← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 88

Sashe 44

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta bangaren Hafiz ma yabar maganar ne a yanzu Badan yabarta har abada ba Dan kuwa duk Wanda ya keta haddin yar uwarsa bazai sake zaman lafiya ba a rayuwarsa daga ranarda yacika kudinsa na inganta rayuwarsu zuwa Wani matsayin.,,

Bazai taba barin a nuna Yar uwarsa da yatsa akan ta haihu ba sbd duk Wanda yayi Hakan zai iya komai akansa,
Amma Kuma a yanzu babbar buri da qudurinsa shine Hana Hakan faruwa ta hanyar Saka rayuwarta matsayinsa Babu Wanda ya Isa ko kallo biyu yayiwa abinda ta Haifa da wata manufar.

***********
Abubuwa sun fara yiwa iyalin gidan Babbah nauyi sbd Babbah da lafiya taqisa Sam Dan haka kullum a yawon Neman lafiyarsa ake asibiti
Hakama Ameenatou ma lafiya nata yin qasa sbd cikin da yanzu da gaske de ya fito tsufa yake yi,
Dadah ce a tsaye gurin hidima da Ameenatou da Babbah shikuma Hafiz gaba Daya ya koma abin tausayi sbd wahalar nema Dan cinsu da neman lafiyansu harma da sauran abubuwan.

Da kansa shi kadai yakai Ameenatou Akai mata register na awon ciki Yana Kaita duk bayan sati Daya sbd Dadah idan zasu barinta akeyi kulawa Da Babbah idan Kuma yaji sauki sai ita takai Ameenatou din awo.

Rayuwa tayiwa Hafiz nauyi sosai Dan Babu abinda yake kalla kaman haihuwan Ameenatou da Baya kaunar ko kadan tazo da matsala,
Hakama Babbah koyaushe maganarsa daya shine Hafiz yayi kokari ya tanadi komai kada Ameenatou ta haihu da matsala ko buqatan komai.

Duk yanda hafiz yake kokarin ganin samun aiki lamarin ya gagara Dan haka kullum yawon aikin karfi yakeyi shiyasa ba Wani abu yake samu ba duka wahalance yake koyaushe,

Cikin Ameenatou Koda ya shiga wata 8 Hafiz ya sauya kamanni gabaki Daya sbd azabar rayuwa da wahala tareda nauyin dayake kansa da yayi masa yawa,
Duk zafin Nemansa da yanda yake tinanin samun mafita kafin haihuwan Ameenatou lamarin ya tsaya cak Dan haka kawai ya yankewa kansa shawarar abinda zai inganta rayuwar Ameenatou dinsu da abinda zata Haifa tareda tsaronsu da samun yancinsu tareda tsayawa su fuskanci komai da kowa kansu a tsaye dan haka batareda sanin kowaba yafara neman hanyar da zai sanar da OMAR JADEN inda suke dan yasan duk inda yake zuwa yanzu yana can yana nemansu.

A yanzu dai Kam Tako ina dukkaninsu suna buqatansa musamman Ameenatou hakama shi nasa karfin Neman Yana Neman qarewa kaman Wanda Bai taba shiga aji ba,ga babba ma duk da ya samu lafiya yanzu Amma Babu karfin nema yanzu,ga Dadah ma duk wahala na Neman tsofar da ita,

Babu me farin ciki ko walwala a cikinsu shiyasa haryanxu sun kasa sakewa sosai a cikin mutanen anguwansu koyaushe suna kame a guri Daya.

Koda Ameenatou ta shiga watan haihuwanta ta sauya sosai tin daga kan lafiyan jikinta harta kanta sbd Takoma shiru shiru sosai ko magana batason yi hakama komai na juyewan kanta kusan ya dawo daidai kawai abinda take kasa tinawa kanta na juyewa wasu lokutan shine shin haroon Yana Ina??
Waye Jamaal a gurinta hakama waye Haroon??
Hakama kamanninsu na mutum Daya take Gani a idonta Kuma ta kasa tantance Ina kanta yake yanzu Ina ta baro.

Babbah da Dadah daidai gwargwado sunata Shirin haihuwarta Kuma Shima Babbah yanzu Babu abinda yakewa yarsa fata bayan kyakkyawar rayuwa ingantacciya itada abinda zata Haifa masa Wanda sun Riga sun rungumi kaddara basa fatan ma tsayawa Wani janye janyen Neman uban sbd rufawa Kai asiri.

Ta bangaren Hafiz ya zurfafa Neman hanyar isarwa da Omar Jaden Sako ta duk inda zai iya Amma rashin kudi ya Hanasa Isa ga wasu hanyoyin da yawa na Isa ga garesa dashi.

Har Abuja yaje so biyu Dan samun isarda sakonsa a companies dinsa Amma kwata kwata ko Daman shiga Bai samu ba bare Isa ga manyan da sune zasu dan iya masa hanyar magana da Jden din ko Kuma Ahmed hakanan yake kashe kudin mota a banza ya dawo.
#MAMUH#[29/05, 10:07 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
100

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

***********
Shorts kaya Hafiz ya Saka masa tareda kamo hannunsa suka fito zuwa qasan Dadah ma Nan ta sake biyosa da fruits din suna isowa dining ya manta da fushi yakeyi da Mommansa yazo da gudu Yana cewa

"Mommah"

Ajiye cup din hannunta tayi tana juyowa cikeda tsananin son babyn nata tayi kissing kumatunsa tana cewa

"My love"

Dariya Dadah take musu tana sake lallabasa itama ta samu suka shirya suka zauna dining din zata basa nasa abincin a Baki,

Fatmah CE ta fito daga hanyar dayar saman ta bedrooms dinta Dana iyayenta ta nufo dining din ko zama bataiba saiga Arry qaninta Wanda yafara zama Dan saurayi.

Gaida Dadah sukai ta amsa cikeda kulawa kaman yayanta suka fara breakfast din kowa da abinda yake ci.

Basu gamaba Didi ta fito ta zauna itama tana Kiran sunan ARFAT zuwa gareta wanda ya saka Fatmah yin shiru har suka gama sbd kowa a table din Arfat ko AM.

Am dince tafara gamawa ta zari tissue ta goge bakinta tareda miqewa ta Isa gurin Arfat ta sake kissing dinsa tana cewa

"Bye sweetie"
Bye Dadah,
Aunt Didi bye"

Qamshinta ne tabarsu dashi ta wuce Arfat na cewa

"Bye Mommah"

Driver ne zai kaita Dan haka tana fitowa Kai tsaye mota ta nufa ta Bude ta shiga Baya Daman Yana ciki yin dazu Yana jiranta Kuma Yana ganin zuwanta ya tada motar Dan haka tana shiga yaja suka bar harabar mansion din.

Wayarta ta fiddo daga handbag dinta Dake ajiye gefenta ta Nemo numbern Dad dinta ta Saka Kiransa cikin sa'a ya tashi kuwa Nan suka fara magana bayan ta gaidasa.

Har suka Isa wayar sukeyi sai da zata shiga exam sukai sallama bayan ya mata adduoi sosai,

Babbah ta kira Shima Amma har lokacin Bai tashiba Dan haka ta shiga exam dinta kawai.

Acan gida ma Hafiz na gamawa dayake shi ya gama nasa karatun na 2yrs ne yayi tini ya fara aiki da babban matsayin dana Ameenatou dinne yake Kai kafin ta gama duk da matsayi daya zasu hau a kamfanin.

Tareda Arfat ya fita zuwa office sbd yau ba Wani aiki ne dashi sosaiba,

Suna fita Dadah ma ta koma bangarensu har lokacin Babbah Bai tashiba Dan haka a dining din palonsu ake jere masa nasa abincin Dan Daman can su basa joining Jamaar gidan cin abinci a table musamman idan Omar Yana gari.

*****Karfe biyu ta dawo gida ta tarar da kowa Yana jiranta cikin farin ciki da murnan gamawanta suka fara murna suna tayata murna sosai,

Mum Nur ce ta rungumeta tana cewa

"Congrats my girl"

"Thank you Mum Nur"

Didi ma rungumeta tayi cikin farin ciki Da Jin dadi kafin Fatmah ma datake gida ta miqa hannu ta tayata murna fuska a sake.

Daidai lokacin ne Hafiz da Arfat suka dawo fa gudu yayo gurinta yana nuna mata abinda yake hannunta ta dagasa daqyar sbd yanada nauyi tana kallan Yaya Hafiz Dayake kallanta Yana cewa

"Finally Lady AM budurwan Babbah ta gama karatu, congrats Lady Jden"

Dariya tayi sbd a yanzu duk lokacinda aka ambaceta da sunan budurwan Babbah farin cikine ya ke rufeta sbd haryanxu duk yanda ta samu sauyin da wayewan ita dai dince budurwan Babbah da haryanxu yake jinta kaman yar jaririya Baya ganin girmanta duk da lafiyayyan jikan data dire masa.

"Yaya Hafiz thank you,Amma ka Tina alkawarinmu right??

Dariya yayi Yana wucewa hanyar dakinsa Dake gefensa shi Daya Yana cewa

"Ban manta ba"

Yana wucewa Kai tsaye palon Babbah ta nufa daidai Yana fitowa zai tafi makarantar tata da kansa su dawo tare sbd farin cikinsa Baya misaltuwa kaman yanda Omar yake can farin cikinsa a bayyane na ganin wannan Rana.

Hannu Babbah ya miqa mata daidai lokacinda suka Hade a tsakiyar palon fuskansa a washe da farin ciki yayi Wani irin haske Shima ya sauya sosai Hutu ya ratsesa daidai gwargwado.

"Budurwata ayau ta zama mace itama ta tashi daga yarinya yar makaranta ko?"

Dariya tayi tana kama hannunsa cikin nata tace

"Babbah ai kullum ni baby ce a gabanka,
Thank you."

Dadah data qaraso ciki itama zaunawa tayi tana kallan yanda Ameenatou din ke narkewa a gabansu  kaman dai koyaushe yanda suka Saba abunsu tafara sakawa karatun da rayuwarta albarka harma da Arfat da babusa a zancen.

Bata Wani zauna sosai ba ta miqe ta fita ta haye Samanta inda dakinta Dana ARFAT ne kadai a saman sai Palo wadatacce sai kofar da zata sadar da ita zuwa palon Dad dinta.

Dayan bangaren saman shine na Uncle Ahmed da matarsa aunt Didi sai dakin Fatmah itama a saman,Hafiz Kuma bangarensa daban.

Komai na Ameenatou da Arfat a gidan ya banbanta Dana kowa duk da na kowa dinma duniya ce me zaman kanta Dan kuwa kaf gidan baka gane waye Asalin 'dan me gidan waye bare,

Rayuwar Hutu da daula kawai sukeyi da wayewa da zallan ilimi sbd ko Babbah yanzu yana shiga mutane ba laifi sbd tini yayi abokin hira Wani dattijo Dan boko dayake zaune kasar da yayansa da matarsa yayi retire tini zaune yake a gida Yana hutawa Kuma me kudi sosai Amma kasancewan baida matsala ba ruwansa sosai yake buqatan Abokin hira da tattauna tsufa da lokaci tini suka dinke da Babbah dayake a kusa suke Dan Hakan kusan koyaushe suna tare kodai anan gidan can bangaren hutawar Omar ko a gidan shi Alh Al'ameen din.
Chapter 44 · 0% Book details