← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 88

Sashe 6

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan kasa yiyuwa alluran tayi duk da tana daure Saida su Fahat suka danneta su dukansu kafin Dr Dee cikin rashin tinanin illan da alluran take qara mata a duk lokacinsa aka sake yi mata ita ya soka mata cikin qwarewa tareda danna ruwan ya tsiyaye mata cikin jijiyanta take tayi wani mummunan yunquri cikin tsananin azaba da gigitanwar alluran ta fara kokarin fisge fisge amma ba qaramin karfi ne da alluran ba take gabobinta da dukkanin duk wani abu dayake jikinta kasawa yana sakewa yana mutuwa sai Alokacin idanuwanra da sukai wani irin mummunan ja suka bude ahankali daqyar sedai babu abinda take iya gani bayan dishi dishi sai kuma wasu irin hawaye masu zafin gaske da suke gangarowa ta gefe.

Sai alokacin kowa ya janye hannunsa daga kanta sbd sunsan Babu wani abu da zata sake yi Kuma.
#MAMUH#
#AMEENATOU
#THE SEELAHS

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
63
Akan gadon datake dauke aka gangarota aka dawo da ita dakinta har lokacin Fahat na gurin cikeda bayyanarda kulawa da damuwa akan Ameenatou din.

Shine ya warware daurinta tareda mayarda belt din inda suke boye jikin gadon kafin ya daura mata ruwa da sauran abubuwan da dole zaayi mata sbd yanzu saita kwana biyu ahakan Bata dawo daidaiba Dan ko ruwa a yanzu bazata iya Sha da kanta ba sai anbata.

Bayan ya gama komai cikin kulawa yayiwa sister Ashley sallama ya fice zuwa wani aikin yabar sister Ashley tana zare mata kayan jikinta ahankali sbd goge raunikanta da mata dressing dinsu.

Har lokacin idanuwan Ameenatou din a Bude suke Amma Bata ganin komai hakama Bata Jin komai bare Kuma motsawa sedai idanuwan sunyi jajir hawayen azaba ne kadai ke gangaro musu ahankali.

Ita kanta sister Ashley cikin damuwan da sanyin jikin take tana goge mata ciwukan da cottonwood.

Sai dare sosai kusan Daya saura kafin sister Ashley ta fito dakinta tareda rufe mata sbd doka ce Babu Wanda aka yadda bayan 1 na dare a gansa gurin patients idan ba Wanda babbar matsala ta tasowa ba sbd tsaro da kiyayewa Dan haka 1 nayi gurinsu tsit zaka jisa Dan yawanci da dare ana Basu maganin bacci ne.

Masifar Dake cikin alluran da akai mata Baya barinka kowanne irin Abu bayan komawanka kaman gawa da ido Bude Dan haka yanda ta barta haka ta taddata da asuba.

Daga Nan kwance ta goge mata jikinta Dan Babu maganar wanka sai tafara sakinka tukuna.

Tana gama goge mata jikinta ta Saka mata wasu uniform din daban ta mayar da ita ta kwantar,

Daga Nan kwancen ta zauna bakin gadon ta gyara mata gashinta tareda tattara mata ta Dan kama sama sama ba sosaiba sbd daman baa kamawa sosai ga wainda ma basuda gashin aske musu kawai sukeyi su huta sbd fisgan gashin sukeyi suna illata kansu kokuma qazantar tayi musu yawa amma ita datake dashi sosai gamawa takeyi da band mara karfi kuma sakwa sakwa baa kamewa sosai.

Harta Saka abin gyara gashi ta fece mata ta kame idanuwan Ameenatou din a Bude Amma har lokacin Bata gane waye a gabanta hakama Bata iya ko motsawa.

Tea ta hada mata me kauri sosai Wanda baida zafi ko kadan hakama baida sanyi me dumi kawai ta Saka spoon tafara Bata a baki bayan ta tayar da ita ta jinginar jikin gadon ta Saka napkin a wuyanta zuwa kirjinta sbd Rabi kusan duk dawowa yakeyi so zai lalata kayanta.

Tana gama Bata ta ajiye cup din tareda zare farin qaramin towel din ta goge mata Baki da fuskan gaba Daya ta mayar da ita ta kwantar ta fice bayan ta Saka mata ruwan alluran baccinta cikin drip data sake daura mata Babu Bata time idanuwanta suka rufe baccin wahala ya dauketa.

Ficewa sister Ashley din tayi sbd attending sauran patient din Daya bayan Daya.

Har yamma bacci takeyi Bata Bude idanuwanta ba sai gap da magrib Wanda yayi daidai da zuwan Nurse Fahat dakin tareda sister Ashley ya duba Ameenatou din Yana sake bayyanarda kulawansa Yana tambayar sister Ashley jikin Ameenatou din.

Babu tinanin komai sister Ashley tace

"She's ok for now kawai dai time na cikakkiyar sakin alluran ne baiyiba but idan time din yayi she will be okay kawai dai Daman fa ita baa rabanta ne batason kowa na zuwa kusa da ita,so please next time Karka bari kazo kusa da ita batareda Kun Saba ba"

Murmushi yayi Yana yiwa Ameenatou din Wani kallan Dayake Saka zuciyarsa sanyi Yana sake zagaya idanuwansa koina akan kyakkyawar fuskanta data fada lokaci Daya kaman Wanda take kwance tsawon lokaci tana jinya yace

"Ai inshallah zamu Saba da ita sbd naga duk naji damuwan sbd nine jiyan ciwon ya taso gashi yanzu zatai kwana biyu a Hakan."

Murmushi itama sister Ashley tayi cikin kulawa tana Dora hannunta kan Wani raunin dayake wuyan Ameenatou din ta shafa ahankali sbd ganin gurin yayi ja tace

"My Beautiful Baby Bata son sabawa da kowa bayan ni sai Siddeeq dinta idan kanason ta sabu da Kai ka ringa tsayawa daga nesa nesa tukuna ahankali ahankali idan tana ganinka zata iya sabuwan da Kai but for now dai pls keep ur distance."

Murmushi yayi Yana kallan fatan wuyanta da sister Ashley din ke shafawa cikin kulawa kaman zata cire mata ciwon shikuwa Jin yakeyi kaman zaiyi fitsari a wando sbd Wani irin yanayi da hakan ke sakar masa Dan haka ya juya ya fice Yana Dan Bude kafafu kada yabarsu a matse sister Ashley zata iya ganin Wani abin.

Yana fita sister Ashley taci gaba da suba sauran raunikanta tana Dan hura mata tana ambatar sunanta kaman baby qarama Dan kusan baby take Jin Ameenatou din Dan ko Babu ciwon haukan Taga alaman Ameenatou din tamkar baby take sbd Wani abin datakeyi ko da akwai hauka to akwai azaliya.

Haka ta ringa kulawa da ita a kwance kaman me paralyze tsawon kwana biyun harta warware ta dawo daidai haukanta sedai Kuma babban tashin hankalin Daya sake samunsu shine ko kwana batai da dawowa daidai dinba cikin tsakiyar dare abin ya sake tashi a cikin daren Babu tashin hankalin da Basu shigaba sbd na ranar ma abin ba sauki haka aka sake taruwa akanta aka sake mata alluran wanda kusan dukkaninsu sunsan ba qaramin hadari bane yin alluran acikin sati biyu ma bare daya to bare kwana biyu dayi mata ita yau ma an sake.

Babban abinda ya Saka sister Ashley damuwa da sauran nurses din harma da wasu doctors shine ciwonta Baya tashi haka kawai dole akwai dalili sbd sai Wani yazo gurinta take wannan tashin hankalin mara dadin Gani.

Haka aka sake mayarda ita dakinta kaman gawa sister Ashley tayita fama daqyar kwana biyu ya sake cika ta dawo daidai sedai Kuma Wani abu da sister Ashley ta lura dashi sabo daga Ameenatou din shine kwata kwata ta Dena walwala ta Dena sakewa ta koma shiru ne kadai yake Bata nutsuwa.

Wannan sabon yanayin ne ya Saka sister Ashley damuwa Dan haka ta kira siddeeq ta sanar dashi sedai kafin yazo a ranar ma da daddaren haka ciwon ya sake tashi kafin kace me dai komai ya rikicewa sister Ashley Dan kusan duk bayan kwana biyu haka ciwon ke tashi Kuma duk Saka idonta ta kasa Gano Menene yake Saka Hakan faruwa daga karshe dai lamarin ya girmama dole ta sanarwa siddeeq komai akan ta zargin akwai Wanda Ameenatou take Gani da Dare Hakan ke faruwa amma batada tabbaci hakama batada ikon fada ko binciken ita kadai sbd zata iya rasa aikinta akan tayi zargin tsaro da securities na asibitin.

A ranar da siddeeq yazo daqyar ya samu permit na dubiyan kallo Daya yayiwa Ameenatou din take ya fidda wayarsa batareda damuwa da cameras Dake gurinba ya dauki hotonta tana zaune kan wheelchair din da sister Ashley ta turota Kai tsaye a gurin ya turawa JEEY hoton tareda sauran bayanin da sister Ashley tayi masa.

Ga mamakinsa harya bar asibitin JEEY Baice komaiba gameda sakon hakama Bai kirasa ba Dan haka yaji zuciyarsa tayi nauyi Dan kuwa a yanzu bayajin zai iya barin Ameenatou asibitin kota halin yayane shi da kansa zai dauketa inshallah.

Ameenatou din ma harya ya gama ya tafi tana zaune Bata iya ko motsawa ba bare iya cewa komaiba bayan fararen idanuwanta data zuba masa.

Bayan tafiyan siddeeq haka sister Ashley ta koma da ita sukaci gaba da lallabawa tana kulawa da ita.

Washe garin ranar da siddeeq yazo babban tashin hankalin da sister Ashley ta tashi dashi shine laifin siddeeq na hoto da aka kamata dashi itama haka aka sauya mata block aka dauketa daga block A din kwata kwata.

Tsaye take a office din Dr Dee ta kallesa cikin son samun yanda takeso tace

"Dr Dan Allah ka Saka hannu abarni A block A dinnan ko Dan sbd patient Dinka Ameenatou kasan Bata taba yadda kowa ya kusantota gaba Daya ciwonta gaba zaiyi komai zai iya faruwa Kuma idan aka cigaba da Bata wannan alluran please Dr"

Daure fuska yayi zaiyi magana Akai knocking kofar office dinsa tareda budewa a natse batareda da jiran izininsa na shigowanba.

Kofan ya kalla itama sister Ashley kofan ta juya ta Dan kalla sedai ganin doctors dinsu manya kusan guda uku tareda siddeeq ya Sakata juyowa gaba Daya tana musu barka da shigowa kafin ta sake magana JAMAAL dake bayansu yana amsa waya ne ya shigo kai tsaye yana kashe wayar tasa qamshinsa me wani irin sanyi tareda qamshin tsadansa a bayyane batareda an fada maka kudinsa ba ko sunansa ba ya gauraya iskan office din gaba Daya.

Fararen idanuwansa akan Sis Ashley suka fara sauka yayi mata kallo Daya tareda dauke idanuwan nasa Ya amsa gaisuwanta Kai tsaye cikin muryansa da Hausa Bata kama ba yanda ya kamata.
Chapter 6 · 0% Book details