← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 88

Sashe 37

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aliyah data kasa fahimtar komai sbd Batama yaddarwa kanta cewan itace ake magana a kanta tinda sunan AMEENATOU din uncle OMAR taji ana fada Dan haka Bata motsa ba bare tankawa jiran takeyi ya gama da bullet yayi tasa maganar da zaiyi da ita.

Bullet kuwa numfashi ya sake Yana gyada Kai yace

"Angama Ranka ya Dade"

Wasu shegun kwayoyi ya ajiye akan table din gabansa batareda yace komaiba yana Kuma zaune a natse ba hayaniya.

Bullet ne ya matso ya dauki kwayoyin qananu sosai guda shida ne a ciki
Ya dago ya Kalli Mam din.

Ganin Mam Baice komaiba yasan me abinda yake nufi Dan haka ya budesu a take Yana kalla sbd saninsa baa wuce Shan Daya da Rabi ko a gurin namiji bare mace Amma tinda shida Mam ya ajiye to tabbas shidan yake nufin a Bata.

Ita Kuma ganin bullet ya dosota da kwayoyin taji gabanta ya Fadi hankalinta ya fara tashi ta juya ta Kalli Mam din da sauri tana kokarin ambatar sunansa ya miqe yabar palon.

Da sauri ta miqe itama tana kallan bullet da tashin hankali me tsanani da tsoro tace

"Menene?
Meyake faruwa?
Me zakayi?

Kwala sunan Dad Mam din tayi da karfi tana shiga tashin hankali babba Dan jikinta har wani rawa ya fara.

Kwayoyin haukan bullet na cocaine da kwayoyinsu Mam din da suka haukatasa tini suka motsa Dan haka ba Imani ko kalilan a ransa ya fizgota tareda shaqeta jikin Bango Yana kallan rigar jikinta.

Hakurinsa ya Saka ya kama gefen rigar ya yagasa Yana kallanta da jajayen idanuwansa,

Babu abinda zaiyi da ita Amma dole Yana buqatan yi mata Hakan sbd cike aiki.

Ja idanuwanta sukai tareda fitowa kaman zasu fado sbd shaquran da yayi mata,

Bude Baki tayi tana kokarin shidewa ta mutu ya yada ledan hannunsa Daya da bakinsa ya watsa mata kwayoyin gabaki dayansu cikin bakinta tareda sakin wuyanta taja Wani azababben numfashin Daya Saka kwayoyin wucewa cikin maqoshinta zuwa cikinta gabaki dayansu a take.

Zubewa tayi qasa tana riqe wuyanta cikin tsananin azaba tana Tari tareda Jan numfashi cikin wahala da azaba.

Tsayawa yayi kallanta Yana gyara gaban rigarsa data riqe datana kokarin sheqewa.

Tarinta lafawa yayi ta dago jajayen idanuwanta ta kallesa tareda Bude Baki zatai magana Wani irin jini kaman Wanda aka tunkudo daga cikin cikinta ya tunkudo da qarfin gaske daga bakinta idanuwanta na kakkafewa jikin na wata irin jijjigan data Saka bullet din Baya sbd kada ta tabasa.

Fitowa Mam yayi hannuwansa da qaramin towel Yana goge hannuwansa Daya wanke daga toilet na qwayoyin daya taba.

Kallanta Yayi Yana nufar inda wayarsa take y dauka Yana zaunawa yace

"Ku qarasa aikin ku miqata"

Allura bullet ya fitar ya qarasa gurinda take kwance tana mummunan jijjiga har lokacin ya durqusa gabanta tareda Saka hannu ya danne kanta a qasa Babu shakka ko tinanin Munin kwayoyin da aka afka mata ya soka alluran cikin Naman wuyanta tareda danna mata ruwan cikin Syringe din da suka Saka komai nata sanqarewa a take kaman gawa,

Wasu azabbin Hawaye ne masu zafin gaske Wanda bama hawayen bane a zahirance ruwan azaba ne suka gangaro Dan kuwa Babu abinda Bai tashi aiki daga jikintaba bayan ranta dayake Nan Bai fita ba sai idanuwanta da suka qafe basa iya rufuwa.

Jinin dayake zubawa bakinta ahankali ya Dena sai gashi Yana gangarowa ta cikin kunnuwanta da hancinta a hankali.

Dauke Kai Mam yayi daga kallanta Yana duba wayarsa sedai yanda jinin ke fitowa ta hanci da kunnenta tareda jijjigan datai kafin jikinta ya tsaya cak ya sakashi ajiye wayarsa gefe Yana karantar yanayinsa a matiqar tsanake yanayin Haroon irin Hakan Yana dawo masa dan a irin wannan mummunan yanayin ya tsinci 'dansa.

Wani sarawa kansa yayi Yana sake zurfafa kallo da tinaninsa,
Shigowan Sako ne a wayarsa ya sakashi miqewa zai nufeta Dan tabbatarwa sai gashi sunan Dr zayyan ya bayyana kan wayarsa shine ya tiro masa sakon.

Bai Budeba Saida ya sake karance yanayinta tsaf kafin yace su wuce da ita din bayan kammala shiryata.

Cikin rashin Imani da tausayi bare Tinawa ko kallanta a mace bullet da yaronsa Daya suka goge duka Wani jinin Daya Bata jikinta kafin bullet ya sake shaqa mata cocaine da take tayi cikin kanta Amma k motsi Batayi Dan kaman Babu rai kwata kwata a jikinta.

Mota suka Sakata tareda zaunar da ita kaman mutum suka dauko Jakarta da wayarta Dan konawa.

Karfe Daya da Rabi na Daren suka shigar da ita asibitin Wanda kafin Daren ne tini aka sauya md da wasu daga cikin likitocin Da Mam ya buqata Hakan Dan haka Koda gari ya waye ma'aikatan asibitin sun tashi da sabuwar patient dinsu me suna Ameenatou Omar wadda da yawa sunyi mamakin sunan Daya Zak Dana patient din Data bar dakin haka zalika ita nata haukan a abinda aka sanar dasu Shan qwayoyine ya juyar da ita haka gaba Daya ta koma kaman mutum mutumi.

Kafin goman safe tini aka rufe case din Ameenatou gabaki Dayansa tareda sabuwar Ameenatou sbd likitoci tini suka fara binta da alluran ganin ko zata dawo daidai daga gawa-mutum Data koma Kuma har lokacin idanuwanta a Bude suke basu rufeba.

********Sakon Dr zayyan Daya shigo wayar Mam ba komai bane face results din Haroon da bayanan kwayoyin da suka samu a cikin jininsa lokacinda Yana Raye da Akai masa wannan mummunan abin tareda yawan adadin wadda suka samu a jinin nasa,

Binciken Jamaal NE da Shine yayi masa kusan duka test din a lokacin tareda results dinsu na duka awon da sukai masa lokacinda ya koma hannunsu Poland duka komai Siddeeq ya hada ya bawa Dr zayyan akan ya turawa Mam din da nufin yayi mantuwa ne JAMAAL zai turawa.

Mam Bai Bude sakon ba sai dare Dr zayyan ya kira wayarsa Kai tsaye lokacin Yana zaune Yana kallan Wani news hankalinsa Kuma na ga tinanin irin rawar da lam yake takawa a gabansa da nufin bai saniba,

Me Lameenu ya daukesa?
Yana tinanin duka wannan shekarun dasuka debo Yana aikata Barnar datafi tasa shi Lameenun zai iya lalata masa aiki ne na burin shekaru??
Hmmmm dukiyar Omar tasa ce kaman yanda yake sake tabbatar da Hakan,
Babu Wanda ya Isa ya shiga tsakaninsa da burinsa na mallakar dukiyar Omar wadda ta Sakasa komawa Mam din dayake a yanzu.

Ameenatou da lam ke kokarin illatawa sbd Abu biyu ne ya sani,
Sbd dukiyar Omar da Kuma tsoron zamanta Sirikitarsa shi Mam din.

"Tabbas lameenu dole kaji tsoro ko shakkar barin Hakan Dan kuwa Omar a hannuna yake tinda yarsa tana auren "Dana,jinina,tsatsona,
Ameenatou itace mukullin arzikin Da duka jinin Dana zubar Dan share fage Bai iso gareniba sai data shigo hannuna,

Ameenatou ayanzu ko ubanta Daya haifeta bazai iya rabasa da ita ba Dan kuwa Babu Wanda bazai iya batarwaba akan ta shigo hannunsa ta dawo gidansa ta zauna a qarqashinsa a matsayin sirikarsa da zai iya komai akanta Dan itace key na tarin Zinariyar Daya Sha jini Babu adadi akanta,

Dan haka kafin mahaifinta da Jamaal su San inda take Yana buqatan Rigan kowa samunta Dan dawo da ita gida a karkashinsa sbd shigowarta hannunsa zai basa Daman mallakan Abu biyu dayafi tsananin so da buqata a rayuwa wato 'dansa JAMAAL da dukiyar Omar harma da mutuwar Omar din.
#MAMUH

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[29/05, 10:07 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
91

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

**************
Sister Ashley Dake asibiti Rai hannun Allah sister dinta na ganin Hakan ta cire Rai daga tashinta Dan haka ta fara shirye shiryen tafiya gida da ita can Asalin garinsu gurin yan uwa dan idan ma mutuwan zatai ta mutu a hannunsu dan hakan sukeyi so sunfi son ciwo na tsananta a kaika gida kawai.

Kasancewanta Ma'aikaciyar jinya itama yasaka Bata Sha Wani wuya ba gurin samun Daman tafiya da ita Dan haka cikin kwana hudu tana samun sauki kadan ta tattarata ta dauko mota har asibitin aka dauketa suka tafi Dan hakama Koda abokan aikinta na asibitinta suka taho dubata antafi da ita Basu Sami damar ganintaba.

*********A Poland kuwa komai ya rikice sbd Hankalin JAMAAL da kwata kwata Baya tareda shi sbd rashin ji daga Ashley kusan kwana nawa Dan haka dole abokan Aikinsa da Baya communicating dasu ya nema Dan gap kansa yake da kuncewa akan Hakan.

Dr Charles tinda suka sallami Ameenatou yayi blocking Dr JEEY din a wayarsa batareda sanin kowa ba dan kada ma tsautsayi yasa ya nemesa idan ya tashi,

Dr ibrahim ma Hakan yayi ya rufesa bazai iya samunsa ba Dan haka dr Zakeer kawai ya samu sbd shima shi kadai yake da number dinsa Shima.

Kiran JEEy Yan shigowa wayar Dr Zakeer Saida kansa ya Sara duk da baisan waye me kiranba Amma ganin numbern ta waje ce yasan JEEY dinne.

Kasa dagawa yayi harta tsinke Wani Kiran ya sake shigowa,

Baida zabi haka ya daure ya daga Kiran cikin kokarin natsuwa da daidaita kansa ya dauka da sallama.
Chapter 37 · 0% Book details