← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 88

Sashe 32

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meya hadasu da 'yar Jaden Kuma??
Yar Jaden anmata ciki a asibitinsu ai qiyamarsu ta tsayu,
Suna baqatan bayani dai cikakke,
Idan dai yar babban ce su bincika kawai asirinsu rufe su Bata sallamarta ya tafi da ita batareda sanin cikin ba Dan tana tafiya record dinta clean zaa rubutasa Babu komai Babu matsala Dan ko zancen cikin ya bulla Babu ruwan asibitinsu lafiya kalau suka badata.

Wannan shawarar Dr Zakeer ya bada Amma suka kasa Naam da Hakan sbd tsaro Dan haka Dr ibrahim ya kirawo su Babbah suka shigo.

File dinta Dake office din md tin jiya
md din ya miqawa Dr ibrahim ya Bude Yana fara karanta informations nata Daya bayan Daya da abinda aka rubuta ya kawota asibitin da duka bayanai akan ciwonta da komai.
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[29/05, 10:07 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
89

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

************
Numfashi me zafi Dr Ibrahim ya sauke tareda dagowa ya Kalli Babbah dasuke zaune gefe cikin bada nutsuwarsa ga abinda zai tambaya da amsar zaa basa yace

"Baba kace cikakkiyar sunan 'yarka Ameenatou Omar??

"Eh hakane sunanta" Babbah ya fada cikin nutsuwa Shima.

"Kaine ka haifeta?
Menene cikakken naka sunan?

"Sunana Nuhu babbah,
Ba nine na haifeta ba Amma a hannuna aka haifeta Dani da mahaifiyarta uwarmu Daya ubanmu Daya nine Uba Kuma uwar mahaifiyarta hakama itama nine ubanta nine gatanta Dan har ayau batasan ba nine na haifetaba.

Shiru sukai dukkaninsu na seconds kafin Dr Zakeer yace ko zamu iya sheda Hakan??

Da sauri Hafiz yace "eh" Yana ciro wallet dinsa daga aljihunsa ya Ciro id cards dinta guda uku duka masu hotonta da sunanta Ameenatou Nuhu babbah ya miqa musu.

Voters card dinta ne,sai national id card,sai Kuma na exams dinta na waec datai duka suna hannunsa Daman shine ko Yaya Abdul suke ajiyewa.

Address dinsu ya tambaya suka karanto masa Ya duba na jikin id cards nata shikuma Dr ibrahim ya duba na jikin file yaga Abu Daya ne Dan komai nata Babu Wanda JEEY ya saka na Seelahs ko na Jaden duka na Nasarawa ya Saka sbd tsaro Kar asan ita wacece din nuhu babban ne kadai bai saka a sunan mahaifinta ba ya saka omar sbd bai san sunan babbah na asalinba babbah kadai yasan suna ambatarsa hakama da sunan asalin mahaifinta aka daura masa aure da ita shiyasa Kai tsaye ya Saka mata Ameenatou Omar kawai batareda ya Saka Jaden din ba.

Md Daya matsu yaji inda sunan jden ya Hadu Da wannan maganar gabaki dayanta ya jeho tasa tambayar d cewa

"Menene cikakken sunan asalin mahaifinta?
Yana raye ko ya rasu ne?

Shiru Babbah ya Dan yi kafin ya Bude Baki Kai tsaye ba shakkar komai yace

"Omar Jaden seelah ne asalin mahaifinta"

Tsit suka sake yi md yana sake goge zufan goshinsa,
Kenan Dr JEEY yar uwarsa ce shine Bai taba nunawa ba koda wasa bazaka taba cewa ma ya Santa ba bare hada family,
Duk kulawan dayake Dan nuna mata da karban case dinta da yayi duk Yana sane,
Innalillahi wainna ilaihirrajiun.

Zufa kowannensu ya sake sharewa hankali na tashi.

Dr Ibrahim ne yayi karfin halin tambayar Babbah dalilin kamuwa da ciwonta da abinda yasa duk tsawon wannan lokacin Basu taho sunzo gurinta ba.

Ahankali Babbah ya zayyano labarin da kusan kowa ya sansa A ranar daurin auren 'dan Mam Seelah yayi taccident ya rasu tareda mahaifin matarsa da uncle dinsa Alh Omar jden wanda tin da Akai accident din Babu Wanda ya sake Ji daga Omar din da ahalinsa.

Iya daga Nan labarin yake tsayawa koina batareda an Dora da sanin Ina amaryar take ba bare danginta tinda su talakawa ne baa sake tada nasu zancen ba.

Shiru kowa yayi tsit na tsawon mintina kafin md ya Kalli Babbah cikin qarfin halin da kulawa yace

"Duka bayanai gasunan munji Kuma mun fahimta sosai Amma duk da Hakan sbd tabbatarwa da gudun matsala tareda cike doka zamu baka hakuri yanzu ka tafi zuwa Nan Da kwana biyu saika dawo inshallah zamu baka damar ganinta harma fiyeda Hakan idan ka buqata"

Shiru Babbah yayi cikin nazari da tinani kafin ya dago yace

"Ba iya ganinta nazo yi ba,sallama muke so mu tafi da ita gida insha Allah zamu nema saukin daga Allah acan"

Daga md har su Dr Zakeer ajiyan zuciya me karfin gaske suka sauke a boye ta dr ibrahim CE ta fito fili sbd anzo inda yanzu Kam sukeson Azo Dan kuwa Babu Wanda ba tsoro da tashin hankali ne a ransa ba Dan alamun dai suna nunawa da gaske ita yar Jaden din ce tinawa da labaran rasuwar matarsa Da aka ringa yi a lokacin da Akai gobaran.

Wannan masifar da balain ko waye yayiwa yarinyar Nan ciki Allah ya Isa a tsakaninsu,
Dole ma suyi gaggawan binciken komai kafin jibi Babbah yazo su miqa masa yarsa su tafi tin kafin cikin Nan Daya fara fitowa ya bayyana su shiga masifar d batada kofar fita a hannun Omar Seelah.

Cikin girmamawa suka bawa Babbah tabbacin inshallah zuwa Nan da jibi yazo zasu duba su sallametan su basa ita din.

Farin ciki ne me tsananin gaske ya rufesu babban yai godiya sosai suka fito.

Suna ficewa md ya miqe Ya dauko ruwan hannuwansa na Dan rawa yakai bakinsa yasha Yana Jin zafi Tako ina,

Yau da ace sunje zubar da cikin Nan Wani abin ya biyo Baya Yaya kenan zasuyi da seelahs?
Cabdijam,
Jin yayi kwata kwata Babu abinda yakeso yanzu kaman Ameenatou tabar asibitinsu kota halin Yaya ne.

Kusan Suma su Dr Zakeer tinanin ne a ransu Dan haka take aka kira Dr Charles aka sanar dashi komai ya sauya,
Shi kansa Yana Jin Hakan ya ringa godewa Allah da matarsa Bata taba lafiyan Ameenatou din ba dan haka shi tin a cikin Daren ma ya fara tinanin Neman sauyin asibiti kawai Yama barta gaba Daya incase idan gaba tsautsayi yasa zancen ya dawo Baya.

Dr Zakeer ma fara neman yanda zaa sauya masa asibitin yayi Dan hankalinsa Kuma ya tashi akan lamarin,
Bawa Babbah ita shine rufin asirinsu  ayanzu to Amma Kuma dawowan Dr JEEY shikuma wani tashin hankalin ne daban duk da kaman yanda md ya fada bai nuna musu yar uwarsa bace koya dawo suma bazasu nuna sun saniba magana Daya iyayenta sunzo an sallameta.

Cikin farin ciki su Babbah suke sukam Dan haka a masaukinsu da suka sauka na Wani hotel suka koma a shirye tsaf da Shirin tafiya kowanne lokaci.

******Sister Ashley Dake kallan Street din gabansu tana sanarwa me taxi din idan sun samu mutane a kusa pls suyi tambaya Dan batasan gidan datazo din ba itama.

Wayarta ce tafara ringing ta Kalli Jakarta Dake kan jikinta ta Bude tareda Saka hannu ciki tana Neman wayar.

Katsewa wayar tayi Wani kirin ya sake shigowa ta fito da wayar tana kallan screen din

Bazata iya Tina lokaci mafi farin ciki a rayuwarta ba kaman yanzu da wani sanyi da farin ciki me tsananin gaske Daya cike zuciyarta ba ganin sunan Dr JAMAAL akan wayarta.

Hannunta har Wani rawa sukeyi ta dauka da sauri tana hamdala farin cikinta da mutuwar jikinta duka a bayyane.

Tana dagawa kafin tayi magana muryansa tafara Ji cikin tsananin sanyi da nutsuwa yace

"Aslm alailkm."

Amsawa tayi cikin girmamawa jikinta na sanyi da yanayinsa sedai Bata karayaba ta gaidasa.

Amsawa yayi da murya me kama da yanayi na rashin lafiya kafin da kasala yace

"I'm sorry,bazan iya magana ba ita kadai nakeson Ji,Inason Jinta,pls can you.........

Katsesa Ashley tayi da cewa

"Dr JEEY kayi hakuri Amma kana buqatan Jina tukuna,
Ameenatou na dauke d........"""dip Kiran ya katse.

Wani mummunan accident ne ya faru sakamakon motar data dakesu batareda sun San da zuwanta ba ta gefensu Wanda ya Sakasu mugun bugawa da transformer Dake gurin wuta tafara Watsi tana kokarin tashi.

Motar su BB da suka cirewa number tini tayi Baya duk da ta bugu sosai ta fashe ta gaba sbd yanda suka daki motar su Ashely din.

Reverse sukai suka bar gurin da mugun gudu goshin BB na zubar da jini sosai na buguwa Shima bullet hancinsa jinin yake zubarwa kansa na juyawa Amma haka suka tsere sedai basuyi tafiya me nisa ba suka parker motar Wani gurin da Babu mutane suka fito tareda cire komai nasu suka bankawa motar wuta sbd bazasuyi wata tafiya me tsayi ba zaa kamosu hakama sun bugu sosai Suma komai zai iya faruwa.

Mutane cikin gaggawa suka Dan taru sbd anguwan ba mutane sosai can JAMAAL ya siyawa umman gida,

Cikin gaggawa mutanen da aka samu sun shigo street din suka rufu aka motar dan taimaka musu.

Cikin yardar Allah daga Ashley har drivern Babu Wanda ya rasa ransa amma Ashley ta bugu sosai hakama bleeding takeyi sosai daga cikinta Wanda ya Saka wata nurse Dake gurin itama cewa tana tinanin cikine a jikinta Kuma Kila fita zaiyi.

Da gaggawa aka kwashesu zuwa asibiti sbd cetan ranta da abinda yake cikinta idan da akwai Rabon ya rayu.
Chapter 32 · 0% Book details