← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 88

Sashe 24

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daqyar ya samu jikinsa ya fara warwarewa da yamman ranar Wanda ya basa Daman Kiran sister Ashley da kansa yaji jikinta.

Ta basa tabbacin da sauki sosai,
Abubuwan buqatansu kawai ya Saka Siddeeq tura mata kudi masu yawa akan tayi musu ko online shopping ne da abinda duka rashin lafiyan ko jinyar zata buqata.

Da daddare sallan ishai kadai yayi ya fito cikin doguwar Riga milk me kyau da tsada,
Kallo Daya zakai masa kasan jinya yayi sbd fuskansa ta nuna hakama yanayin kuzarinsa duk da ya boye Hakan sosai.

Siddeeq ne a mota Yana jiran fitowansa Dan haka Yana fitowa ya shiga motan shikuma ya tayar suka fice zuwa asibiti.

****Ameenatou kuwa tin jiyan yanda aka daukota daga dakinsa kusan Hakan take har lokacin Babu wani kuzari ko motsin kirki,

Ta illatu sosai sbd Bata taba dandana azaba da wahala irin wannan ba tin a lafiyanta har yanzu da batada lafiyan,
Idanuwanta sunyi zuru zuru sun fada sosai kaman wadda tai jinyar wata,
Zazzabin jikinta sosai yaqi sakinta har lokacin jikinta dumi ne dashi.

Tea kadai take iya Sha Wanda sister Ashley ke iya lallabawa tana Bata sbd takasa cin kowanne irin abinci.

Tin jiyan sister Ashley duk yanda zatai ta Hana kowa gane akwai ma rashin lafiya jikin Ameenatou din tayi ta Hana,
Hakama duk iya kokarinta na ganin ta kula da ita akan abinda ya farun tana yinsa Dan haka ne ma yasa Ameenatou din tayi Dan Dama dama hakama ba Ameenatou kadai ba a yanzu itama batason kusancin JEEY din da ita sbd tasan zaiyi wuya Ameenatou Bata fara tsoronsa ba daga yanxu din.

Da daddaren ruwan zafi ta shigar da ita sukai gashi kafin akayo wanka suka fito ta zaunar da ita bayan sun Tako ahankali daqyar sbd raunin Ameenatou din,
Goge mata jikinta tayi tareda shafa mata Dan body mist kawai ta Saka mata kayan bacci masu Dan kauri sosai riga da wandon ta Bata maganinta Wanda taqi Sha Sam Saida tai mata dabara kafin Tasha.

Qamshinsa ne ya fara yi musu ison zuwansa kafin aka Bude kofan dakin Kai tsaye ya shigo cikin nutsuwa, idanuwansa masu haske da se ayau suka dawo daidai sbd ciwo ya saukesu akanta tareda zuba mata su yana takowa zuwa cikin dakin.

Ameenatou Bata gansaba sbd idanuwanta a rufe suke tana kwance bacci ya Dan fara daukanta,

Tsayawa yayi a kanta cikin nutsuwa da Kwanciyar hankali yayiwa fuskanta kallan seconds kafin ya waiwayo sister Ashley a natse ya Bude Baki suka gaisa Yana sake tambayar jikin Ameenatou tareda Jin idan Babu matsalan komai.

Babu matsala ya sanar masa bayan rashin kuzari datake fama dashi sai stitches nata datake kukansu koyaushe Amma Suma zasu dauko hanyar warkewa inshallah.

Numfashi me sanyi mara sauti ya sauke ahankali kafin ya daga hannunsa Daya ya Dora a goshinta cikin sanyayyar kulawa ya rankwafo zai sake Jin jikin nata Dan Bata nasa treatment din da kulawanda Bai samu Daman bataba sai kawai ta bude idanuwanta ahankali akan fuskansa.

Zuba masa su tayi tana kallansa kaman Bata ganesa ba na tsawon seconds kaman yanda Shima yake kallanta cikin sanyi da tausayi me karfi,

Kaman ana tantance mata Kamanninsa Haka ta qare masa kallo tas take komai ya dawo mata na azaban datasha a hannunsa take tayi wani mummunan firgita tana fasa kuka me karfi tana Jan jikinta zuwa Baya Amma Batada karfin sosai hakama ko ihun bame irin karfin Nan ne ba sbd batada kuzarinta Bai dawoba,

Kuka takeyi jikinta na daukan rawa tareda rintse idanuwanta gam gama tana miqawa sister Ashley hannu idanuwanta a rufe tana cewa

"Ameenatou batason Haroon,
Ameenatou batason Haroon
Sister Ashley takeso,
Sister Ashley Ameenatou takeso, batason kowa"

Lumshe idanuwansa yayi ahankali ya Budesu akanta suna Dan sauyawa ya Kalli yanda jikinta ke rawa sosai tana miqawa Ashely hannuwanta ido a rufe gamgam batako son ganinsa ko kadan.

Hannuwansa ya miqa ya kama nata din duka biyu tareda matsowa zai kusantu da ita sosai Dan rarrashinta
Harta kama hannunsa gamgam ido rufe a tinanin na Ashley ne sai Kuma ta Bude ido Taga shine a kusa da ita kaman zai dawo da Baya ya goge mata wannan memory din ta fizge hannuwanta da sauri tana kokarin saukowa gadon da kanta kaman zata kife,

Da sauri sister Ashley ta matso Shima Yana tareta ya janye Yana bawa sister Ashley Daman rungumeta da sauri tana shafa bayanta tana rarrashinta tareda ambatar sunanta sbd rikicewa da lafiyanta ke Neman yi musu Dan juyewan kan tini yafara motsawa duk da yanzu wautan da dabiun kaman na yara ne ya rage ta Dena haukan Nan tuburan datake a Baya Wanda Hakan alamace ta treatment din da JEEY din yake Bata Yana aiki.

Duk yanda sister Ashley taso ta koma daidai Qi lamarin yayi sbd ganin JEEY din a gurin ya haukatata gaba Daya kuka da rawan jikin sai karuwa yakeyi har tana Wani jijjiga dole ya tafi yabarsu Yana Jin Dan Kwanciyar hankalin ganin ta samu Dan sauki a jikin.

Yana fitowa harya bar block din Yana Jin sautin kukanta Dan haka Yana fita ya rubuta magani ya saka siddeeq yaje ya siyo a Wani pharmacy da maganinsu kadai yake amfani dashi indai Yana Nigeria,

Kiran sister Ashley yayi ya Bata sbd a bawa Ameenatou din zata Fi samun kuzarinta ya dawo dakuma saurin samun saukin stitches din.

Sbd Shima ba Wani dawowa daidai yayi ba ba a asibitin ya kwana ba gida suka koma yasha magani Shima yayi wanka ya kwanta Dan ba laifi ya warware ta nasa bangaren sedai Dan abinda baa rasaba.

***Washe gari dayake Monday ce akwai aiki Amma Bai shiga ba sai guraren goma da Mintina Kuma Kai tsaye dakinta ya fara zuwa Dan har Wasu likitan ya dubata Kuma ana samun sauki akan maganin da dr JEEY ya Dorata Dan haka duka dai abinda ya kamata doctors suyi sunyi sun tafiyarsu batareda sun lura ko fahimtar wani abu datake ciki ba sbd abune da Babuma rashin hankalin da zaisaka ayi tinaninsa ga patient din dayake rayuwa cikin asibitin mahaukata.

Har bacci yafara daukanta tana ganinsa ta rikice gabaki Daya jikinta na rawa dole ya tafiyarsa yabarta Daman ganin nata kadai yake buqatan Kuma Yaga saukin dayake fatan ganin duk da radadin Hakan yakeji da tausayinta me tsananin Dake cinsa Dan ya tabbata azaban datasha ne a hannunsa ya Saka take gudunsa.

Sister Ashley da qyar da hadawa da allura tukuna ta Samu tayi bacci daga firgitan datai na ganinsa.

Harya wuni yabar asibitin Bai sake zuwa ta gansa ba bare ta shiga tashin hankalin sedai wayarsa kusan uku da Ashley kafin ya tafi gida.

Washe gari ma Hakan ce ya faru fiyema da Baya Dan kuwa ko sunansa yanzu sister Ashley ta ambata ta ringa maimaita "Ameenatou batason Haroon,batason ganinsa"

Hakan ba qaramin Sosa ransa yakeyiba da radadi Amma duba da yanda take jinyar cikin azaba ya Saka tausayinta fin Jin radadin yawa,

Sosai take cikin azaban stitches dinta sbd rashin cikakken hankali da firgitan datake yi yanzu sosai a cikin bacci sbd wannan lamarin Daya faru tsakaninsu da yanda Bata duba Dinkin dayake jikinta take fisge fisge ya Saka Dinkin yake wahalarda ita sosai sedai Kuma duk da Hakan yafara warkewa sosai hakama zazzabi da ciwon jikin datake yi me tsanani na muguwar rungumar data Sha a gurinsa ya kusan karyata Allah ne ya Hana Hakan.
#MAMUH#
#THE SEELAHS
#JDENS
#LOVE
#ROMANCE

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[29/05, 10:07 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
83
Cikin satin biyu Ameenatou ta warke sosai ta dawo daidai Babu sauran ciwo ko azaban dinki komai ya warke sister Ashley tayi iya kokarinta na ganin Hakan Dan kuwa kulawan data samu da tattali daga gareta ko mahaifiyarta data haifeta ce a raye ko Dadah iya abinda zasu mata kenan Dan haka ta warke fes cikeda kulawa da gyara me kyau na gaskia.

Ameenatou din ta koma Yan qananun rigimarta tini ta manta da abinda ya faru sedai tana ganinsa zata fara cewa

"Ameenatou batason Haroon" hakama Bata qara zuwa gurinsa ba Koda da riqe hannunsa ne kuwa daga nesa nesa take daga masa hannu da rigima suke rabuwa duk suka Hadu.

Ta nasa bangaren Shima tini ya warke ya koma JAMAAL dinsa Dan kuwa yanzu wata sabuwar nutsuwa ce da Kwanciyar hankali suka shigesa Baya Wani damuwa da Rigimanta idan tana cewa batason Haroon tinda dai ya samu rigimar tafara ragewa Bata firgita idan ta gansa sedai Kuma Bata yadda yazo kusa da ita.

Sister Ashley itama gudun da Ameenatou takewa Dr JEEY din dadi yayi mata sosai sbd ta Hakan ne zasu huta Babu abinda zai sake faruwa Dan kuwa tashin hankali ne mummuna a gabansu idan Hakan taci gaba da faruwa anan din wani abin ya biyo Baya Dan daman ko kadam batason wannan maqalewan da ameenatou ke masa tin farko sbd gudun irin hakan amma gashinan saida me afkuwa ta afku dan haka take fatan lamarin ya tsaya iya nan kenan shiyasa tana ganin tafara gudu da tsoronsa hankalinta ya kwanta.

Shi kansa a nasa bangaren yanajin ciwon gudunsa datakeyi fiyeda komai Amma Kuma Shima ya zabi Hakan tareda Jin Kwanciyar hankali da hakan sbd toshe yiyuwar faruwar Wani abin dan ko yanzu yanajin daci da takaicin Daya bari Hakan ta faru dasu batareda akwai alaqa me sunan data wuce kalman aure a tsakaninsu ba.

******Kusan kwanaki sun sake ja yanzu Shima janyewa yakeyi daga garesu Dan kaucewa damuwa duk da sosai yakeson ganinta Dan kewan rigima da fitinarta Amma dai ya dakewa Hakan sbd abubuwa da yawa.
Chapter 24 · 0% Book details