← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 88

Sashe 36

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meya hada haroon da wannan kwayoyin?
Kota Yaya kwayoyin Nan suka Isa ga dansa BB Ya sani Kuma zai bayyanarda saninsa Dan kuwa Koda Haroon ne da kansa ya Siya yasha Saiya tabbatarda Wanda ya siyar masa din yabisa inda yake,
Idan Kuma Wani ne ma ya illata masa shi to bayanin dai duka dayane.

Wayarsa ya daga cikin nutsuwa ya Saka Kiran Lameenu Yana daidaita kansa tareda bayyanarda nutsuwansa a sauti.

Lokacinda Kiran ya shiga wayar Lameenu Yana zaune tareda matarsa mum Sarah suna magana tana zuba masa fresh Madara me sanyi a cikin bowl din fruit Dake gabansa.

Kallan wayar yayi Yaga sunan Mam,

Da mamaki ya sake kallan wayar sbd saninsa Mam Baya kasar,
Sake dubawa yayi da kyau sai yaga Whatsapp call ne Dan haka ya dauki wayar Yana ambatar sunansa da cewa

"Ya sauka ne??

Dan murmushi Mam yayi Yana jeho masa gaisuwa suka gaisa suna shiga zancen abubuwa daban daban tsawon lokaci kafin Mam yace

"Ina Poland tareda Jamaal yayi rashin lfy nazo dubasa Amma bamu Hadu ba sbd zafin kansa yaqi sauka har yanzu,
Amma Kuma na samu Wani zance me daure Kai akan rasuwar Haroon a bakin Siddeeq batareda sun San naji Hakan ba,
Jamaal Yana zargin mune muka kashe Haroon Dan haka bincike ake masa sosai,
Binciken ba abin damuwarmu bane sbd nasan Babu Wanda ya Isa ya kashe 'dan Mamman Seelah idan ba Allah ba,
Amma abin mamaki anan shine Dr zayyan naji ya kira siddeeq Yana sanar dashi sun samu hada results din Haroon Dana Wani Dr da akace ya rasu kwanaki.............

Ruwan Madarar da aka zuba cikin fruit salad dayake Sha ne ta biyo ta hancinsa da karfi cikin sarkewan tashin Yana dire bowl din har Yana zubewa a shaqe yana dedeta muryansa yace

"Me yake kokarin yi da results din Wani daban Kuma??
Meye amfani ko dalilin Hakan?
Haroon ya Riga ya rasu yabar Dan uwansa ya kwanta lafiya,
Kuma yasan dai Babu yanda zaayi mu illata Haroon da kanmu sbd shi 'dan mu ne"

Murmushi me sauti tareda ajiyan zuciya Mam ya sauke Yana sakewa a natse yace

"Nabari su hadasa da results din Dan Nima inason Jin Menene sakamakon"

Zufa lam ya share Yana miqawa Mum Sarah hannu ta Sako masa tissue ya sake goge hancinsa da ruwan Madara ke fitowa ciki har lokacin.

"Hakan ma shine daidai muna buqatan samun results din kafin JAMAAL din Amma sbd kada Akai masa abinda zai ruguza mu batareda mun saniba"

Murmushi Mam ya sake sakewa Yana cewa

"Dayake shi din jinina ne Magajina zai iya samun Hakan Amma bayan shi kansa ganin akwai Wanda zai taba Mam Seelah tabawa irin wannan ya miqe kuwa?"

Dariyan karfin hali lam ya sake Yana janyo Wani zancen.

Sallama sukai Mam Yana ajiye wayarsa gefensa idanuwansa na sauyawa sosai sbd ya karanci abinda yakeson karantar.

Lameenu seelah yayi wautan datafi shiga ruwa da hular dutse.

Wayarsa y dauka Kai tsaye ya kira bullet yace a Saka ido a gidan Dr zayyan a Gani idan zaa Kai masa hari a gidansa.

Hakama a tanadar masa kwayoyinsu zaiyi gwajin overdose da normal dose ga mutum biyu Daya overdose Daya normal dose Kuma a cikin ahalin seelahs zaiyi kwajin idan har ayau ankai farmaki gidan Dr zayyan zancen ya sake Bude masa da kyau.

Yana kashe wayarsa miqewa yayi ya shige ciki Yana Jin Asalin jininsa na Seelahs na Wani irin tafasa da kunar da Bai taba samun kansa a cikiba,

'dan cikinsa ake maganar anyiwa mummunan illan da tai kusan sanadinsa koma tayi din Dan ko baiyi accident ba mutuwar zaiyi sbd kwayoyin bazasu taba barinsa ya rayun ba,
Tabbas zaiyi gwajin abinda yagani a ranar da Haroon dinsa ya ringa aman jini da kusan mutuwa,
Zaiyi gwaji ga mutane biyu da Hakan zai girgiza kowa Dan tantanve yawan adadin Wanda suka durawa 'dansa kafin ya waiwayi Wanda yayi aikin gaba daya.

Lameenu kuwa tinda ya ajiye wayar yake Neman wayar BB Amma kwata kwata Baya samu Dan haka dole bullet ya kira Kai tsaye sbd idan gari ya waye komai zai iya faruwa idan Dr zayyan ya aikawa JAMAAL sakamakon komai zai iya faruwa Wanda yasan sanin JAMAAL kadai zai iya zautashi bare Mam ya sani.

Mum Sarah Kuma itama tashin hankalin take Neman shiga na Neman Aliyah da aketa yi tin dazu Babu zancenta Babu labari,
Siyam kuwa ma Bata qasar sai satin zata dawo Dan haka hankalinta ya tashi tanason sanar masa Amma ganin Halinda yake ciki na Kaida kawo Yana hada zufa ya Sakata kasa sanar masa taci gaba da Kiran Aliyahn.

*********Sai dare sosai suka Isa lokoja lokacin Ameenatou tayi Nisa sosai a bacci,

Taxi suka dauka har kofar sabon Dan qaramin gidan dasuke haya Hafiz ne ya Bude gidan bayan ya sallami me motar suka shiga Ameenatou na qanqame hannun Babbah sbd duhun datake Gani tafara Kiran sunan jamaal Dana sister Ashley.

Da sauri Hafiz ya qarasa ya kunna wutar tsakar gidan Yana cewa gashinan ya kunna mata haske.

Rintse ido tayi tana Jin kaman zata tsorota Amma yanda suka zagayeta kowa na kokarin rarrashinta ya Sakata fasa rikicewa ta Bude Baki a hankali cikin sanyi da kasala tace

"Ameenatou zatayi fitsari,
Kuma Ameenatou zatasha tea"

Dadah ce ta zare mata qaramar hijab din kanta tareda kama hannunta zuwa toilet din tsakar gidan dayake fes takaita Tayo suka fito.

Babu maganar gyara a tsakar dare Dan haka salloli sukai Dadah tayiwa Ameenatoun wanka Hafiz ya kawo tea da bread tareda kwai aka Bata Tasha tea sosai Amma bataci kwan ba tana gamawa tafara neman Jamaal kafin ta rikice bacci yayi gaba da ita.

washe gari da safe gyaran gidan dadah tayi tareda gyare dakin Ameenatou din tsaf tai mata wanka ta Saka mata kayanta ta zaunar da ita tana binsu da kallo kowa na faman yimata hidima kaman zasu cire mata ciwonta a rana Daya lokaci lokaci tana Ambatar a kira mata Jamaal da sister Ashley.

Abinci dadah ta Dora Babbah kuwa gefen Ameenatou Shima Akai masa shimfidar ya zauna Yana tayata duka shiririta ko rikicin da zatai
Hafiz kuwa wankin kayansu da suka dawo dasu yayi harma Dana Ameenatou din Yana gamawa ya fita aiki Super market din dayake Aikin yamma.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[29/05, 10:07 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
92

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

**********
Wayoyinta takeyi cikin wayewa da sakewarta tareda Isa irin ta macen da kudi ya gama ratsa rayuwarta Tako ina batareda sanin Menene wahalan rayuwa ba bayan bacin Rai da damuwan rayuwa irin Wanda ba'a rasa ba,

Bullet Yana driving ne Amma hankalinsa kunnuwansa na kanta sbd bazata Fadi inda zata ko tareda waye take Kokuma gurin Wanda zata je, wayoyin business nata ne da mutanenta sai yaranta dake kira dan tambaya ko sanar da ita wani abin.

Tafiya me Dan tsayi sukai kafin suka Isa gidan Kai tsaye ya shige da motar ciki aka rufe gate ruf.

Parking yayi tareda kashe motar ya juyo ya kalleta Kai tsaye yace

"Mun iso"

Budewa yayi ya fito tareda zagayowa ya Bude mata
Tana fitowa ya nuna mata hanya Yana cewa

"Barka da zuwa"

Gaba tayi tana kashe call datake yi ta Saka wayar Jakarta tana Dan kallan tsarin gidan da yayi kyau Kuma Babu wani hayaniya anguwar da gidan duka tsit,
Yana boye da ita Yana nuna mata inda zata shiga har suka Isa kofar palon ya Bude mata tareda janyewa gefe ta shige Shima ya shigo ya rufe kofar
Yaronsa Dake bayansu ya tsaya bakin Kofar Yana fidda wayarsa ya kunna waqa iPod na kunnensa.

Suna shiga handbag dinta bullet ya miqa hannu ya karba mata tareda ajiye mata inda zata zauna ta zauna a natse cikin nutsuwa tana Dora kafarta Daya akan Daya.

Ko minti biyu batai a zaune ba Mam ya fito cikeda nutsuwa da girma kallo Daya yayi mata ya amsa gaisuwan datake masa cikin sakewa Dan akwai sakewa sosai a tsakaninsu da yaransu tareda Wani irin gata da sakewan dukiya da ake musu,

Aliyah Seelah itace hasken idaniyar Daddynta haka Kuma tafi duka yayansu rawar Kai da nuna Isar su waye iyayenta,

Zaunawa yayi tareda ajiye wayarsa gefensa ya juyo ya sake kallanta itama tayi shiru shi take Jiran bayani daga garesa
Maida kallansa yayi akan bullet Dake tsaye yace

"Itace Ameenatou Omar a asibitin da aka dauke Ameenatou din daga yau,
A file,a suna,a rayuwa,a hauka,a alluran asibitin a gurin kowa da kowa likitoci da nurses tareda mahaukata Yan uwanta itace Ameenatou Omar daga yau,
Abari ubanta yaci gaba da Saka ana kasheta da alluran hauka batareda yasan waye yake kashewan ba da hannuwansa kafin daga karshe su BB idan sun samu sa'a su cika masa Aikinsa na son kasheta idan an kawo gawarta janazah yagani da idonsa wacece Ameenatou din,
Duk Wanda ya kirata da wani suna bayan Ameenatou a asibitin a aikasa inda kowa yake gudun zuwa wannan umarni nane,
Nagama magana da duka manyan asibitin akan wannan miqata kawai ne ya rage."
Chapter 36 · 0% Book details