← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 88

Sashe 43

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zo zauna kiyi breakfast din dai kafin ko fita banasan fitarnan batareda kinci komaiba,gashinan duk cikinki ya shafe sbd rashin cin abinci yanda ya kamata"

Murmushin Jin dadi tayi tana rungume dadahn ta Baya tana cewa

"Dadanah yau ni kikeji Dani kenan?"

Itama dadan murmushi tayi tana janyota daga bayan nata ta zaunar da ita akan dining tana cewa

"Idan na Dena ji da 'yata naji da waye??

"Hmmm Dadah ai Kinsani ni yanzu duk Kunje Kun Raba mun soyayyana da kukemin Kun bawa ARFAT har nashi Yana son fin nawa ma,
Ni Babbah ma fushi zan fara dashi"

Maids ne guda biyu suka shigo dining din kowanne Yana Turo kayan breakfast da aka shiryo.

Suna isowa ta farkon ce ta fara Dan kallan Ameenatou cikin girmamawa tace

"Good morning lady AM"

Dan juyowa tayi tareda amsawa a natse tana kallan abincin da suke jerawa kafin dayar itama ta gaidata suka gama jere komai suka juya.

Qamshin Hafiz ne ya cike gurin dadah ta dago tana cewa

"Bara naje dai naji da Angona kafin ku gama tinda ga Hafiz Nan,
Kaima ta tabbatarda kayi breakfast din kafin ka fita."

Daukan tray dinta data ajiye farko tayi ta wuce zuwa sama inda Ameenatou ta sauko.

Dago fararen idanuwanta tayi ta Kalli Hafiz lokacinda ya qaraso gurin ya ja kujera ya zauna ya ajiye wayoyin Dake hannunsa guda biyu gefensa ya dago Shima ya kalleta Yana cewa

"Yaya dai,
Ina Champ dina?
Haryanxu Bai tashi bane banjisa ba time na school ma Ya wuce fa."

Hanyar sama ta kalla kafin tace

"Yaya Hafiz ko gaisawa bamuyiba fa,
Yana can Yana rigima yau da ita ya tashi Sam shi bazashi school ba sai Dad ya Kaisa da kansa Kuma ka sani Dad Baya qasar bansan ya zan masa ba ga Dadah can ta tafi Kila su daidaito."

Sam sama Yaya Hafiz din yayi breakfast dinsa da bama Wani abin kirki yaci ba ya miqe ya nufi saman Kai tsaye zuwa dakin ARFAT din Dan yasan Yana can.

Yana Isa ya miqa hannunsa ya Bude kofar dakin Ya shiga Yana cewa

"Where's my boy??"

ARFAT din Dake tsaye sanye da bvlgari underweyna Yara me shegiyar tsada gabaki Daya jikinsa kaman babyn da Bai taba fita Rana ta tabasa ba haskensa koyaushe qaruwa yakeyi,

Kaya Dadah zata Saka masa ta basa fruits dinsa Amma Yana Jinsa ya kwace da gudu ya Isa gurinsa bakinsa a washe da farin ciki Yana cewa

"Uncle Buddy"

Daukesa Hafiz yayi yai sama dashi Yana cewa

"Waye ne ya taba mun my boy?"

Dadin maganar yaji ya juyo ya Kalli Dadah Yana dariya fararen qananun hakoransa na bayyana kafin ya juyo ya Kalli Hafiz din yace

"My Mommah and granny D"

Kallan Dadah Hafiz yayi Yana qarasawa ya karbi kayansa a hannun Dadah ya ajiyesa kan gado tsaye tafara saka masa Yana cewa

"Dadah kune kuka tabamun yaro keda yarinyarki gashinan yayi fushi yaqi zuwa school,"

Ko kulasa Dadah batai ba ta Kalli Sarrah Nanny din Arfat din wadda ita iya aikinta a gidan na kulawa da Arfat da duk abinda ya shafeta Koda slippers dinsa ne kuwa.

Tana tsaye yaqi yadda ta Saka masa kayansa gashi lallabasa akeyi baa masa Wani dole Mommah dinsa da Dadah ne kadai a gidan suke masa fada da masa dole Amma kowa Baya takurasa Baya laifi ko kadan a agurinsu.

"Sarah jeki kici gaba da aikinki"

"Ok ma" tafada tareda juyawa tafara gyara dakin da Babu ma Wani gyaran komai a cikinsa gashi da girma da kayan Yara irin na buqata da wasan Maza masu tsada da kyau a tsare kaman dakin shine na sarkin mansion din gaba Daya"
##MAMUH
#AM JDEN
#THE JDENS
#THE SEELAHS
#ARFAT OMAR JDEN

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[29/05, 10:07 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
96

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

*************
Cikin sanyi da nauyin zuciya Dadah ta Bude Baki tace,

"Cikinta ne muka ga yayi girma Kuma Babu rashin lafiyar komai"

Kallan Ameenatou din yayi kafin ya Kalli su Babbah yace su Basu gurin Abar Dadah kawai.

Fitowa sukai Babbah kirjinsa na wani irin toshewa,
Hafiz riqesa yayi sbd har lokacin Bai fahimci komai ba.

Zaunar da Babbah yayi batareda ya iya cewa komaiba sbd ganin lamarin me girma ne Dan ba qaramin lamari ke Saka Babbah shiga wannan mummunan halin ba.

Zaunawa sukai shiru shiru kowa da abinda zuciyarsa ke sakawa cikin damuwa da fargaba har tsawon mintina kafin aka fito dasu zuwa gurin scanning tareda Dadah wadda bata iya kallansu ba.

Can ma Basu Wani jima sosai ba suka dawo suka shige office din ganin likitan sai gashi Shima daga bayan ya dawo ya shige.

Dadah ce ta fito ta kira su Babbahn ciki.

Tasowa sukai suka shiga suna kallan Ameenatou Dake zaune duk zazzabi na Neman taso mata sbd bata Saba wahala ba hakama duk an cakuda mata ciki gurin scanning ga yunwa tanaji.

Likitan mamakinsa ya fara bayyanarwa tareda tambayarsu basusan ciki bane da tana dauke da cikin kusan wata BIYAR Amma ace Basu gane ba.

Fiddo idanuwa Hafiz yayi da sauri cikin tsananin tashin hankali da mamaki me karfi Ya kalli Ameenatou kafin ya Kalli Babbah da Dadah murya na sarkewa yace

"Ciki Kuma?
Cikin haihuwan 'yaya ko me??
Budurwan Babbah ake magana kokuwa wata daban??

Kukan da Dadah ta fashe dashi jikinta gabaki Daya Yana daukan rawa ya Saka likitan yin shiru cikin mamaki da tausayinsu Dan alama dai Wani ya lallaba cikin rashin hankalinta yayi mata cikin.

Daqyar Babbah ya iya Bude Baki da Dan karfin Daya rage masa yace

"Likita kace ciki?Kuma harna wata biyar?"

Ajiyan zuciya Dr ya sauke cikin sanyi kafin ya gyada Kai Yana cewa

"Eh inshallah"

Wani abu me nauyin gaske ne ya danne zuciyar Babbah Wanda ya Saka idanuwansa fara yin duhu Yana dafe kirjinsa.

Hafiz ne yayi karfin halin tare babban shida likita suka fito dashi Dadah kuwa kuka takeyi mara sauti tana share Hawaye.

Mota suka shiga da Babbah suka nufi gida Babu Wanda ya iya magana a cikinsu sbd babu Wanda zuciyarsa take bugawa daidai ko kadan,

Dadah sbd kuka Koda suka iso idanuwanta sunyi mummunan kumbura,
Hafiz kuwa idanuwansa ne sukai Wani mugun jajir hannuwansa na Dan rawa ya damqe takardan awon cikin datake hannunsa.

A tsakar gidan suka zauna kowa shiru Babu Wanda ya iya cewa komai har lokacin hakama Babu Wanda yake Gani ko ji daidai.

Wani radadi me tsanani idanuwan Hafiz keyi sbd abinda yake cinsu,
Zuciyarsa radadin Datake yasa har lokacin jikinsa yar rawa yakeyi,

Rintse idanuwansa yayi ya sake budewa sai kawai ya fashe da wani irin kuka Mai ciwo da radadin zuciya sbd ya kasa riqe abinda yake ji.

Kukansa ya Saka gidan ya sake daukan tsit hakama Babbah hawayen dayake riqewa ne suka gangaro masa Shima zucuyarsa na sake nauyi.

Kuka sosai Hafiz ke yi dukkanin jikinsa na jijjiga da rawa,
Duk masifar da suka shiga Bai taba kuka irin haka ba sai yau,
Kuka yakeyi sosai kaman ba namiji Mai karfin hali da jarumta ba.

Dukkaninsu kuka sukai Saida idanuwansu sukai jajir Ameenatou na zaune gefe tana Shan fruits itama jikinta a Sanyaye.

Sun jima a wannan mummunan yanayin kafin Hafiz ya miqe ya dibi ruwa a bucket ya shige toilet.

Wanka da alwala yayo ya fito ya shirya ya wuce masallaci sallan magrib da ake kira.

Babbah kuwa Saida Dadah ta taimaka masa ya samu yayi alwalan yayi sallan a gida Dan bazai iya fita.

Itama sallan tayi tareda Ameenatou Dake gefenta.

Shiru gidan yai Babu Wanda ke ko dogon motsi,

Saida Akai ishai Hafiz ya dawo gidan ruwa kadai yasha ya shige ya kwanta.

Ameenatou din kadai Dadah ta bawa tea Tasha ta shiryata ta kwanta Suma suka shige sbd Babbah tini ya shige sbd lafiyansa datake rawa tini zazzabi me karfi ya rufesa da nauyin kirji me tsanani.

Yanda suka ga Rana haka suka ga Daren Dan Babu Wanda ya samu bacci ya ziyarci idanuwansa idan ba Babbah da ciwo ya rufesa a cikin Daren Wanda daqyar sukaga safe suka tattarasa zuwa asibiti.

*******Jinyar kusan sati biyu Babbah yayi a asibiti kafin aka sallamosa suka dawo,
Hafiz Shima ciwon ne yake Neman kwantar dashi Amma yayi karfin zuciya yaqi barin Hakan sbd idan ya kwanta shine bangon gidan Dan komai shike nemowa Dan haka ya sake sakawa kansa karfin hali Amma zucuyarsa bata qara lafiya ba daga ranar da cikin Ameenatou din ya bayyana garesu hakama Babbah lafiya tini tafara masa rawa gashi sun rufe maganar cikin a tsakaninsu batareda sun tsaya Jan maganar inda cikin ya fitoba sbd cutace ta tabbata an musu mummunan illa,
Idan ma sunje asibitin wahala ce zasusha kudin ma zuwan Lagos a yanzu basuda shi hakama Babbah har abada bazai yadda a nunawa Ameenatou dinsa yatsa ba,.kaman yanda suka reneta Babu Uba Hakan zasu reni abinda zata Haifa Babu Wanda har abada zai San fyade Akai aka samesa matiqar Yana Raye.
Chapter 43 · 0% Book details