← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 88

Sashe 31

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*************
Hafiz ne da tafiyarsa ta sauya sanadiyar accident dinsu yake riqe da Babbah din Wanda shima dai tafiyar ya sauya Amma shi hadda dadewa a kwance Yana jinya sosai qari Kuma ya farfado Bai Jira ya warke sosai ba ya daga hankalin Hafiz da Dadah akan duk inda Ameenatou take ita kadai yake son Gani yakuma dawo da abarsa a hannunsa tinda Haroon ya rasu hakama Omar baa San inda yake Yana jinya Rai hannun Allah ba gwara abasa 'yarsa kawai.

Hafiz ne ya sanar dashi labarin Ameenatou na ta samu matsalan kwakwalwa tana asibitin mahaukata Wanda Hakan ne ma ya sakashi barinta anan kafin su samu kansu su dawo su tafi da itan tin farko,

Babbah Jin Hakan ya rikice musu Saida suka sake komawa asibiti kusan satinsu Daya suna sake jinyarsa kafin ya matsa aka sallamesu Babu abinda yake son ji da gani bayan 'yar budurwansa,

Yayi kukan da Bai taba yinsa ba tin bayan rasuwar Aminatunsa sai yanzu da 'yarta ta samu kanta acikin wannan kaddarar ta fitowa daga tsatson Yan ta'addan da Babu ko sunan Allah a ransu bare tsoronsa,

Yayi baqin cikin hada zuria da SEELAHs Dan kuwa hada jini ne dasu ya kawo Hakan,
Omar daban yake acikinsu Kuma har cikin ransa yanzu yake kaunarsa sedai bayan shi kaf yanzu Babu Wanda zai iya kalla a siffar musulmi ma a cikin dangin,

Haroon ne jinin Mam Kuma ya rasu Dan haka su ayanzu babu abinda zai sake hadasa ko zaman gari Daya dasu harshi har kaf duka ahanlinsa har abada inshallah Dan haka ya daga hankalin a kawosa ya duba yarsa a Basa abarsa suje inda suke su nema mata magani.

Dadah kuwa tin daga ranar da komai ya faru Bata sake walwala ko farin ciki ba Dan itama Allah ne kadai da girman kulawan da maman fadila ta tsayu akanta tai mata kafin Hafiz ya daukesu suka tafiyarsu ya Hana itama nata kan juyewan Dan tini tafara zautuwa Allah ya tsareta Dan haka itama da radadin rashin Ameenatou da tsoron abinda zai iya faruwa da ita Babu kowa take kwana take tashi shiyasa Babbah na tashi Bai Wani Jira Saiya warke sosai ba ya buqaci yarsa itama take ta amince da Hakan Dan duk halinda Ameenatou take ciki tana tsananin buqatan iyayenta.

Hafiz kuwa Daman shi Yana Nan da Shirin dawowa asibitin daukan Ameenatou duk tsawon wannan lokacin Bai manta ba yabari NE su samu Babbah ya tashi sbd duka karfinsu da komai nasu ya qare gurin jinyarsa hatta gidansu dake Nasarawa ya siyar da rabinsa da kudin ne suke amfani har suka qare ya shiga fadi tashi da gwagwarmayar duniya Dan Nemo musu abinci da abin jinyar Babbahn.

Gate din asibitin suka qaraso
Securities na gate din suka kallesu
Daya daga cikinsu ne yace musu

"Baba daga Ina??
Ina zaku shiga???

Hafiz ne ya kallesu cikin nutsuwa yace

"Muna da patient a ciki ita muka zo dubawa"

Wani security dinne ya taso ya qaraso gurinsu ya Kalli Dan uwansa cikin yorbanci yace

"Me suke cewa ne??

"Dubiya suka taho" ya fada masa da yaren Shima Yana dorawa da baima taba ganinsu ba sunzo Kuma asibitin ta kudi ce sosai ta Ina zasuce sunada patient a ciki.

Wulaqantasu babban securities din sukai ta hanyar cewa

"Baba baa dubiya anan yanzu,lokacin ya wuce Kuma yau din bama ranar dubiyan bane so ku tafi sai Next time idan anduba"

Hafiz ne ya kallesu Yana danne ransa Daya fara Baci cikin daidaita kansa yace

"Wainnan iyayenta ne ni brother dinta ne bamu taba zuwa dubata ba sbd abubuwan rayuwa yanzu Kuma munzo kuce mana aa??
Dan Allah dai ku duba."

Ko kallansa basuyiba shi Kuma tini zuciyarsa ta fara harzika Dan haka ya kallesu zaiyi magana Babbah ya riqesa tareda kallansu ya Bude Baki yace

"Yaushe ne ranar dubiyan da kuke magana??

Batareda sun kallesa ba suka ce sai Wani sati.

Dan daure fuska yayi Shima zuciyarsa na 'daci da konuwa ya kallesu yace

"To zan Jira anan har Wani satin Dan wllah tallahi bazan tafi ba batareda naga 'yata ba"

Dadah Dake gefe matsowa tayi zata gwada nata rokon Wani security ya taso Yana hawansu da masifar data Saka ran Hafiz qarasa Baci take suka fara hayaniyar data Saka dole sauran securities din tasowa ana son kashe zancens amma babbah take ya fara son tara musu jamaa dan yayi rantsuwan bai tafiya koina sai yaga yarsa.

Kafin kace me tashin hankali yafara kokarin tashi a gurin sbd Babbah sarai yasan ba barinsu zasuyi shigar ba Amma idan Akai rigimar dole bazaa rasa wani babban daga ciki shiga zancen ba daganan sai a duba buqatansu.

Suma securities din basuda wani dogon mutunci Dan haka suka rufe idon bazasu ma duba maganar shigarsu ba Dan Haka lamarin yafara zama babba mutanen Dake shige da fice suka fara taruwa kallan fitinar.

Babbar sa'ar dasu Babbah suke tafe da ita itace ta taimakesu Allah ya kawo Dr Zakeer zai shiga asibitin motar dr ibrahim na bayansa Dan kusan tare suka iso Dan yau ne zasu tafi da Ameenatou asibitin matar Dr Charles wadda take private ce itace da kanta zata cire musu cikin batareda sani ko fatan samun matsalan komaiba su dawo da ita.

Fitinar da akeyi ce ta Saka Dr Zakeer Dake gaba tsayawa da motarsa batareda ya shige ba ya sauke glass Yana amsa gaisuwan securities din kafin ya Kalli su babbah dake tsaye Wanda kana kallan babbah kasan baida lafiya kwata kwata hakama Dadah Dake gefe kuka takeyi sosai Dan bata dauka ganin ameenatou zai musu wuya ba kenan babu maganar daukanta garesa zuwa gida kaman yanda sukazo da shirin hakan.

Dr Ibrahim ma sauke glass yayi Yana sauraron bayanin da security kewa Dr Zakeer akan hayaniyar.

Kallan Babbah Dr Zakeer yayi cikin girmamawa a matsayinsa na babba garesa yace

"Baba da alama bakada lafiya meyasa zakaita hayaniya
Zaka tayarwa da kanka ciwo ne ko qarawa
Yanzu dai hakuri zakayi baba ku tafi ku bari zuwa Nan da kwana uku ku dawo inshallah zaku samu ganin Wanda kukazo dubawa din"

Girgiza Kai Babbah yayi Yana Jin radadin ransa na karuwa Dan ma ciwone yasaka yake kasa Wani tashin hankalin Amma ai shi Kam bayajin zai matsa daga gate dinnan indai ba daukesa zaayi ba amma wlh Saiya ga Ameenatou yau ba sai gobe ba bare kwana ukun da likitan yake magana kaman yanda sukaji securities na Kiransa Dr kenan alaman shi din likita ne.

Hafiz ne ya Dan matso cikin Sanyaya zuciyarsa da son rokon Alfarman yace

"Dan Allah Dr ku taimaka ku bari mu ganta,
Wlh kusan wata Tara mahaifin nata Yana jinya a kwance yake baisan waye akansa ba duka duka baifi sati uku da tashi ba ita kadai yakeson Gani sbd baisanma ta samu matsalan da aka kawota Nan din ba,. dukkaninmu bamu samu Daman ganinta ba tinda aka kawota..."

Dr Ibrahim Dake jinsu tinda Babbah ya ambaci sunan AMEENATOU acikin zancensa sai sunan ya tsaya masa Dan haka ya katse Hafiz daga cikin motarsa da cewa

"Menene sunan patient din taku??
Daga Ina kuke??
Cikakken sunanta?"

Suna Jin Hakan suka Maida hankalinsu gurin Dr Ibrahim din
Da sauri Babbah yace

"AMEENATOU NUHU BABBAH ko AMEENATOU OMAR JADEN........

gabaki Daya securities din gurin dasu dr ibrahim din juyowa sukai da sauri cikin tsananin mamaki me girma suka kallesa Baki sake.

Dr Zakeer ne ya Bude motarsa ya fito Yana kallan Dr Ibrahim Wanda Shima budewa yayi ya fito ya Kalli security Daya yace a Kori mutane da suka tsaya kallo.

Qarasawa sukai gaban Babbah Wanda yasan ba komai bane ya sakasu shiga mamakin face sunan Omar jeden daya ambata Dan ko ciwon haukan ne da 'yar Jaden sun San tafi karfin asibitin Nigeria bare shi da suke gani talaka yana tsaye da ciwo a jiki.

Dr Ibrahim ne ya sake jeho tambayarsa ga Hafiz sbd tinanin ko Babban baida cikakkiyar lafiyan Kai tsufa yafara cinye kan a natse cikin kokarin fahimtarsu ya Kalli Hafiz yace

"Daga Ina kuke?
"Menene cikakken sunan mara lafiyan taku?

Babu yanda zaayi su fada asalin inda suka koma a yanzu Dan haka Kai tsaye inda aka Sansu a Baya ya fada.

"Daga Nasarawa muke,
Wannan mahaifinmu ne,ga mahaifiyarmu Nan tsaye a gefe,
Ita wadda mukaxo Gani qanwata ce sunanta AMEENATOU OMAR kaman yanda ya fada"

Dr ibrahim zai sake jefa wata tambayar sbd kansa ya kasa dauka, shi ganin yake kaman Basu gane tambayarsa ba, dr Zakeer ne ya katsesa da sauri ta hanyar cewa su shiga ciki ayi maganar kawai.

Daman Hakan Dr Ibrahim Shima yakeda niyar yin Dan haka take aka shige dasu Babbah zuwa cikin asibitin aka bar securities da mamaki me girma da shakka sbd sunan daya fito daga bakin babban.

Kai tsaye office din md suke nufa Wanda yake asibitin tin sassafe sbd hankinsu duka yau din baa kwance ba da abinda zasu aikatawa Ameenatou,
A matsayinsu na likitoci sunsan illan abortion da hadarinsa musamman irin wannan da sune zasuyi sa da kansu,Barna ce akan Barna suke Neman aikatawa Dan rufe Barna da barnar,
Fatansa dai Allah yasa sunada Rabon rufe wannan Barnar batareda komai ya faru ba.

Shigowan su Dr Zakeer office dinsa ne ya Sakasa sauke ajiyan zuciya zaiyi magana su Hafiz suka kunno Kai.

Kallansu Dr Ibrahim yayi Yace su Jira waje tukuna.

Komawa sukai waje suna Jira Dr Zakeer ya rufe kofar ya dawo Yana cewa

"Dr ibrahim kana tinanin baban Nan Yana lafiya kuwa??

Numfashi Dr Ibrahim ya sauke Yana fara jerowa md bayanin komai kafin ya Dora da cewa

"Lafiyansa kalau ga dukkanin alama,
Kuma idan na Tina duka bayanin Ameenatou dayake rubuce a file nata itace Ameenatou Omar Kuma address nata Nasarawa ne kadai a jiki,sedai abin mamakin anan shine wannan din yace shine mahaifinta sannan Kuma ya ambaceta da Ameenatou Omar Jaden a sanina Kuma Omar Jaden Daya muka sani Babu wani"

Qara karfin AC md yayi sbd zufan Daya fara jiqasa hankalinsa na tashi kansa na daukan zafi kaman yanda Dr Zakeer Shima ya rude.

Wata masifar ce da alama take Neman Hawa akan masifar da suke ciki.
Chapter 31 · 0% Book details