← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 88

Sashe 42

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafiz ma kuka yakeyi sosai kaman qaramin yaro sbd dawowanta daidai sai yanzu ne zasu koka rashin Dan uwansu da sukai Abdul.

Dadah ma kukan takeyi an rasa me magana a cikinsu Daren tsit hakama gidan tsit sannan dakin ma tsit sheshekan kukansu ne ke tashi kowannensu zuciyarsa kaman zata mutu sbd radadi da Kuna tareda damuwanda basusan Yaya zasuyi ba Kokuma ta ina zasu fuskanci rayuwa yanzu.

Kukanta yafi na kowannensu tsananin radadi da azabar zuciya sbd batasan ma Me ake nufi da duka bayanan da akeyiba abinda ta sani kawai shine Haroon ya rasu hakama Yaya Abdul to Amma a Ina ta samo cikin jikinta?
Aure Akai mata da wani batareda tana cikin hankalin kanta ba.........

Fashewan ruwan nakuda ne masu karfi ya Saka dukkaninsu dago jajayen idanuwansu suna kallan ruwan dayake gangarowa daga karkashinta.

Dadah na ganin Hakan tayo kanta sedai Kuma take azabbiyar ciwon mara ta tinkarota gadan gadan cikin tsananin ciwo da azaba ta dago jajayen idanuwanta ta Kalli dadah Dake tambayarta nakuda ta taso ne?.

Fitowa su babbah sukai daga dakin sbd sosai nakudar ta taso mata me azabar radadi.

Rikicewa Dadah ke Neman yi Amma sbd dare ne dole ta nutsu tafara taimaka mata tinda Babu Daman zuwa asibiti yanzu hakama Babu Daman Kiran Mai Taimkawan.

Cikin qanqanin lokaci Ameenatou tafara ficewa hayyacinta sbd azaba da wahala,

Hafiz kuwa sai duba wayarsa yakeyi Yan fatan gari ya waye da wuri ya fita Neman kudi kafin a haihun Babu komai na abinci Kokuma abin Sha a gidan bare kudin siyan magani.

Babbah kuwa gabaki Daya fita hayyacinsa yake Neman yi da ciwon kirji ya taso masa sosai sbd ranar yau din tana dawo masa da tinanin komai na ranar da Aminatunsa take nakudar haihuwan Ameenatoun Kuma a ranar ne ya rasata rashi na har abada.

Nakudarta tayi nauyi sosai Dan haka tafara gabalaita karfinta yafara karewa daqyar suka samu Safiya tayi Hafiz ya fita jiki na rawa zuciya ba kwari Neman abinda zai samo ya kawo ko asibiti ne sai atafi akaita.

Yana fita Dadah dataga tana Neman rasa 'yarta fita tayi hayyacinta ga hadari me tsanani ya Hadu ana kokarin fara yayyafi ta fita ta Nemo Hafsatu me karban haihuwa Dake maqota dasu.
#MAMUH
[29/05, 10:07 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
99

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

************
*_Three years later_*
A natse take saukowa daga stairs tana Saka wayar hannunta cikin tsadaddiyar Lv handbag dinta datake hannunta sbd lokacin ne ta kunna wayar batareda ta tsaya duba sakwannin da zasu shigo ba Kokuma kira duk da Babu wani Wanda zai kirata a daidai wannan lokacin sbd lokacin hutunta ne idan ba irin yanzu da dole take butqan fita Office ko final exams dinta datakeyi.

Sanye take da doguwan rigan Abions black kala data fito da haskenta sosai tareda sauyinta daga Ameenatou Babbah zuwa AM JADEN datake amsawa a yanzu Dan duk Wanda ya Santa France din da AM Jden ya Santa.

Lafe rigar take a jikinta batareda ta matse ta ba daidai shape dinta,
Versace silk scarf ne a kanta daure sai agogon kawai da takarman jimmy choo,
Fuskanta Wani irin haske da glowing yakeyi na asalin Hutu,Jin dadi, Kwanciyar hankali tareda Arziki Daya ratsata,
Karatunta ne kadai damuwan datake gabanta a yanzu,
Batada damuwa ko kunci ko Wani abu rashi,
Arfat shine hasken idaniyarta Kuma hasken zucuyarta fiyeda komai,
Tana masa Wani irin tsananin so Mai cikeda tsananin tausayin rashin sanin Asalin mahaifinsa,

A farko tashiga depression,
Ta shiga hauka,tashiga masiffen tashin hankali da damuwa da qunci me tsananin zurfi akan halinda ta tsinci kanta na haihuwar 'dan da batasan da cikinsa ba,batasan waye ubansa ba,
Batasan ya Akai ta samesaba.,

Amma familynta,ahalinta,iyayenta,danginta abin alfaharinta sun taru sun hada karfin zuciyarsu da karfin tsananin son da suke mata sun hanata shiga dawwamammiyar haukan da zata mayar da ita mahaukaciyar data fito,

Sun tsayu sunyi yaqi da Hakan soyayyarsu ta rinjayi mummunan qaddarar dataso afka mata ta dawo daidai,
Sune suka nuna mata ARFAT a yanzu shine dukkanin abinda suke tsananin so da kauna tareda buqata Dan haka itama Hakan ya zauna ranta batada kaman 'danta,
Tana sonsa,Dad Omar Yana tsananin sonta da ARFAT fiyeda duka abinda ya mallaka a rayuwarsa Shima,

Babbah Yana musu Wani irin tsaftacciyar kauna da so Dan bayama Tina ARFAT baida Uba,tini ya kashe ya binne zancen a zuciya da rayuwarsa kaman yanda kowa yayi Hakan,

Hafiz shine Uba,uncle,Yaya,Aboki Kuma Abokin wasansa,
Yanawa Arfat Wani irin so dayake Jin tamkar shine ya haifesa,Jinsa yakeyi kaman tsatsonsa,
Bai hada mahimmancin duk wani abu Daya shafi Arfat da komaiba,
Dan kusan Hakan ne ya Saka duka tsaddadun designers na kayan dayake sakawa harma Dana amfaninsa kusan set ne na father and son Dan haka kusancinsu na musamman ne,

Ta bangaren Mom Nur da aunt Didi kuwa kwata kwata basa wasa da duk lamarinsa hakama komai yakeso a gidan shi akeyi baa barinsa Kuka baa barinsa duk abinda zai ji masa ciwo,

Fatmah ma sosai take Ji dashi duk da Bata cika son Yara ba Amma Kuma Arfat na musamman ne hakama a yanzu indai a karkashin Dad Jden kake to so da kaunar Ameenatou da Arfat tamkar dole ne Kokuma ace farilla ne Dan haka suka Bada himmar sonsu Babu kakkautawa duk da lokutan da dama tsananin kishi da qyashin Ameenatou da Arfat Yana cin zuciyar Fatmah din Amma Didi na mata nasihar karma ta yadda ta bari shedan da son zuciya ya rinjayeta sbd Sune tsawon shekaru suke cikin daular dukiyar Dad Omar jden din suna rayuwarda bazaka taba cewan su din ba asalin jininsa bane kuma baitaba damuwa ba saima sake sakar musu da dukiya akeyi suna yanda sukeso amma 'yarsa ta cikinsa tana can cikin ukuba da masifar data Kaita harga samun haihuwar 'da mara Uba sai yanzu ta samu shiga rayuwar mahaifinta dan yana bayyanarda sonta da 'danta fiyeda komai shine zataji haushi.

Wannan maganar ce take Dan danne Fatmah wasu lokutan da dama Amma Kuma zafi da kishin Hakan Yana cikin ranta sbd kusan a yanzu kowa girma da matsayin dayake bawa AM daban dana kowa,daga Dad omar din da kansa sai kuwa ita da 'danta kafinma ita mata daddy din wato Ahmed ya biyo baya,
Hakama tsananin son da daddy Ahmed yake yiwa Ameenatou da Arfat ganin takeyi kaman ita yarsa ma baya mata irinsa sannan duk yawon kasashen datakeyi ta kasa tsaya guri Daya tayi karatu gashinan daga zuwan Ameenatou din ta tsayu su Dad din sun tsayu,su Babbah ma sun dage sun tsayu tayi karatu gashinan tana kokarin gamawa daga wannan exams din datakeyi hakama tini tafara shiga office a matsayin 'ya Kuma Magajiyar Jden Daya kwal ita da 'danta.

Dadah tinda Taga basuda ranar komawa zama ne shikenan Dan haka dole ta sake jikinta ta karbi rayuwar hannu bibbiyu Dan Babbah tini ya ware ya zama lafiyayyan dattijon da Hutu da Arziki yake ratsawan,

Hakama ganin 'yayanta Ameenatou da Hafiz sun samu rayuwar datake musu fatan samu ta wadataccen ilimin da Jin dadi tareda arziki tini taji ha kalinta ya qara Kwanciya dan haka batada wani aiki saina hutu da hutu itama saikuma na rigima da qiriniyar ARFAT.

Arfat lafiyayyan yaro ne Daya taso da karfinsa Da Dan jikinsa bulbul Babu wani nakasa ko ciwon komai a tattare dashi bayan na mura dayake yi wasu lokutan musamman idan ya shiga Rana ya Dan yi ko awa Daya haka a ciki to jikinsa Bata dauka take zai fara ciwo da rashin lafiya,

Da farko sunji tsoron yanda Allah yayi SA bature sosai Dan kuwa kusan kullum sake zama bature yakeyi sbd yanayin haskensa Daya zarce na Momma dinsa sosai hakama gashin kansa sosai yake gashi me santsi shiyas baa Wani bari Akai Akai Uncle Hafiz dinsa yake masa aski,

Ta bangare Daya Kuma idanuwansa da suke Wani irin kala dasu kaman blue kaman green sune suke bawa Dad omar shakka da tsoro sbd idanuwansa koyaushe kama suke masa da idanuwan daya sani amma ya kasa tina na waye.

Su kuwa su Babbah ko kamanninsa basa son tsayawa tantancewa sbd a zahirance Babu amfani ko buqatan Hakan tinda dai sune suke Haifa abunsu,
A gabansu Ameenatou ta haifar musu shi Dan haka Babu zancen sauya musu Akai Arfat dinsu koyayane kamanninsa sonsa a jininsu yake.

A cikin shekaru ukun Nan komai na rayuwarsu Babu Wanda bai canza ba,
Cimarsu, rayuwarsu, yanayin jiki da halittarsu harma da halayya sbd ita rayuwan Hutu,Jin dadi Kwanciyar hankali da daula tareda ilimi da wayewa ta dabance Dan haka Babu Wanda sauya me girma Bai samu ba a rayuwarsa.

Hafiz ya bude sosai geamin da tsananin hutun Daya ratsashi da ilimi,yayi haskenda zaka dauka shi kansa halfcst ne dan haka kallo daya bazaka gane shi din bane.

***********
Qarasa saukowa tayi daga saman tana kokarin nufar dining room Dadah ce t fito daga hanyar lafiyayyar kitchen dinsu da Babu abinda Babu na buqata hannunta dauke da tray me dauke da transparent bowl na glass an yanko fruits an zuba condensed milk da Madaran gari sosai Akai ta Kalli Ameenatoun fuskanta a sake da kulawa sosai tace

"Zaki fita ne batareda kinyi breakfast ba??

Ajiye handbag din hannunta tayi tana cewa

"No, Dadah Ina sauri ne 10 zan shiga exams yanzu Kuma is after 9 Ina buqatan Isa da wuri,
Ina Babbah ya tashi kuwa?

Wucewa Dadah tayi ta Isa dining ta ajiye tray din hannunta tana cewa
Chapter 42 · 0% Book details