← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 88

Sashe 27

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowa yayi da ita zai kaita daki yabar asibitin sister Ashley tai knocking kofar office dinsa Yana budewa yaganta baisan lokacinda idanuwansa da sukai wani mummunan Jan tashin hankali take suka rintse ba sbd ayanzu ne lokacinda yafi buqatan sister Ashley a rayuwarsa fiyeda ko yaushe.

Hannun Ameenatou data riqesa gam ya miqawa sister Ashley din Yana Jin Wani abu me nauyi ya danne kirjinsa yace

"Ki kula da ita,Na bar miki amanarta"

Cikin tashin hankali sister Ashley ta Kallesa zatai magana Amma ganin mummunan yanayin dayake ciki ya Sakata kasawa ta kama hannun Ameenatou data kasa sakinsa duk da azabar datake ciki.

Kasa kallan Ameenatou din yayi sbd idanuwansa da bayason t Gani a yanda suka koma ya juyo tareda kama fuskanta cikin matsanancin karfin hali ya Kalli cikin tsakiyan idanuwanta yace

"Ki bi sister Ashley Zan dawo na tafi Dake I promise Ok?"

Sakinsa tayi ahankali tareda kama hannun sister Ashley din.

Sister Ashley Bata buqatan kudi Dan ko a jiya ya saka mata kudi me yawa Dan haka Saiya Isa zai sake Saka Siddeeq ya Saka mata kudi.

Key din office dinsa sister Ashley ya bawa ya shiga mota yabar asibitin tin acikin motan ya fidda wayarsa ya Siya ticket.

Cikin sa'a akwai jirgin 10 Dan haka Yana Isa gida Babu Bata lokaci ya shirya ya fita zuwa airport Yana kashe wayarsa.

Yana Isa baifi mintina 30 ba jirginsu ya tashi daga qasar Nigeria ya daga.
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[29/05, 10:07 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
86
*_AISHA's COLLECTIONs_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

************
Kwanaki nata Dan tafiya,yawan Rigiman datakeyi yanzu ya Saka take jawa kanta zazzabi suyita fama saita kwana biyu sister Ashley ta samu ta warke,

Sister Ashley tana sanar masa ko ciwon Kai Ameenatou din tayi Dan haka ya rage yawan Kiran da mugun shagawabatan dayake yi a wayar sbd bayason yawan ciwon Shima,

A nata bangaren kuwa rage yawan Kiran ya Saka ta qarasa rikicewa kullum sai anyi gama da ita ta koma kawai wata rigimammiya kullum sister Ashley cikin dawainiya da fama da ita take sai itama ta koma Abar tausayi sauran nurses kuwa duk sai suka ji basa kaunar Ameenatou din ko kulata basa iyawa kowa ya Barwa Ashley wahalarta duk da Daman Tim can itace me wahalar Amma dai idan rigimarta ta tashi kusan nurses na taruwa akanta.

Wannan rigimar tata tasaka lafiya take Neman gagararta yau lafiya gobe ciwo take tafara rama haka kawai tana Wani irin haske kaman zata koma jinjira,

Ciwo me wahala takeyi sbd sosai take laushi idan ya tashi ko motsin kirki Bata iyawa ko tayar da ita sai sister Ashley tayi,
Itama sister Ashley din yanayi na zuciya na rashin mijinta da rigimar Ameenatou din datai yawa tareda wahalar ya Sakata itama layin Ameenatou din zazzabi takeyi sosai da rashin lafiyan Dan haka suka koma dukkaninsu sai ahankali.

JAMAAL ma dole ya sake rage Kiransu sosai tinda Kiran ke Saka Ameenatou din rigima da tashin ciwon...

Wannan yasa abubuwan suka fara cabe musu Amma duk da Hakan karfin hali sister Ashley keyi sosai tana kulawa da Ameenatou Dan tafita jin jikinta sosai hakama batason asan dukkaninsu Basu da lafiya sosai irin Hakan Dan zaa iya Bata Hutu ita ace saita warke to Kuma a yanzu da Ameenatou batada lafiyan batajin tafiyanta shine maslaharsu Dan kuwa qarasa rikicewa Ameenatou din zatai.

A nasa bangaren kuwa Shima abubuwan sun tsananta Dan haka Shima suka jisa shiru ba labari kwana biyu,

Ana cikin Hakan jikin Ameenatou yaqi sauki Tako ina Sam Dan haka dole likitoci suka Maida hankali sosai akanta sbd patient din Dr JEEY ce kowa yasan tanada mahimmanci a gurinsa a asibitin dan duk yanda yakeda basarwa da kamewa duka an fahimci mahimmancinta a gurinsa Dan Yanda yake dubata daban da sauran patients hakama suna lure da kyautatawan dayake wa sister Ashley akan yanda take kulawa da ita batareda sunsan asalin alaqarsa da ita ba har yanzu din.

********Tashin farko abinda Dr Zakeer ya samu a results nata shine ya sakasa Zare farin glasses dinsa ya Ciro handkerchief dinsa ya goge glass din da kyau a natse ya sake mayarwa fuskansa ya Saka tareda sake daukan takardun ya Bude da kyau Yana sake karantawa.

Abinda ya Gani farko ya sake Gani Wani zufa na tsatsafowa daga goshinsa har tafin hannuwansa.

Baya tayi da kujeran dayake Kai ta office dinsa ya miqe tareda daukan sauran takardun ya nufi kofa ya fice zuwa office din Dr Ibrahim Yana sake dubawa da kyau Dan kada yaje aga ba Hakan bane ya zamana ya hadawa kansa masifa.

Harya Isa office din Abu Daya yake Gani ba gizo bane.

Yana zuwa office din cikin sa'a dr Charles ma Yana office din suna tattauna maganar Nurse Fahat da familynsa ke rokon a tsananta musu Neman lafiyansa,

Zufansa ya share ya iso gurinsa tareda ajiye takardun hannunsa kan table din gabansu batareda ya sake gaisawa dasu din ba bayan wadda sukai da safe da suka Hadu.

Kallan takardun sukai a tare kafin Dr Ibrahim ya dawo da kallansa kan Dr Zakeer din
Shikuwa Dr Charles takardun yake kalla har lokacin Yana Kai hannu ya dauka Yana cewa

"Menene?
Results din waye?"

Bude takardun yakeyi Yana fara karantawa.

Yana gamawa ya dago ya Kalli Dr Ibrahim Dake jiran Jin Menene kafin ya dawo da kallansa kan Dr Zakeer cikeda mamaki me girma yace

"pregna....""

Katsesa Dr Zakeer yayi da qarasa masa da cewa

"Yes,patient 6, Ameenatou Omar"

Dr Ibrahim Dake Neman shiga duhu akan rashin ganewa ne ya karbi takardun ya fara karantawa a bayyane.

Ajiye takardun yayi tareda dagowa ya Kalli Dr Zakeer cikin son Bude zancen sa kyau kan kowa ya sake yace

"Ciki ne a jikin patient dinmu?
A wannan asibitin?
A cikin asibitinmu?
Cikin haihuwa fa,
Cikin haihuwan 'dan mutum fa??ko dai na aljanu ne??
Tayaya zaa samu wannan mummunan masifar Rana tsaka a asibitin Nan??
Kun San me Hakan ke nufi??
Kunsan license dinmu ne gabaki dayanmu ya hau Wani mummunan siradi kuwa na rayuwa da mutuwa?
Kaiii innalillahi."

Dr Zakeer ma dayake cikin mummunan tashin hankalin share zufansa yayi sbd sanin Suma makomarsu irin ta dr Dee ce kenan,
Tayaya zaa samu patient dinsu da ciki?
Tayaya zata samu ciki a qarqashin kulawansu?
Me zasu fadawa Wainda suka kawota?
Me zasu fuskanta daga lokacinda zancen cikin ya fita Dan hukun Hakan me girma ne tinda mahaukata ne basa iya gane Wanda yayi musu Cikin sbd tabbas tabbas dole daga cikin ma'aikatan asibitin ne dole aka samu Wanda yake lalata patient tinda angansu Basu da hankali shiyasa ake hukunci me tsananin da zai lalata career din aikin mutum gaba Daya to su yanzu da baa San ta inda zaa San ina wannan masifar ta bullo ba.

Dr Charles daya fisu shiga shock kallan result din yayi Yana cewa

"Menene abin tsayawa fargaba da tashin hankali har Wani yasan da cikin bayan a cire mata shi asiri rufe Babu sanin kowa,
Kokuma tsayawa zamuyi tinanin abin yi har nurse dinta tasan da cikin zancen ya fita,
Kuna sane da Dr JEEY SEELAH ne ya Saka aka dauke Dr Dee daga Nan daukewan wulaqanci data Saka sa kashe kansa bayan sunansa ya gama Baci akan qwayoyin da aka samu a tareda gawarsa,
Dr JEEY na sanin maganar anyiwa wannan patient din ciki a asibitin Nan zai tabbatarda careers na mutane da dama a cikinmu sun lalace,
Ku kalla nurse Fahat Wanda bibiyan yarinyar kawai ya gwada yi Amma Ina yake yanzu???
Akwai Wanda ya Isa yayi magana akan Hakan??
Dukkaninmu munsan lafiya kalau Fahat yake Amma dare daya haukan ta samesa dole muka bi yarima muna Shan kida bare yanzu ace ciki,
Ciki na haihuwa fa??
Raping dinta fa kenan akeyi da alama ba so Daya ba akwai Wanda yake Kwanciya da ita a cikin ma'aikatanmu ko likitoci ma ko nurses ko clearners koma ward attendence duk zai iya faruwa ace Wani daga cikinmu ne."

Shiru dukkaninsu sukai kowa na shiga nazari Dan sune manyan asibitin sai md Wanda Shima dole a sanar dashi asan mafita Dan kuwa daga kan likitocinsu har asibitin gabaki dayanta zaa iya sokesu.

Dr Charles ne ya buqaci abari ya sake aunata da kansa ya Gani Dan su sake tabbatarwa kafin su Sako md acikin zancen tukuna,

Naam sukai da Hakan Dan haka aka bari aga me sakamakon ze bayar.

Babu Bata lokaci Dr Charles ya koma office dinsa yayi abinda zaiyi kafin daga baya ya nufi dakin Ameenatou din.

Koda ya Isa sister Ashley na hanyar zuwa dakin itama Dan haka cikin girmamawa ta gaidasa suna qarasawa tare Yana tambayarta jikin Ameenatou din ta amsa masa da ba laifi tana samun lafiya zazzabi ne kadai yanzu yake Sakata gaba ko ya tafi Saiya dawo.

Dan juyowa yayi ya Kalli sister Ashley din wadda itama tayi wani irin zuru zuru da ita
Yayi mata kallan mintina kafin ya dauke Kai suna shiga dakin tareda wata sister fareeda data biyo Dr din.
Chapter 27 · 0% Book details