← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 88

Sashe 54

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin farin Cikin da a duniya Mam ya manta rabon daya samu kansa acikinsa ya fara sake murmushin farin Cikin 'dansa ya dawo garesa tareda Aleena data kasa zaman r
Nigeria ta rabu da aurenta sbd bazata iya ba Amma ayau tadawo zata zauna sbd 'danta,
Hakama Jamaal Bai dawo qasar ba garesa sbd Yana mahaifin daya haifesa sai akan mace sbd ya sani Kai tsaye Jamaal ya dawo Nigeria ne sbd Omar daya dawo da 'yarsa.

Shidai koma yayane hakan ya masa daidai sbd Jamaal bazai taba sake barinsa ba daman sbd Aleena yake barinsa Kuma Aleenan yanzu gatanan duka Suna guri daya,tayaya bazai bari Yan media su San da hakan ba a fadawa duniya 'dansa ya dawo gurinsa,
Sauran Kuma surprise na gaba.

Budewa Mum dinsa mota yayi da kansa Yana kokarin sake hannunta ta shiga Wani Dan jarida ya jeho masa tambayar data sakasa dakatawa cak daga shi har Mum din da Siddeeq ma dayake kokarin budewa Jamaal din mota Shima.

Siddeeq ne ya fara juyowa ya Kalli Jamaal
Itama mum dinsa shi ta kalla kafin ta Kalli Mam dayake bayyanar da nasa mamakin Shima a fili na tambayar duk da daga garesa labarin ya fita.

"Da gaske ne Dr JAMAAL Seelah ka Dade da auren 'yar Omar jden tin baa San ita din 'yar sa bace???
Tsawon shekaru nawa ne da auren??
Menene gaskiyar zancen?"

Dan jaridar ne ya sake jeho tambayar wadda hatta sauran yan jaridar amsar suke jira Cikin mamaki Mai tsanani dukkaninsu suna sake jeho tambayar da a yanzu ne suka fara jinta.

Zafin daya taso zuciyarsa ya hadiye a hankali tareda Dan sauke numfashi a boye kafin ya qarasa Saka Mum motan ya rufe mata da kansa kafin ya juya y shiga kofar da Siddeeq ya Bude masa batareda yace komaiba.

Siddeeq ma motar ya shiga securities ma suka rurrufe motocin suna Koran Yan jaridan take aka tada motocin suka wuce anata yada zancen Mam seelah da kansa yaje airport tarbon 'dansa Jeey seelah daya Bata ba labarinsa sai yanzu tareda tsohuwar matarsa uwar yayansa biyu Haroon seelah da Jamaal Seelah.

Tinda suka kama hanyar gida babu me magana sbd mamakin inda zancen ya fita ya shiga kunnuwan Yan jarida da bakinsu,

Tayaya Dad Omar zai tsinci maganar a bakin Yan jarida,.
Ba hakan yaso ba sbd ba abin rushing bane yaso yafara sanin asalin komai a kansu na sirrin dayake Jin akwai a boye sbd hakanan ya kasa nutsuwa da yanda Dad yanda ya sameta kawai ya sanar masa Bai sanar dashi komaiba sbd a yanda yasan power dinsa dole zai San yayi Aiki a asibitin data zauna din Amma Kwata kwata Bai masa maganar ba idan Kuma Bai saniba to tabbas Shima Neman sister Ashley yakeyi Kila sbd yasani bazai wainda suka ringa haukatar masa da 'ya ba wanda yasan shima Yana Ciki.

Yanzu Kuma Dad dinsa ya lalata komai a yanda zancen Nan ya fita yasan ba shakka daga Dad dinsa ne Kuma dole Yana da manufa da hakan wanda Shikuma a yanzu Babu wanda aka Haifa da zaiyi using matarsa Dan cimma wata manufa Koda kuwa Dad dinta ne bazaiyi amfani da ita Dan cimma manufofinsu na yaqin da tin kafin a haifeta suke abinsu Bata saniba,

Shima zaiyi yaqin Amma tabbas saiya tabbatarda Bata cikinsa.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[29/05, 10:08 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
109

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

**********
Tin kafin su isa gida a motan siddeeq yafara wayoyi Yana kokarin Hana labarin fita ko kadan Amma ga alama hakan ba lallai ya samu ba sbd Mam ne da kansa ake magana.

Jamaal har lokacin baice komaiba sbd Baya buqatan magana ko hayaniya da Dad din daga isowansa Kuma siddeeq yasan abinda ya kamata Dan haka magana ma sakawa Kai ciwon Kai ne kawai.

Mum dinsa ma daya San batasan tashin hankali ta lafe jikinsa hannunta har lokacin riqe Cikin nasa Ya Dan juyo ya kalleta itama shi ta kalla zatai magana ya katsesa ta hanyar Bude bakinsa a natse da sauti mara qarfi yace

"Its okay,Siddeeq will handle everything"

Gyada masa Kai tayi tana sauke ajiyan zuciya sbd batason ko kadan Jamaal din na shiga hayaniya da Dad dinsa duk da tafi kowa sanin waye Mam din Amma tinda ya Riga ya haifesa ya gama dashi.

Koda suka isa gida securities tini suka wangale gate din gidan motarsa data Dad din kadai suka shige harabar gidan sauran a waje suka tsaya sbd na mansion din Mam ne Dan haka can suka shige kawai.

Suna parking Mum Atee da Ayesha Dake jiran isowansu a gidan tareda masu aikinsu fitowa sukai tarbonsu Cikin farin Cikin dayake ba har zuciya ba sbd sanin waye Aleena a gurin Mam,
Duk da basuda aure matsayin Aleena daban a gurinsa Cikin matan duka duniyar Dan itace ta haifar masa rayuka biyu dayafi so duniya fiyeda tasa rayuwar hakama itace macen dataso shi tsakaninta da Allah har ranta take sonsa.

Daga gefen danta Mum din tasa ta gaisa dasu Mum Atee tana amsawa da thank you a welcome din da ake musu,

Shima Jamaal din Bai saki uwarsa ba har Saida suka isa Ciki yakaita har sama bedroom dinta tukuna y sauko ya koma nasa palon ya haye samansa.

Siddeeq kuwa kayan Mum din ya Saka masu Aiki suka Kai sama har bedroom dinta aka jere mata komai aka sake gyara koin kaman tana Poland dinta sbd duk abinda aka Saka gidan na wanda zaiwa Mum din da Jamaal daidai ne siddeeq yayi wannan aikin sbd a wannan Dan lokacin Shima yayi yawon jirgi kaman tsutsu Dan haka Shima yanzu ya samu nutsuwa tinda zasu zauna guri daya.

Bangaren Jamaal kuwa tini yayi masa gyaran daya San shine daidai raayinsa da rayuwarsa da kansa yayi aikin,

Closet dinsa a cike take da dukkanin kayansa tin daga kan kananu da kaftans, designers kuwa kaman baa San zafin kudin ba Dan kuwa wardrobe dinsa gabaki daya designers ce originals daga kamfani.

Shoes,clips, toiletries, cosmetics da komai na amfaninsa Babu abinda ba designers ce take bugun juna ba.

Shi kansa siddeeq yanzu a gidan zai zauna sbd part dinsa me zaman kansa dayaji wata sabuwar kudin aka Gina da sunasa tareda zuba luxuries Shima abubuwan da sukai masa daidai raayinsa da buqatansa ya zuba hakama wardrobe dinsa Shima duka designers ne Dan Shima a yanzu kudin sun zauna masa iya zaunuwa.

Tsit gidan yayi bayan komawan Dad dasu Mum Atee mansion dinsu ta kofar garden din gidan zuwa nasu garden din daya hade Mansions din.

Hutawa masu gidan keyi Babu wanda ya fito sai dare lokacin masu Aiki tini suka gama shirya dining da koina suka fice zuwa dakinsu.

Siddeeq ne yafara fitowa cin abincin ya nufi dining room din Yana kunna wayarsa dan duba halinda ake Ciki yaga labarin ya Riga ya fita Amma ba sosai ba sbd kokarin da yayi na Hana fitar tasa Dan haka zaiyi wuya ya isa kunnune Dad Omar ko Wani daga Cikin jdens din kafin JAMAAL ya tinkari Dad Omar da kansa.

Mum ce itama ta sauko sanyeda doguwan jallabiya black daya masifan mata kyau sbd farinta tana qamshin English perf me shegen tsada da sanyi itama.

Tana ganin siddeeq ta sauke ajiyan zuciya tana Jin dadin ganinsa ta sake tana sakin murmushi tana qarasa saukowa ya miqa mata hannunsa ta kama ta qarasa saukowa Yana mata sannu Cikin tsananin kulawa da kauna sbd uwa yake jinta kaman yanda takejinsa kaman Haroon dinta data rasa sbd shine ya zama kaman kariya daga kowanne cuta ga 'yayanta duka biyun,
Tana masa kauna me tsafta da karfi sbd sanin zai iya bada ransa ga 'danta hakan ya Saka take masa tsaftatacciyar so kaman yanda take kaunar danta Babu qabilanci ko kadan.

Dining room suka nufa Suna magana Shima Yana dariyar abinda take fada masa din.

Suna zama Mum din ce tafara juyawa sbd qamshin Paco Rabanne daya shiga hancinta tasan JAMAAL dinne ya shigo.

Shi dinne sanyeda Off-white Nikes gashin kansa me santsi a kwance hakama na fuskansa a kwance kwance yayi duhu sbd farinda yakeda dashi sosai.

Qarasowa yayi Yana sakarwa Mum dinsa nitsatsen murmushi me sanyi da nutsuwa ya rankwafo ya Dora bakinsa a hankali gefen goshinta ya Bata kiss Yana zaunawa kujera kafin ya Kalli siddeeq Dake son tsokanarsa da kallan dayake masa akan maganar dazun ta Yan jaridan.

Wani kallo ya watsa masa Yana cewa

"Karka fara,
Nasan Kuma zancen dole zai iya kunnen Dad Omar so gobe Mum acan zamuyi dinner tareda su zanyi magana da Dad Omar din"

"Hakan ya kamata kayi magana dashi kafin Dad Dinka ya Riga Omar bazaiji Dadin hakan ba,hakama itama AM din zancen zaije mata a Wani irin sbd Abu ne da batai tinani ba Kuma jinsa daga sama baiyiba."

Siddeeq ma Naam yayi da hakan Dan haka suka fara cin abincinsu Cikin nutsuwa,

Siddeeq Tuna fried rice yaci da Salad din Nikakken nama,
Chapter 54 · 0% Book details