← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 88

Sashe 3

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
60
BB ne ya matsa Baya ya dawo gefen Alh Lameenu ya tsaya Ya Kallesa kafin ya zauna a natse Yana sake gaisawa da Dr Dee din Yana bayyanarda girmamawansa sosai tareda nutsuwa kafin Shima Alh Lameenu ya sake sakewa suka gaisa sosai Yana tambayarsa aiki suna shiga zantukan rayuwa Dana ayyuka da yanda businesses na mutane ke tafiya kafin a natse cikin Kwanciyar hankali ba boye boye Daddy lameenu ya Kalli Dr Dee daidai lokacinda BB ya miqe tsaye ya ajiye masa Yan 100 100 doller a kan table din gabansa kusan bundle biyu zuwa uku batareda yace komaiba.

Alh Lameenu dinne ya Kalli fuskan Dr Dee a sake Yace,

"Akwai patient danake buqatan dukkanin bayanan komai akanta tareda sani akan girman matsalanta da duk abinda ya shafi komai dayake cikin file dinta na matsalanta."

Sake kallan Dr Dee yayi Yana mayar da bayansa jikin kujera ya jingina a natse Yana Dora kafarsa Daya kan Daya cikin Kwanciyar hankali kafin yace,

"Ko Hakan zai iya yiyuwa Dr Dee??"

Numfashi Dr Dee ya sauke Yana mayar da nasa bayan ya jingina Shima a natse kafin ya dago ya Kalli Alh Lameenu din kafin ya ka mayar da kallansa kan dalolin Dake gabansa a shimfide.

BB da Shima a natsen yake amsar Dr Dee din yake Jira kallan Dr Dee din yayi Wanda Shima BB din ya kalla,

Numfashi ya sake saukewa tareda sakin murmushi me Fadi da sanyi Wanda ya Saka su daddy lameenu din sakin murmushin Suma ba tareda damuwan komaiba.

Dr Dee wayarsa ya Ciro daga aljihunsa Kai tsaye yana Neman numbern da zai kira harya ganta.

Saka kiran yayi tafara ringing har tsawon lokaci kafin aka dauka cikeda girmamawa kafin ya amsa gaisuwan da Akai masa Kai tsaye yace

"akwai patient danake buqatan cikakkiyar bayani akanta a ayau so Ina buqatan file dinta a office dina kafin na iso akaisa desk dina,

Kallan Alh Lameenu yayi a natse yace,

"Wat's the name???

"AMEENATOU JADEN SEELAH or AMEENATOU NUHU BABBAH Kokuma AMEENATOU JAMAAL SEELAH "

Sunayen a jere kaman yanda Alh Lameenu ya fadosu haka ya fada yace kafin ya shigo Akai masa file dinta office ya kashe wayar.

Wani shegen murmushi Alh Lameenu ya sake Yana kallan Dr Dee Wanda yake dariyar Jin dadin Shima Yana Koro masa bayanan da suke sake kashe alh Lameenu din da dadi Dan kuwa yasan kudi shegune Amma Bai dauka Dr Dee zai zama Dan Kai tsaye haka ba Babu Batawa Kai lokaci bare dalolin gabansa su huce Dan haka da zafinsu BB ya matso ya tattara ya zubasu a cikin farar envelope me sunan SEELAHs a jiki ko rufewa bataiba ya ajiye gefen Dr Dee din Wanda sai a lokacin ya buqaci ruwa aka kawo musu Nan suka shiga fira sosai kaman sun Saba sbd take aka kulla alaqa.

Daga office din Alh Lameenu Kai tsaye asibitinsu Dr Dee ya nufa,
Yana Isa office ga mamakinsa babu file din Daya buqata take ya kira ya sake tambaya da sauri incharge na record office ya iso ya sanar masa file Daya buqata Bai taba dawo musu ba Yana gurin Dr Adams sbd patient din tasa family dinsa ce Dan haka komai nata shine yake kulawa dashi.

Sallamarsa Dr Dee yayi tareda daga wayarsa ya kira office din Dr Adams din Kai tsaye.

Cikin sa'a kuwa Dr Adams na cikin asibitin Bai Riga ya fita ba Dan haka Yana daukan wayar cikin girmamawa ya gaida Dr Dee din sbd shine a gaba dashi.

Babu Bata lokaci Dr Dee ya buqaci files din patient din Dake special A block duka sbd kawar da zargi ko tinanin komai daga Dr Adams din.

Da farko Dr Adams baiyi tinani ko zargin komai ba Dan haka ya tattara duka files nasu Dake office dinsa ya fito dasu da kansa yakai har office din Dr Dee din sbd Daman zasu tattauna matsalan wata sabuwan patient dinsu dake jiwa kanta rauni sosai Dan nata ciwon yayi tsananin gaske gashi itama special patient ce sbd matar babban mutum ce itama.

Ajiye files din yayi akan desk tareda zama Yana sake gaida Dr Dee cikin sakewa
Shima cikin sakewan yake amsawa suna fira cikin sabo da girmamawa kafin Dr Adams yafara jero masa bayanin patient din Yana nuna masa file dinta.

Amsawa Dr Dee keyi Yana duba files din Daya bayan Daya a tsanake har ya gama Babu file din dayake tsananin buqatan ganin Dan haka ya dago ya Kalli Dr Dee din batareda nuna komaiba da kulawa yace

"Duka duka iya patients din special block A kenan?Coz Nan duka 8 files ne and a record Kuma munada 9 patients a block din so meya samu Dayan file din ko patient din zance???

Dagowa yayi ya zubawa Dr Adams idanuwansa Yana jiran qarin bayani batareda tsaurarawa ba.

Numfashi Dr Adams ya sauke Shima batareda nuna fargaba ko Wani damuwa ba yace

"Dayan patient din is my patient, she's family,
Case nata Yans hannuna ne tin kafin Nan so file nata Yana office nawa"

Numfashi Dr Dee ya sauke Yana gyara zamansa yace

"Ok ba damuwa but dole zaka barwa Wani case dinta tinda kace she's family Kuma kasan me Hakan ke nufi so idan ka koma office ka Aiko min file dinta zan bawa Wani kwararren likitan case dinta."

Dagowa Dr Adams yayi da sauri ya Kalli Dr Dee din zuciyarsa na shiga shakka da fargaba tareda tinanin ta yadda zai iya yarda case din Ameenatou ya koma hannun Wani bayan yasan komai zai iya lalacewa hakama tayaya zai iya bari JEEY ya dawo ya tararda matarsa ba a yanda ya bar masa ita ba tinda idan har tabar hannunsa to tabbas zasu iya dorata akan drugs Wanda ba Bata time zai juyar da ita da gasken ba kaman wannan dayake temporary ba tinda wata na qarewa zata saketa ta koma daidai gashima duka duka a wannan lokacin baifi 6days watan ya qare ba.

Ganin yanayin Dr Adams ya Saka Dr Dee Dan sake fuska cikeda kulawa da nuna kaidar aikinsu kenan ya sani dole Wani likitan ne zai kula da Wanda yake family gunka sedai bazaa yi Maka iyaka da shiga case dinba kaima Amma dai Kuma bazaka karba ace Kai kadai ba.

Sanin Dr Adams ma yanada matsayi babba Kuma mugun kwararre ne a aikinsa ya saka Dr Dee kwantar da Kai cikin nuna kulawa Kai tsaye yace,

"Ka Aiko file din zan dubasa a Daren Nan zan karba case din nata da kaina yanda hankalinka zaifi Kwanciya coz zan iya cewa Ina ganin mahimmancinta gareka tin yanzu din."

Babbar matsalan dayake gudu kenan Dr Adams ta fitar Ameenatou hannunsa duk tsawon wannan lokacin daga zuwanta,
Sanin zata iya cike kwanakinta ta dawo daidai kaman yanda JEEY ya buqata ya sakashi karban case dinta gashi Kuma a yanzu datake gab da dawowan daidai ana Neman samun matsala haka zalika Kuma bazai taba iya Hana Dr Dee karban case dinba tinda aka Riga da aka fara maganar.,

Shi kansa Yana cikin manyan Dake karfafa girman dokan da Dr Dee ke magana,
Me zai fadawa Dr Dee idan yashiga file din ya tararda Babu komai face information da Dan sauran tests da ba'a rasa ba na lafiyanta da Basu ma shafi hauka ba kwata kwata na tabbacin lafiyan jiki da jininta ne da suke fes ba cutar komai a tattare da ita.

Hakama me zai fada akan patient din zaman asibitin kawai takeyi Bata kan kowanne drug,
Bugu da qarin matsalan shine idan suka San alluran da Akai mata shi kansa laifi ne Mai girman gaske Dan kuwa shi kansa yayi mamakin Fitaccen kwararran likitan Poland ace da kansa yayiwa macen datake dauke da igiyoyin aurensa irin wannan alluran duk da baisan dalilinsa ba Amma yasan koma menene dalili ne me Girma kadai zai Saka JEEY SEELAH yin Hakan.

Jin shirunsa ya sake Saka Dr Dee maimaita abinda ya fada din tareda basa tabbacin inshallah zai duba lamarinta yanda ya kamata Dan haka ya kawo masa file dinta kafin gobe.

Baiyi dogon musu ba sbd babu abinda zai iya fada a lokacin bayan cewa ok kawai ya miqe ya fice daga office din.

Dr Adams baiyi niyar bayarda file dinta ga kowaba Kuma baida niyar bayarwa din Dan haka dole ya nema JAMAAL akan ya dawo da gaggawa ya karba patient dinsa daga asibitin gabaki daya kafin tabar hannunsa barinta asibitin yayi wahala.

Duk yanda Dr Dee yaso tsanantawa ya karba file din a Daren dole hakura yayi sbd kada Dr Adams ya fahimci zalamarsa ga Hakan Dan haka ya bari sai washe gari yabar asibitin gabaki Daya.

Dr Adams kuwa kasa ma barin asibitin yayi yafara kokarin Neman JEEY sedai kwata kwata Baya samunsa,
Siddeeq ya kira ya sanar masa Yana son magana da JEEY akan kwanakin Ameenatou din sun kusa cika na Alluranta.

Siddeeq da tini ya kusan kammala komai na barin qasar da ita kaman yanda JEEY yabar masa komai zuwa lokacin Dan kowanne time ma zasu iya tafiya Dan haka sai Bai raba hankalin JEEY din da maganar ba ya sanar masa inshallah kafin lokacin ya cike zasubar kasar kawai so ma yakeyi kafin ta dawo daidai sun riga sun bar qasar dan tana dawowa daidai komai zai iya dawowa 'danye.

Ganin siddeeq Basu fahimci abinda yakeson fahimtar dasu ba yasa Dr Dee cigaba da kokarin Neman JEEY din da kansa sedai ba wannan time din dan tini duk yanda yaso kaucewa dr Dee abin ya gagara dan shima dr Dee ganin duk yanda zaiyi ya karbe patient din daga hannun dr Adams yayi amma dr Adams yaqi yadda komai nata ya shiga hannun wani take abin yafara tsanani dan kuwa manyan asibitin kusan tini suka shigo zancen.

Qarfi da Iko aka nunawa Dr Adams Wanda ya tabbatar masa da akwai abinda yake faruwa Wanda shi Bai saniba sbd a cikin kankanin lokaci abubuwan sukai nauyi ba zato ba tsammani kwatsam aka daukesa daga asibitin gabaki Daya aka turasa wata qasar ma.
#MAMUH#
#BESTLOVESTOTY
#AMJEEY
#HOTLOVE
#ROMANCE
#BABY
#AMEENATOU
#JEEY SEELAH
#JDENS
#SEELAHS

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
Chapter 3 · 0% Book details