← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 88

Sashe 63

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kayan Yara ta Siya sosai tana dawowa sallah tayi ta sake wanka ta shirya tana gamawa Ariana na isowa lodge din da mota ta dauketa sai airport.

Ko awa daya bataiba a airport jirginta ya tashi tabar Madrid.

Ko data isa France safiya tayi Hafiz ne yazo daukanta tareda Arfat wanda Yana hango mommansa da Wani irin gudun gaske ya kwace daga Hafiz ya nufeta yana ambatar sunanta farin cikinsa Mai tsananin gaske Yana bayyanuwa sbd Bai taba dadewa haka batareda mommnsa ba.

Itama ware hannuwanta tayi Cikin tsananin farin Cikin da take Idanuwanta suka ciko da hawaye tana cewa

"My blue eyed champ,mommas love, honey I missed you like crazy,ohh my love......."

Daukansa tayi tayi sama dashi duk da nauyinsa tana dariya Shima dariyan yakeyi.

Hafiz daya iso gurinsu Cikin farin Cikin ganinta Shima barka da sauka yayi mata Yana kallan yar ramar datai Amma ta qara haske sosai yace

"Yau akwai turancin France a bakin babbah da Dad jden idan yaga yar budurwansa ta rame haka"

Dariya tayi Suna yin gaba tana cewa

"Allah sarki babbahna duk kun rikita masa yar budurwansa"

Dariya yayi Shima Suna isa mota ya Bude aka Saka komai nata ya Bude mata ta shige ya karbi Arfat dinsa ya Bude masa baya ya sakasa tareda Saka masa seatbelt ya rufe kofan kafin ya zagaya ya shiga lafiyayyan motar ya tayar suka bar airport din aguje.

Idan akwai abinda yafi hawan jini to siddeeq Yana cikinsa sbd mutuwan tsaye yayi na ganin babyn a tsakiyar Hafiz da AM Kuma Yana kiranta mommah idan kunnuwansa sunji masa daidai kenan.

Innalillahi wainna ilaihi rajiun""

Wannan babyn waye ne ya haifesa a kaf familyn jden shine abinda yake tsananin son sani kafin isawar da Jamaal wannan sakon da zai iya tarwatse komai,
Tukuna ma Ina aka samu jinin bature a fmlyn??
Kodai Cikin familyn asalin jdens dinne Omar jden ya dauko...

Numfashi ya sauke daqyar dole Yana buqatan sanin komai kafin barinsu AM din kasar kaman yanda JAMAAL yafa masa.

Su kuwa Kai tsaye gida suka nufa Suna isa Aunt Didi ce tafara farin Cikin ganinta sbd zata fita ne tana bakin motarta suka shigo.

Rungumeta tayi tana mata sannu da zuwa itama Cikin farin Cikin ta rungumeta tana Dan bayyanarda shagwabanta.

Wata lafiyayyan Ferrari ta Gani a harabar gidan Amma Bata damu da tambayar ba sbd tinanin ko Dad dinta ne ya siyo sabuwan motan kokuma ta Hafiz ce.

Ciki sukayo Arfat har lokacin Yana maqale da ita a hannunta babbah bayanan shi da dadah Dan haka Kai tsaye palon Dad dinta ta nufa da Arfat a hannunta Hafiz na gefenta suka shigo palon.

Dad dagowa yayi fuskansa cikeda farin Ciki ya kalleta Yana ware mata hannuwansa ta taho har Arfat din suka shige jininsa sai alokacin ta lura d JAMAAL SEELAH dayake zaune tareda Dad din batareda y dago ya kalletaba waya yake amsawa a Cikin wata irin nutsuwa da kamewan data sakata dauke nata Idanuwan daga kansa
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[29/05, 10:08 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
107

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

*************
Da daddare gurin Dad dinta da Mum Nur tayi dinner tareda su sbd haka take rabawa Dad dinta da su babbah kanta kowa tana tsananin sonsa tana kokarin basa time dinta da kulawanta yanda ya kamata sbd dukkaninsu ta rasa wanda ya fi sonta tsakanin Dad dinta da babbah.

Ko da suka gama dinner tin a Nan dining Arfat yayi bacci Dan haka Sarrah ta kira ta daukesa daga jikin Dad ta nufi sama dashi Dan masa wanka da Shirin bacci.

Itama bata Wani ci sosai ba sbd abincin Rana ya kama cikinsu sosai Dan haka itace ta fara tashi ta tafi har gefen Dad dinta inda yake zaune tai masa goodnight ta juya tayiwa Mum Nur hakama Uncle Ahmed kafin ta wuce tabar gurin sbd Didi batanan Fatmah ma Kuma haryanzu babu Wani shakuwa a tsakaninsu, da Arry ne ta Saba sosai har take wasa da shi sosai.

Tana zuwa daki toilet ta wuce tayi brush tareda wanke fuska da hannuwa ta fito tana goge fuskanta da towel ta sauya kaya zuwa kayan bacci masu kauri Riga da wando sbd tana wanka ne ta sauka dinner,

Face dinta ta zauna gaban mirror ta goge da cleanser din La Roche posay tana gamawa ta haye lafiyayyan gadonta tareda kashe wuta ta shige bargon da Arfat yake Ciki Yana baccinsa Cikin nutsuwa Yana fidda Wani sayayyan kamshi me dadi Dan baa masa wasa da qamshi ko kadan.

Addua tayi musu tareda shigewa jikin 'danta tana lumshe Idanuwanta.

Washe gari tin a gurin breakfast kowa na kan table Dad ya sanarda kowa yafara shirinsa sbd sati uku masu zuwa zasu tafi Nigeria din Dan haka kowa saiya fara tattara shirinsa da ayyukan gabansa.

Hakan shine ya Saka zuciyar AM shiga Wani irin sanyi da daci lokaci daya sbd abubuwa datake son ta isa Nigeria din tayi da kanta wanda ba komai bane Neman sister Ashley.

Hafiz ma hakan Yana daya daga Cikin burikansa na son komawa Nigeria Dan haka yaji dadin hakan sbd a yanzu basuda Wani fargaba ko shiga damuwan komawa Nigeria sbd sunyi tsayuwan da bazasu taba tabuwa ga kowa ba,

Shi kansa babbah daman hakan yake jira a koma Nigeria din su huta da Wani boye boye ko yawon gudun kowanne Jan wuyan.

Dadah kuwa tafi kowa ma farin Ciki Dan ita Kam daman koyaushe fatanta yaushe zasu Nigeria din.

Mum Nur ce ma ta Dan ji kaman bazata iya zaman Nigeria din na Amma Kuma duban familyn nasu duka Suna tare zasu zauna a guri daya ne kaman Nan din sai taji qwarin gwiwa da nutsuwan tafiyan.

Fatmah kuwa so tayi abarta ta koma Poland da karatu sbd abinda yake maqale a zuciyarta na ganin wanda zata iya rabuwa da gidansu da qasarta ta koma qasarsa karatu Dan kawai samarwa zuciyarta nutsuwa da ganinsa kadaima.

Dad Omar ne Kai tsaye da kansa ya Hana hakan yace duka Nigeria zasu dawo bazai taba barinta zuwa Poland ba Wani Sabon karatun itama suje kawai aikin zata fara gaba dayansu har AM da Hafiz da ita tare zasu fara shiga office kowa da babban matsayinsa.

Wannan hukuncin na Dad Omar ya Saka zuciyar Fatmah din shiga damuwa Mai tsananin gaske da shakkar ta inda zata fara Amma koma dai yayane Taga Dr JAMAAL SEELAH din datake ji a bakinsu Dad din Kuma a kallo daya ta mace akansa Dan haka bazata iya auren kowanne namiji a rayuwanta ba idan ba JEEY SEELAH ba a duk inda take kuwa.

Shirin dawowa duk wanda yake gidan yafara kowa na kokarin kammala ayyukan dayake dasu a qasar da huldodinsa,
Fatmah ma shirinta takeyi tareda fita kullum Bata wuni gida tana tareda wasu friends dinta guda biyu da koyaushe Suna tare Suna yawon bankwana duk da bawai an rabu dinne ba Dan zata ringa yawon kasashe kaman yanda ta Saba.

AM school dinsu Arfat ta tafi da Dad dinta da kansa sukai bayanin komai tareda karban masa takardunsa via email suka baro school din.

Tin kafin su isa aka Saka a samarwa Arfat best school a Lagos da tsarin gidansu ma dayake kwata kwata ba anguwa daya da seelahs ba tini aka hai gyaransa da tsarinsa kaman na turai daidai da yanda aka San zasu iya rayuwa aciki musamman sbd Arfat da Mum Nur da Arry sai Fatmah da kwata kwata Basu taba sabawa da Nigeria ba bare Arfat da baima San inane hakan ba, Arry ma rayuwarsa kaf so daya aka taba zuwa dashi lokacin auren AM da Haroon hakama Fatmah shine zuwanta na farko da wayonta dai sedai lokacinda tana baby da iyayenta suka taho da ita dangin daddynta,
Mum Nur kuwa itama zata iya kirga zuwanta qasar sbd asalinta ba anan take ba itama,

Irin mahaukacin mansion din da aka Gina din da tsarinsa da uwar Tarin dukiyar da aka zubawa mansion din kaman baa qasarmu ba ya Saka mutane fara yada dawowan tasa Nigeria da iyalinsa,

Mam kuwa ajiyan zuciya kadai ya sauke Yana tabbtarda idan Bai mallaki dukiyar Omar ba kenan dai sunzo a asara sun koma a asara,
Sun dauki rayukan su kasim da Jameelu a banza,

Me hakan ke nufi?
Omar yafisu Kuma ahakan zaici gaba da finsu??
Meye amfanin rayuwar da suka zaba sbd dukiyar da haryanzu ta gagara shigowa hannunsu?
Meye sunan wannan asarar da suke kokarin tafkawa?

Ajiyan zuciya ya sauke Yana sake kallan hotinan mansion din da kudin dayake rubuce na adadin uban millions of dollars din da ake tinanin an kashe a tsarin mansion din a kiyasi ma batareda an tabbatarba Dan da alama ma sunfi hakan

Lameenu ne ya taba Tako Ina Dan kuwa shi Bai taba yadda ya tabe,
Idan dukiyar ta gagara shigowa hannunsa ta hanyar dasuka fi iyawa to kuwa zasu shiga hannunsa ta hanyar zumunci da jinin da zasu hada Dan kuwa lokaci yayi da zai bayyanarwa da duniya AM jden sirikirarsa ce 'dan cikinsa take aure,
Chapter 63 · 0% Book details