← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 88

Sashe 8

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Numfashi ya sauke ahankali tareda qarasawa dining Bai taba komaiba kallan yanda aikin cook din yayi ya wuce kitchen ya dauko ruwan Roba Daya da milk drink me sanyi ya fito daidai fitowan JEEY Wanda qamshin Paco Rabanne ne yafara iso masa yasan ya fito Dan haka Yana ajiye kayan hannunsa kan dining ya dago idanuwansa Ya kalli hanyar bedroom din.
#MAMUH#
#JEEY SEELAH
#JAMAAL SEELAH
#DR JAMAAL JEEY MAM SEELAH
#JAMAAL
#JJ SEELAH

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
65
Sanye yake da black Dior loose fit tshirt da guntun wide leg wandon AG Shima black sai slippers Suma dai black dinne,

Kallo Daya siddeeq yayi masa yayiwa Allah godiya Daya halacci JEEY din a cikin wadatacciyar ni'iman rayuwa sbd wahalan rayuwa take zata narkar da fatar JEEY din yake Gani da a cikin marasa arziki ya fito sai gashi Allah me yi kowa a inda yaso.

Dining din ya nufo Yana kallan time din agogon palon kafin ya dawo da kallansa kan dining din.

"Barka da fitowa" siddeeq ya fada Yana komawa ya dauko masa ruwa da drinks tareda fresh tangerines masu kyau cikin bowl masu Dan sanyi ya ajiye sbd JEEY din yanada wuya yaci abinci ya gama baisha oranges ba dai tangerines din dai yafi buqata sbd ya saba ne tin yana yaro mum dinsa ce ta saba masa da hakan.

Zaunawa sukai kusan a tare Yana cewa

"An samu Wani bayani daga binciken inda su family dinta suke??"

Fara serving na abincin sukai siddeeq na cewa

"No Babu wani bayani a yanzu Amma dai na bawa Wanda zai tafi Nasarawa komai da zai ishesa ya nutsu sosai ya binciko sai aje a taho dasu.

Gyada Kai yayi ahankali cikin gamsuwa da zancen Yana daukan roban ruwa ya Bude yakai bakinsa yasha a natse batareda ya tsaya zubawa a cup ba.

Abincin da Akai ya kalla,
Penne pasta ce dataji cheese da qananun Naman Kazan broiler,

Zuba masa siddeeq yayi tareda white rice kadan ssaiya zubawa kansa White rice din da sauce din kidney dayake gurin Dan bazai iya cin cheese ma shi Kam kusan cimar JAMAAL din ya kowace iri ya kasa sabawa ko iya cinsu Dan abubuwane da Bai taso shi Kam Yana cinsu ba so bazai iya koyan cinsu lokaci Daya ba.

A natse JEEY din yake cin abincinsa siddeeq ma abincin yakeci Yana sake duba wayarsa kafin ya dago ya Kalli JEEY din yace

"Sister Ashley gobe zata bar Ward din da AM take take"

Kalman AM din da siddeeq yayi amfani da ita ne ya Dan Saka shi dakatawa daga tauna abincin dayake bakinsa na seconds kafin ya Dan dago ya Kalli siddeeq din da idanuwansa masu haske sosai tukuna yaci gaba da cin abincin bayan ya gyada Kai alaman yaji.

Siddeeq kuwa tin daga ranar da Ameenatou ta zama matar JAMAAL din Bai sake kiranta da Ameenatou din ba sbd ta zama matan maigida Kuma ubansa Dan haka AM din shine sauki saukin abinda yake kiranta.

Harsu suka gama cin abincin bayanai ne Daya bayan Daya na dukkanin abubuwansu da JEEY din ya bari yaci gaba da kulawa yake jero masa a natse tareda yanda ake kulawa dasu sosai Dan kuwa dukiyar Dad Omar din da kusan su Dad Mam Basu San da ita ba itace JAMAAL din yake kulawa da ita ya saka wainda Babu Wanda yasan dukiyar waye suke juyawa siddeeq na kulawa da sauran Wanda Hakan ya Saka siddeeq din duk da ana cikin tashe tashen hankalin nan yayi nasa kudin daidai misalin Dan kuwa harkokin na tafiya cikin nasara da yanda ake son Dan Shima siddeeq din yanada iliminsa sosai da qwarewa akan Aiki Dan nesa ba kusa ba yafi Haroon sanin aiki da kwarewa.

Suna gamawa siddeeq ne ya fita ya Siya sauran dukkanin abubuwan da JEEY din zai buqata a asibitin da zai fara shiga gobe sai dare ya dawo ya kawo masa yabar wainda zasu tafi dasu cikin mota,

Masallacin dayake gaban Houston Astrt da Dan tafiya suka tafi da mota acan sukai sallan magrib da ishai daga can ya dawo da JEEY din gida shi Kuma ya wuce nasa gidan da motarsa Daya bari gidan JEEY din.

Ya shigowa gidan Kai tsaye laptop dinsa ya kunna ya fara duba sabon reports na mum dinsa da akace an Turo masa na yau din.

Yana gama dubawa Dr Adrian ya kira suka jima suna magana akan mum din sbd saukin data fara samun shi kansa yafara basa mamaki Dan kuwa baiyi tinanin saukin zuwa haka sauri sauri ba daga bayan Nan bayan sun gama Shan wuya.

Godiya yayiwa Dr Adrian din kafin ya kashe ya kira Aunt dinsa ta bangaren mum din wadda take tareda ita itama Muslim ce Dan yanzu dangin mum din tasu ya kasu ne akwai musulmai akwai Christians Amma dai baa qyama ko gudun juna sbd sun yadda da Addinin raayi ne kowa yayi Wanda ya yadda dashi.

Ya jima Yana magana da Aunt Mariam Yana kallan Mum dinsa ta screen din laptop dinsa sbd vcall ne,

Zubawa Mum dinsa idanuwansa yayi suna Dan sauyawa Yana Jin kewanta da kaunanta me tsananin gaske Dan har yau ban dandana son datakai wadda yakewa Mum dinsa ba,

Rasuwar Dan uwansa yabar Wani mummunan gibi a rayuwarsa da har abada bazai cike ba hakama radadi ne da harya mutu bazai taba Dena Jinsa ba sedai ciwo da radadinsa ya ninku ne sbd Mum dinsa datake cikin wannan halin sbd rashin 'danta datai,

Shi kadai ne yasan irin yanda mum ke tsananin son Haroon sbd Bai rayu da ita ba,
Bai zabeta ba ya zabi Dad dinsa,
Da wannan ciwon a cikin zuciyarta take rayuwa kowace Rana,
Babu rana ko Daren da Bata kewa ko mararin son kasancewa da 'dan nata ba tin daga ranar Daya zabi zama da mahaifinsa akanta harya tafi ya barta da wannan ciwon a ranta.

A yanzu mata biyu ne a rayuwarsa masu mahimmancin da zai iya komai akansu,
Da mahaifiyarsa da ko rayuwarsa zai iya Badawa akan sai macen da har 'dan uwansa ya rasu itace a bakinsa itace burinsa itace ya yadda yabi bayan hanyar mutuwarsa akanta yakuma rasa,yancinsa,jin dadinsa,iliminda daga qarshema rayuwarsa duk akanta.,

Alkawari ne ya daukawa Haroon da Dad Omar bazai taba barin kowace irin cuta kusantota ba matiqar yanada Iko da Rai da lafiyan hanawa sai Kuma Wanda Allah yariga ya kaddaro mata kaman wannan matsalan ta gabansu a yanzu Dan kuwa Bai taba tinani ko hango Hakan zai iya faruwa gareta da gaske ba daga ya tafi ya dawon duk da abubuwan duk Basu tafi yanda akeso ba.

Sallama yayi dasu Aunt Mariam din ya rufe laptop din ya bar palon tareda nufan kitchen Kai tsaye ya dauko ruwan Daya ya wuce bedroom dinsa ya ajiye ruwan ya nufi toilet.

Ruwan dumi ya sakarwa kansa suna bin fuskansa zuwan jikinsa suna sauka qasa idanuwansa a rufe sbd duk lokacinda wainnan tinanin suka dawo masa nauyi kirjinsa keyi tareda basa zafin Kai.

Sai Daya gama wankan ya wanke bakinsa da mint mouthwash ya fito da towel dinsa da baya wani zama.

Shirin bacci yayi ba Riga jikinsa dagashi sai underwear da wata Riga mara nauyi gabanta duka a Bude ya haye gadonsa yayi kwanciyarsa bayan yayi addua.

Washe gari karfe goma na safe ya fito a shirye cikin Brown Paul Smith fit shirt da fit AG jeans sai agogon Bottega veneta black dayake hannunsa Koda ya fito siddeeq ya iso yana gidan a dayan palon yana aiki a laptop hakama cook tini ya iso yayi breakfast ya jere a dining.

Fitowansa kusan daga siddeeq har cook din qamshinsa ne kaman yanda ya Saba ya sanar dasu fitowansa Dan haka cook dinne yafara fitowa kallo Daya yayi masa yayi qasa da idanuwansa cikin girmamawa ya masa barka da fitowa tareda gaisuwa ya juya ya koma kitchen.

Siddeeq ma cikin girmamawan ya gaidasa Yana masa barka da fitowa.

Breakfast sukai sama sama kafin suka fice Kai tsaye fuskansa sanye da Black Prada goggles sbd ya saba Baya iya shiga Rana Bai rufe idanuwansa ba.

Siddeeq ne ke janye da sabuwar motar JEEY din mrcs Beymach Kai tsaye asibitin suka nufa.

Koda suka Isa asibitin Sister Ashley tagama fidda rai Allah yasa evening shift ne da ita Dan haka ma da safen taqi shigowa asibitin kwata kwata Amma tasan Ameenatou na can ko wanka Kila bazata yadda kowa ya kusantota ba idan ba ita din ta Gani ba Dan haka akwai yiyuwan tana can ko wankan Bata samu ba bare brush da sauran su.
##MAMUH#
#AMEENATOU
#JEEY
#SEELAHS

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
Chapter 8 · 0% Book details