← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 88

Sashe 13

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani sarawa Rabin kan daddy lameenu yayi ya dago idanuwansa sai alokacin ya zubawa Dr Dee su yanason Tantance kodai alluran mahaukan asibitinsu ta cakesa ne ta samman masa juyewan kan,

To Amma a yanda ya fada cikakkiyar sunan JEEY din alamace ta kaman daidai yake.

"Dr Dee ka tabbata JEEY SEELAH ne dai namu kake magana Akai??
JAMAAL SEELAH 'dan Mam??

Kasa magana Dr Dee yayi saima zaro takardansa ya ajiye gaban Daddy lameenu din Yana dafe goshinsa tareda rintse idanuwansa da sukai jajir kaman zasu fashe.

Daukan takardar daddy lameenu yayi ya karanta Bai qarasa ya tabbatarda wlh tallahi aikin JEEY din Kuma Hakan na nufin Yana zargin Dr Dee din Kokuma yafara fahimtar akwai Wani abu a qasa game dashi Dan haka yaji zufa na jiqasa.

Dole Yana Neman batar da sheda ko duk wani abu da zai danganta sunansa ko da Saka hannunsa akan abinda yake faruwa acikin asibitin bare kofar asirinsa su bude gaba daya qiyamarsa ta tsaya.

Kallan Dr Dee yayi da idanuwansa da suka sauya take yayi Yana hango masifun da zasu biyo bayan sanin Abu Daya da JAMAAL zaiyi daga Dr Dee hakama a yanda Dr Dee dinnan yake a rude a rikice cikin tashin hankali da son riqe position dinsa na asibitin JEEY zai iya samun Wani sirrin daga garesa Wanda shine karshen tashin hankalin da zasu shiga shida su BB Dan haka dole ya sassauta ya sake numfashi cikin nutsuwa da kwantarwa Dr Dee din da hankali yace

"Dr Karka damu da wannan takardar Babu abinda zai faru Nima ayau dinnan basai gobe ba zanyi magana Koda zaka tashi goben zaka samu kyakkyawar rayuwa tana jiranka inshallah."

Kasa Kwanciya hankalin Dr Dee yayi Amma hakanan daddy lameenu ya tabbatarda ya kwantar masa da hankali tareda masa alkawarin sabuwar rayuwa kafin goben inshallah Dan haka ya sake tareda Jin nutsuwansa ta dawo jikinsa.

Hadda kudi masu kauri daddy lameenu din ya basa kafin sukai sallama bayan sun Dan jima suna tattaunawa ya wuce.

Yana ficewa waya daddy lameenu ya dauka ya Saka Kiran BB Wanda Shima daga kwancen dayake tashi yayi da karfi Jin Jamaal na qasar ya dawo Amma Kuma ya Akai duk baza idanuwa da kunnuwan da sukai Basu taba sanin ya sauka kasarba.
##MAMUH#
#AMEENATOU
#BESTLOVE

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*[29/05, 10:04 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
72
Fahat kuwa tini tashin hankalinsa da balain dayake Gani na tonuwan asirinsa ya saka shi Neman haukacewan shima dan haka Babu wani sauki ko tausayi a idanuwan JEEY d suka gama rufewa Yana ganin yafara haukan ya Saka aka kawo masa Alluran da Dr Dee yake sakawa yana Ameenatou idan ciwonta ya tashi take yayi masa ita Shima.

Wannan aikin tin kafin zuwan likitocinsu da sauran manyan asibitin yayisa Dan haka Koda suka iso Fahat tini yake kwance Yana Wani juyi Yana ihu da buga Kai a qasa Yana yagar jikinsa.

Hankali tashe aka daukesa Akai dakin duba patients dinsu dashi sbd Babu Bata lokaci Dr JEEY ya sanar dasu da alama Daman yanada tabin hankali sbd an kamasa da laifin shiga dakin son haiqewa patient haukansa ya tashi.

Yana fadan Hakan ya juya ya wucewansa sbd Yana buqatan Fahat din a cikin asibitin Dan sanin waye yake son kashe Ameenatoun ta hanyar Banka mata alluran da kisheta zasuyi Kai tsaye bawai iya juyar da Kai ba Dan yanda akeyinsu abin ya wuce tinanin me tinani Dan haka bazai so miqasa yanzu ga sojojin da zasu kakkarya masa duka wata gaban Dake jikinsa Saiya gama dandana masa azaban da duka Ameenatou tasha dan duka lissafin yawan alluran dake cikin file da Akai mata Saiya masa adadinsu Dan yasan daga yau dayayi masa ta farko koma patient a asibitin Shima labarin nurse ya Kau tukuna.

Acan dakin kuwa doctors da Basu San allura ce akaiwa Fahat din ba hauka yakeyi tuburan sbd jininsa nada karfi shiyasa ma Bai sume ba yake buge bugen Daya Saka kayan dakin fara fashewa take hankalinsu ya sake tashi Dan tini yayiwa Dr Zakeer rauni dole Nurses dinsu Maza hudu suka Saka karfi aka dauresa a gado da belt cikin sauri aka dauko allura Aka lafta masa akan Wadda take jikinsa wannan Karan take ya sume sbd a cikin qasa da awa Daya an masa allura biyu duk karfin jini bazai dauka ba.

Siddeeq da ma'aikatan da aka kawo tini suka fice da thprint din,

Siddeeq Bai sanar da JAMAAL din Ameenatou na office dinsa ba ya wuce,
Shi kuwa kwata kwata Bai nemanta ba sbd sanin tana gurin sister Ashley Dan ganinta zai iya Saka jinin babansa Dake yawo a jikinsa yaci galaba akansa ya illata Fahat din gaba Daya musamman da tsoro ya saka Fahat din fadan wai kaddara ce ta Sakasa zuwa.... adaidai lokacin ne ya banka masa Alluran wadda da sama da goma ne a gabansa zai iya banka masa su duka.

Kai tsaye office din ya nufa lokacin karfe kusan uku da mintina koina tsit Babu motsin komai Dana kowa kaman Babu abinda ya faru duk da suna can dakin da ake komai suna fama da fahat din.

Sister Ashley ta samu Ameenatou din ta sassuto batareda alluran komaiba ta Dena ihun da haukan tayi shiru a kwance Babu kuzari ko kadan a aikinta ga sanyin AC din office din Daya gama kama koina sai Kuma Taga kaman sanyin zai mata yawa sbd Babu Riga a jikinta sai black halfvest me laushi da sirkin Roba data ke Dan kame da kirjinta tinda ta zare rigar jikinta ta bayar.

Rasa abin rufa mata tayi gashi Babu ta yanda ma zata Kalli ko kofan shiga dakinsa Dake cikin gurin bare ta shiga harma Kuma ta dauko Wani abin Dan haka dole ta miqe tareda zare Ameenatou din daga jikinta ahankali ta kwantar da ita ta Dan tafiya samo abin rufeta.

Tana ficewa Ameenatou din ta sake dunqulewa guri Daya sbd baccin Daya dauketa din,

Dakin Ameenatou din ta nufa sedai kusan Babu kowa koina tsit kaman baayi komaiba.

Wata Rigan ta dauko mata ta juyo tareda rufe dakin ta zare key dinsa da baa cirewa kowanne daki key dinsa na daga waje jikin kofan maqale ta waje ake rufesu baa barin key ciki su rufe kansu a rasa tayaya zaa budesu.

Ba komai ya Sakata rufe dakin ba Dan kada Wanda ya shiga ya Gano Ameenatou din Bata dakin Dan haka ta wuce da key din zuwa office dinsa takai mata Riga.

Basu Hadu a zuwa ba Dan hanyar databi daban da Wanda ya bi sai a komawan tana dosar office ta hangesa Yana gap da Isa Shima office din Shima Dan haka ta dakata cak daga inda take batareda ta qara taku ko Dayaba tana tinanin ta isa takai din kokuwa ta juya tinda ya riga ya isa ta tabbatarda bazai taba barinta kwana babu riga jikinta ba ga wannan sanyin hakama kwata kwata Ameenatou din Bata Wani son sanyi Dan haka ko ya barta ba kayan bazata taba barinsa bacci ba.

Fasa kaiwa din tayi tana tsaye ya Saka pins na kofan ya Bude ya shige tareda rufewa batareda yasan Ameenatou din tana cikin ba.

Juyawa tayi ta koma dakinsu tana nade Rigan hannunta zuciyanta cikeda tinanin abubuwan da suka faru din Wanda kwata kwata Babu Wanda ya samu Daman magana ko tantancewa take Dr JEEY ya lalata rayuwan Fahat din cikin qanqanin lokacinda Babu Wanda yayi tinanin Fahat dayazo aiki ya koma gida da safe kafin safen ya koma patient dinsu.

****Dr Dee a Daren tin bayan ishai ya fita da takardansa ta sauyin gurin aikin harma da takardunsa da lameenu ya sanar dashi yayi magana zaa mayar masa da matsayinsa dan haka karfe goma yaje yaga wanda zaiyi aikin a gidansa dan kai masa koman dare sbd a daren zaa sauya da safe ya koma office dinsa.

Hakan ya Saka Dr Dee tin ishai Daya fita yanata Kiran BB Wanda Alh Lameenu yace shi zasu tafi tare sbd asan shine din ya Aiko.

BB Bai dauki wayar Dr Dee din ba sai kusan qarfe goman dare cikin tsananin girmamawa da bayyanarda rashin jin dadinsa yafara cewa

"Dan Allah Dr kayi hakuri wlh wayar a silent take Kuma matata ce take Labor tin magrib muna asibiti shiyasa duk ban luraba kasan yanayin dai me iyali,Dan Allah kayi hakuri."

Cikin sanyin jiki da janye rashin Jin dadin da yayi tinda dai ya samu BB din ya kira Dan haka ya sake Yana cewa

"Haba haba ba komai ai tinda uzuri ne Kuma uzurinma irin wannan babba,
I hope she's ok now?
Ta sauka Kuma??

"No tukuna dai Amma ba damuwa Ina asibitin ganinan zan hawo taxi na sameka saimu tafi motana ta tsaya dazu....

No bari kawai na biyo na daukeka mu tafi din sbd dare Yariga yayi gashi idan bamu samu ganinsa yanzu ba ganinsa gobe da safe ko Wani lokacin zaiyi wuya so muyi Savin time muje kafin dare ya sake yin sosai just send the location I will be there in no time"

Take BB ya tura masa Yana kallan yaransa Bullet Dake gefensa Yana zuqan wata fitinanniyar cocaine Dake shiga cikin tsakiyan kwakwalwan kansa tana basa wani irin cajin da ba dr Dee ba ko ubansa aka ajiye masa a gabansa zai iya illatasa dan kansa tini ya juye kaman baida cikakken hankali haka yake.

Baayi mintina arbain ba Dr Dee din ya kira BB ya sanar dashi gashi a anguwan Amma Bai gane asibitin ba gashi Babu mutane sosai bare yayi tambaya.

Parking yayi inda BB yace ya jirasa Yana duba time fuskansa a hade sbd kwata kwata komai Baya tafiya yanda yakeso din Dan kuwa kwata kwata Baya Wani fitan dare Dan girmansa da mutuncinsa harma da ayyukan gabansa dasuke da yawa da mahimmanci Dan idan ba wannan huldan Daya Saka kansa ba da yanzu Yana cikin matsayinsa hankali kwance.
Chapter 13 · 0% Book details