar da ita a kujera da pant da halfvest a jikinta take mata wankan Dan haka Bata taba lura da yanda cikinta yake ba sai yau.

Zaunar da ita tayi taje ta dauko ruwan wankan tana ajiyewa Ameenatou ta zabura da sauri ta miqe tsaye daga ita sai halfvest da wando sbd kyankyason Dayayo cikinta daga karkashin bucket din.

Cikinta ne ya fito sosai fes dashi Wanda duk dare ta kwanta Bata iya Kwanciya daidai ya ringa juyi kenan tana jujjuyawa sbd rashin Jin dadinsa a jikinta Amma batasan me zatace ba Dan batama San wani abu a jikinta ba na Wani ran.

Makancewa Dadah take Neman yi gurin Bude ido da kafawa cikin Ameenatou idanuwanta gabanta yayi mummunan faduwan da sauran kiris paralyze ya kamata.

Sake yankewa gabanta yayi ya Fadi tana matsowa gurin Ameenatou din idonta a cikin Wanda yafara tsayi ya fito sosai.

"Innalillahi wainna ilaihirrajiun"

Hannunta dayayi mata wani irin nauyi sbd tashin hankali ta daga ta nufi cikin ta Dora Akai tareda dannawa kadan tajisa da taurin gaske,

Kafin ta cire hannunta Akai Ameenatou ta Dora hannunta akan na Dadah din tana cewa

"Babyn Ameenatou inji Ashley,
Ashley tace Babyn Ameenatou kada kowa ya tabasa.......

Yanke jiki Dadah tayi a bakin toilet din tsakar gidan ta zube qasa zaune jikinta na wata irin rawa sosai zuciyarta na tsananin bugun datake Neman bugawa.

Bakin na rawa tace

"Me kikace?

Zaunawa a kujeran wankanta tayi tana cewa

"Ashley tace baby ne anan Kuma babyn Ameenatou ne"

Hannu Dadah ta Dora Akai tanason fasa ihun tashin hankali Amma Kuma batasan ma me zata fada a cikin ihun ba.

Babbah Baya gidan hakama Hafiz bare a taimaketa da radadin dayake Neman illata ganinta da Jinta,

Rarrafawa tayi ta dafa ta tashi sbd kasa yadda dataji tanayi da wannan mugun fata da mafarkin.

Hannuwanta na rawa jikinta Babu karfi ko kadan ta danne abinda take ji Akai wankan tana kasa kallan cikin Dan tsoro ma takeji fatanta zancen rashin hankalin Ameenatou dinne kawai take maganar baby a cikinta duk da girman cikin ma ga fada Hakan Amma bazata iya yadda cikin mutum na haihuwa ne a jikin 'yar yarinyarsu ba da batama cikin hankalin kanta.

Kwata kwata ba nutsuwa ko Kwanciyar hankali ko Daya a tareda dadah suka fito ta shiryata cikin doguwar rigar material da Hafiz ya siyo mata su a kayan sawa tinda batada wasu kayan a tareda su.

Duk yanda taso dafa abincin Rana kasawa Dadah tayi sbd zazzabi ne na tashin hankali ya rufeta take,
Tea kawai ta hadawa Ameenatou din ta Bata tana sake zurfafa a tinanin abubuwa da dama da Suka sauya daga Ameenatou din Daya kamata ace sun gane Amma sbd ganin rayuwarta ma ta sauya gaba Daya ya Sakasu daukan duka akan kanta ne Daya juya.

Karfe Hudu na yamma Babbah ya dawo gidan dauke da ledan fruits Daya siyo a hanyarsa ta dawowa daga inda ya samu Yana Dan shiga kasuwancin dabbobin Daya Saba.

Zazzabin Daya tarar da Dadah ya Sakasa mamaki Yana zaunawa yace

"To lafiya dai kuwa?
Meya sameki ne tinda lafiya kalau muka fita muka barki kina aikin gidan,
Ko cizon sauro ne? To Amma Kuma ai bamada Wani sauro tinda Akai akai anawa gidan feshi sbd yar buduwata da banason sauro ya ciza"

Ajiyan zuciya ta sauke idanuwanta sai a lokacin suka cika da wasu hawaye masu tsananin radadi da ciwo ta dago ta Kalli Ameenatoun Dake kwance tana bacci ita Kuma tanai mata fita.

Ajiyan zuciya ta sake saukewa a Karo na uku kafin ta dago ta Kalli Babbah Daya zuba mata ido Yana jiran abinda zata fada Dan bayason delay a gurin Bada labari ko Fadar Abu.

Sanyi jikinta yayi hakama muryanta tace

"Babbah Ameenatou ciki ne a jikinta ga dukkanin alama Dan ni dai na kasa tabbatarwa a rude nake Kuma itama da kanta tace baby a cikin Ameenatou....."

Kallan Ameenatou din yayi kafin ya juyo da kallansa kan Dadah yace

"Meyasa haryanxu kin kasa sabawa da yanayin tashin lafiyanta,
Kinsan yanzu batasan me take fada ba batasan Menene wannan ba bare wancan."

Girgiza Kai dadah tayi idanuwanta na sake cikowa da Hawayen da suka gangaro mata tace

"Ciki Kam akwaisa da alama Dan gashinan a bayyane harya fito Dan kuwa da alama zaiyi wata hudu komai fiye,
Kullum saitace cikin Ameenatou tsalle sosai na dauka idan tana Jin yunwa take Fadar Hakan shiyasa duk ta fada saina Bata Wani abin taci da alama Motsi ne yake mata.......

Ajiye kankanar Daya dauka zai Sha Babbah yayi Yana sake kallan Ameenatou din dakyau ya dawo da kallansa kan Dadah idanuwansa na sauyawa yace

"Wai maganar me kikeyi??
Cikin haihuwa ko me??

Gyada Kai tayi hawayenta na sake gangarowa.

"Ni bangansa ba to" ya fada muryansa na sarqewa.

"Nima wlh bantaba Gani ba sai yau Amma wlh Babbah naga ciki me girma Kam ni Amma na kasa yadda da cikin mutum ne a jikinta,
Nidai muje asibiti a duba mana Dan jinina Neman Hawa yakeyi da wannan babban tashin hankalin dayafi kowanne dayake Shirin bayyanar mana"

Wani azababben zufan tashin hankali ne ya fesowa Babbah lokaci Daya a ko Ina jikinsa,
Hannunsa dayake Dan rawa yakai goshinsa ya share tareda qurawa Ameenatou idanuwansa dasuka qarasa sauyawa gaba Daya suna yin wani Jan tashin hankali da masifa.

Kaman tasan abinda ake ciki ta juya Kwanciyarta ahankali zuwa Dayan bangaren Wanda Hakan ya bayyanarda cikin sosai take Babbah ya sarqe da yawun bakinsa da suka kasa wucewa sbd muguwar bushewan da maqoshinsa yayi take.

"Innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Badai ciki ba wannan sedai koshi ne yayi mata yawa Amma tayaya zaa samu ciki a jikin yarinyar datake budurwa Babu miji,Babu hankali Kuma tana can killace asibitin da baama barin kowa shiga sai dole.

Wurgi yayi da kayan gabansa Yana miqewa tsaye jikinsa na sake jiqewa da zufa ya Saka takarmansa Yana cewa

"Shiryo asibiti zamu yanzu basai gobe ba"

Miqewa dadah tayi tareda shiga daki ta shirya ta fito ta dauko hijab ta tayarda Ameenatou ta Saka mata suna kokarin fitowa Hafiz ya dawo ya tsaya Yana kallansu cikin mamaki Amma Kuma ganin Babbah a mummunan halinda Bai taba ganinsa ba a ciki ya Sakasa Maida kallansa kan Dadah da jikinta yake a mace gaba Daya Babu kuzarin komai,

Ameenatou ya kalla itama yaga ita baccinta ne ma Bai isheta ba fuskanta duk a daure sedai itama a kasalance take.

Magana zaiyi Babbah ya dakatar dashi ta hanyar cewa suje kawai.

Ciki ya shiga ya ajiye ledan siyayyar kayan tea da wasu abubuwan Daya siyo ya fito ya rufe gidan ya biyo bayansu zucuyarsa Shima tini tayi nauyi ta shiga Wani mummunan damuwa Yana fatan ba wani abin ne ya samu Ameenatou dinba Dan zuciyarsa bazata iya dauka ba Dan yanzu haka duka nemansa akanta ne sbd ita yakeson yaga sun samu sauyin rayuwa itada iyayensu.
Chapter 40 · 0% Book details