← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 88

Sashe 34

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanuwan md Dana Dr Ibrahim da Charles akan Ameenatou da yanda zatai reacting idan Taga su babban duka suke zuciyarsu a Dan rikice da fargaba Dan Hakan ne ma Dr Zakeer yayi saurin sallaman sister fareeda din yace ta tafi sbd Yana bayansu tana  ficewa ya rufe office din Yana dawowa gaban Ameenatou din daga bayanta dayake Yana kallanta lokacin ne ta dago kanta fuskanta a rame idanuwa duk sun fada ta narke idanuwanta Dan yiwa Ashley kukan barinta datai.

Babbah,Hafiz da Dadah kuwa idanuwansu kaman zasu fado kasa sbd fitowa da gwalo mata su da sukai suna kalla hankali tashe da Kuma tsananin kewa da kaunarta me karfin gaske Dake azabtar dasu na rashinta.

Akan fuskan Babbah idanuwanta suka fara sauka ta tsaya cak daga Jan numfashin kuka datake Shirin yiwa Ashley.

Ko kyaftawa idanuwanta kasawa sukai ahakan ta maidasu akan Hafiz tana kalla,

Rawa jikinta yafara yi ahankali Yana qaruwa hakama ta kasa ko kyafta idanuwanta daga kansu.

Babbah ne ya taso da sauri ya tsaya gabanta cikin rawar murya da Mummunan karyewa da zuciyarsa keyi ya Bude Baki yace

"Budurwan Babbah??,
Babbanki ne,tareda Hafiz dinki
Ga Kuma dadanki......

Katsesa tayi cikin rawar da hannuwanta ke qarawa da Bude Baki cikin Wani sauti mara fita sosai ta furta

"Babbah,Babbah,
Ameenatou tanada Babbah,
Ameenatou tanason Babbah,
Ameenatou na son babbah...."

Wata shegiyar ajiyar zuciya su Dr ibrahim suka sauke gabaki dayansu a fili sbd tashin hankalinsu Daya fada lokaci Daya da jin kalamanta Dan kuwa shikenan ba matsalan tafiya da ita Dan Daman tashin hankalin da zaa zuba sukaiwa tsit cikin zufan tashin hankali.

Sake jero ajiyan zuciya md keyi Yana share zufa hakama Dr Charles,
Dr ibrahim kuwa a fili ya bayyanarda farin cikinsa Yana tayasu murna gabaki dayansu harsu Babban.

Su kuwa su Babbah jikinsu ne yayi mummunan sanyi da karyewan zuciya akan ganin Ameenatou dinsu da gaske dai ta koma Hakan.

Dadah kasa riqe hawayenta tayi ta fasa kuka ahankali mara sauti sosai tana tasowa ta nufo Ameenatou din Amma ko tabata bataiba tayi Baya tana girgiza Kai cikin sanyi na rashin kuzarinta tace

"Ameenatou batason kowa Ashley da JAMAAL Haroon da Babbah takeso"

Qarasawa tayi tana kallan Babbah da har lokacin shine a cikin ido da zuciyarta,
Jamaal take Gani da Ashley sai shi da hotonsa ya jima tin farko a cikin zuci da idonta harma da tinaninta Bata taba ganinsa ba a zahiran sai yau Amma Tsaf sunansa a bakinta yake.

Hafiz ne ya taso Shima ya tsaya gabanta tareda Kai hannu zai tabata ta turesa tana komawa bayan Babbah tana girgiza Kai a kasalance.

Kasa magana Babbah yayi sbd nauyi da radadin da zuciyarsa keyi,
Kirjinsa ma yaji yayi nauyi numfashinsa na Neman rokarewa Amma sbd kada a samu matsalan tafiyan tasu da ita saiya daure kawai Yana juyowa gurin su Dr Zakeer aka qarasa rubuce rubucen da zaayi aka Saka hannu da sunansa da komai ya Basu photography na id card nasa Dana Hafiz tukuna sukai sallama suka basa Ameenatou wadda take gefen Babbah kaman ba itaba.

Da farko kin tafiya tayi duk da Babbah ne yake riqe da hannunta da kansa Amma ta tsaya tareda maqalewa bazata ba gurin Ashley takeso.

Cikin mamaki suka kalleta dukkaninsu hadda su Dr kowa Saida ya shiga firgici harsu Babbah din.

Da sauri Dr Zakeer ya matso Yana kallanta cikin kulawa da tausasawa yace

"Ameenatou zata gurin sister Ashley ko??

Gyada Kai tayi tana kallansa,

"Yawwa, to idan Ameenatou tabi su Babbah zasu Kaita gurin Ashley ne harma da Jamaal Haroon Yana can gurin Ashley suna jiran Ameenatou da Babbah"

Wani sanyayyar murmushi ta sake Jin hadda Jamaal zata gani tareda juyowa ta Kalli fuskan Babbah Wanda ya rasa ya zaiyi bayan gyada mata Kai alaman Hakan ne.

Wani murmushin me Fadi ta sake sakewa tana kama hannun babban Daya sake miqa mata suka nufi kofa Dr Ibrahim da sauri ya bude musu yana musu a sauka lafiya.

Har gate Dr ibrahim da Zakeer suka rakosu suka fice Ameenatou na riqe da hannun Babbah gam kaman shine Jamaal din datake ta nanatawa da Ashley,

Duk lokacinda ta ambaci kalman Jamaal da baimasan ta inda ta gansa ba harta riqe sunansa Wani radadi yakeji sedai Kuma idan ta ambaci Haroon a karshen Saiya Tina waye Haroon din a gurinta ciwon yakesata cakuda sunansa Dana Dan uwansa batareda tasaniba Kokuma Bata iya Tina waye nata a cikinsu.

Har suka fito dadah hawaye takeyi tana sharewa hakama Hafiz duk karfin zuciyarsa ta namiji saida yayiwa Yar uwarsa Hawaye Dan itace kadai yar uwansa yanzu tinda Yaya Abdul ya tafi ya barsu.

Suna fitowa cikin sa'a suka samu taxi take suka fada masa inda zasu suka shiga Hafiz a gaba babbah da Dadah a Baya Ameenatou na tsakiyansu tana kallan koina idanuwa a Dan Bude sbd Bata taba fitowa waje Taga mutane haka sosai ba da hayaniya.

Park suka Isa
Hafiz ne ya biya driver kafin suka fito Kai tsaye motar lokoja suka shiga.

Tsananin Hayaniya da tarin mutanen da Bata taba Gani ba ya Saka kanta Wani irin daukan nauyi Yana sarawa sosai
Da karfi ta riqe hannun Babbah da hannuwanta biyu tana rintse idanuwa,

Suna ganin Hakan suka lallabata suka shiga mota Allah yasa ba Jira take motarsu ta daga daga tashar zuwa inda zasu.
#MAMUH#
#THE SEELAHS
#AMEENATOU

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[29/05, 10:07 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
94

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

***********Karfe 8 na safe siddeeq yayi parking motarsu a kofar gidansu Babbah tareda fitowa motar Yana gaisawa da Jamaar dasuka tarar kofar gidan suna firar safe.

Shima fitowa yayi idanuwansa a sauye sosai sbd ciwon Kai da rashin baccin da baiyiba,

Bai iya kallansu ba ko barin Suma su Kallesa da kyau ya amsa gaisuwansu Yana wucewa gaba sedai ko kofan gidan Basu Isa ba aka sanar dasu Babu kowa a gidan.

Dakatawa yayi batareda ya juyo ba
Siddeeq ne ya juya Yana tambayarsu a natse suka basa tabbacin Babu kowa tsawon lokaci hakama gidan tini su Babbah suka siyar dashi Babu Wanda yasan inda suka koma.

Rintse idanuwansa da suka qara ja a take a gurin Jamaal yayi kalaman da ake fada suna ratsashi da radadi.

Juyowa yayi sai a lokacin ya Kalli mutanen ya bude baki yace

"Tsawon Wane lokaci suka siyar da gidan?
Babu me communicating dasu?
Waye yasan inda suka koma?
Wane anguwa a cikin Nasarawa suka koma kokuwa wane gari suka tattara suka koma??

Babu me amsar tambayarsa ko Daya sbd yanda ya jerosu a tare cikin tsananin tashin hankali da buqatan amsa kawai ya sake rudar dasu akan tambayar Amma tinda Basu da sani haka suka sanar dashi babu ko Daya.

Wani jiri ne ya dipesa sbd BP dinsa da yayi raising take,

Da sauri cikin tashin hankali siddeeq ya riqesa tareda Bude masa mota yace ya koma Amma Sam Bai yadda da Hakan ba idan ba gidan ya shiga ya Gani da idonsa cewan basa ciki ba.

Da kafa yayiwa kofar gidan bugu Daya ta Bude ya shiga gidan Kai tsaye Siddeeq na biye dashi sbd ganin Baya Wani Gani sosai zai iya faduwa,
Ga rashin lafiyansa da Bai gama warwarewaba ga tashin hankalin rashinta da rashin baccin dayake tareda shi.

Kofofin dakunan gidan ya ringa shiga Daya bayan Daya Babu komai sai qura da qadangaru.

Rintse ido yayi Yana yiwa Baya kirjinsa na tsananta Wani irin nauyi da radadin da Bai taba jinsa ba a rayuwarsa,

Ina suka tafi da Ameenatou?
Ina suka boyeta?
Meyasa zasuyi masa Hakan?
Meyasa zasu dauketa batareda sani ko izininsa ba.

Siddeeq dayaga Yana Neman kasa tsayuwar da sauri ya qaraso ya kamasa suka fito ya sakashi mota sedai ko tafiyan Mintina biyu basuyiba jikinsa ya rikice da mummunan zazzabin Daya Saka har Wani rawa jikinsa yakeyi me ban tsoro.

Masaukinsu ya nufa dashi da sauri tareda Neman likita a waya Babu jimawa likitan ya iso yafara dubasa tareda basa taimakon gaggawa jikin ya Dan samu sassauci Amma ciwon Kam Yana Nan.

Ganin Hakan siddeeq ya fita bayan Jamaal din ya samu bacci ya bazama cikin mutanen dayasan dukkaninsu sunyi Hulda da muamala dasu Babbah da Hafiz harma da Marigayi Abdul ya ringa tambaya da bincike ko zai samu Wani Dan bayanin dazai taimaka musu Gano inda su babban suke Amma Sam Babu wani bayani ko kadan.

Haka ya wuni Shima a wahalce ya raba hankalinsa biyu tsakanin Jamaal dayake kwance da bincikesa.

Sai dare ya dawo ba Wani bayani Shima Bai Wani jima a zaune ba ya wuce dakinsa sbd zazzabin dayake cinsa na wahala da damuwa me tsananin gaske.

Washe gari daga shi har Jamaal acikin ciwon kowannensu ya daure suka sake bazama nema Jamaal kansa na Neman kuncewa Dan Bayan tashin Haroon dayake na mutuwa bai taba rasa abinda yakejin zai iya zauncewa ba idan ba ita din ba,
Jin yakeyi Yana zarewa daga cikin kansa,
Jin yakeyi kaman ya cinnawa koina wuta sbd rashin sanin inda take.
Chapter 34 · 0% Book details